Da ɗumi-ɗumi Bankin Najeriya CBN ya fidda sabbin dokoki wajan kuɗi
1. Yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.


Idan mutum na son cire kuɗin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.


2. Duk wanda ya je banki cire kudin da suka haura naira 50,000 da caki na banki da wani ya rubuta masa, to ba za a ba shi kudin ba. Yayin da dokar cire kuɗin da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da caki a tsakanin bankuna daban-daban tana nan a yadda take.


3. Yawan kudin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na'urar cire kudi ta ATM a sati kuwa shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a ranar naira 20,000 ne kacal.


4. Takardun kudin naira 200 kawai bankuna za su dinga lodawa a cikin na'urar ATM.


5. Idan a wajen masu amfani da na'urar POS ne kuwa, naira 20,000 ce yawan kudin da mutum zai iya cirewa.


6. A yanayin da ake da tsananin buƙata kuwa da ba zai wuce sau ɗaya a wata ba, inda ake buƙatar cire kuɗin da yawansu ya fi wanda aka ƙayyade don wani dalili mai ƙarfi, to abin da za a bari mutum ya cire ba zai haura naira miliyan biyar ba, idan kuma kamfani ne to ba zai haura naira miliyan 10 ba.


Sannan a hakan ma sai an caji kashi biyar cikin 100 na yawan kudin ga mutum, da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da za a cire.

A cikin sanarwar, CBN ya ce, ga dukkan mai son yin amfani da doka ta shida, to zai ya bi waɗannan ƙa'idojin na ƙasa, don tare da sanya su a shafin CBN da za a ƙirƙira saboda hakan:


Ka tanadi katin shaida kamar katin ɗan ƙasa ko fasfon tafiye-tafiye ko kuma lasisin tuƙi.

Lambobi na musamman na banki wato BVN

Cikakken sanya hannun mai cire kuɗin

Samun amincewar babban jami'i don cire kudin a inda ake buƙatar hakan

Amincewa a rubuce daga wajen shugaban bankin don ba da damar cire kudin.

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Gaskiya wannan doka ta takura Yan Nigeria musamman yan kasuwa da talakawa

    ReplyDelete
  2. Maganar gaskiya shine wannan doka tayi sosai saboda ata dalilin haka ne kawai za asami sauki game da harkar kidnapped nidai abin da zance akan wannan doka shine kawai allah ya barmu ikon bin ka,idojinta amin

    ReplyDelete
Previous Post Next Post