Da farko ina neman addu'a ga duk Wanda ya karanta ya karu,Allah ya biya mana bukatumu na alhairi !!!

 



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

Saiwar zogali

👉 Sanyin kirji 

A tamna saiwar zogale a tareda citta kwara daya.


👉 Tsutsar ciki

A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.


👉 Ciwon sanyi ga mata da maza 

A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.


👉 Yawan ruwan maniyi ga namiji

 A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.


👉 Tarin sanyi ko Mura : A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.


👉Rage nauyi ko qiba

A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum


👉 Zafin fitsari 

A tafasa saiwar zogale da kanumfari a aha sau uku safe da rana da yamma.


👉 Ciwon sugar

A zanka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.


👉 Qazuwa


A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha 


👉 Ciwon daji a cikin baki

A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dasu a kullum sau uku,safe da rana da yamma


👉Ciwon yatsa na Dankankare 

A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.


👉 Matsanancin ciwon kai na zafi.

A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.


👉 Ni'ima ga mata

A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin cup sai a zuba rabin gwangwanin madara  a sha.


Idan kun ji dadin wannan post din sai a yi shere wasu su karu.


A yi man addua ita ce goron sadaka.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post