CIGABAN YUNƘURIN GWAMNATI NA SHAFE HARKAR MUSULUNCI

 



KISAN KIYASHIN ZARIA EPISODE 6


WALLAFAR: Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)


CIGABAN YUNƘURIN GWAMNATI NA SHAFE HARKAR MUSULUNCI


Ganin irin tausayawar da ake ta samu daga ƙungiyoyi daban-daban da ɗaiɗaikun mutane, tare da Allah-wadai da ake yi da wannan ta’addancin na Sojojin Nijeriya akan ‘yan uwa Musulmi. Sai gwamnatin Buhari ta fara fito da wasu shirye-shirye da tsare-tsare da zai bayyana abin da aka yi a matsayin abin da ya dace, tare da samar da muryoyin da za su nuna goyon baya da cire tausayin al’umma ga iyalai da dangin waɗanda aka kashe a Zariya. 


 A ranar Asabar, 19/12/2015 wasu daga cikin Gwamnonin Arewa, ƙarƙashin shugaban ƙungiyar Gwamnonin, Kashim Shettima, suka gabatar da zama a Kaduna, inda suka tattauna yadda za su ɓullowa al’amarin takawa Harkar Musulunci burki a dukkan jihohinsu na Arewacin Nijeriya. 


Makonni biyu bayan wannan zaman, a ranar 28/12/2015 ƙungiyar Limamai da Malamai na jihar Kaduna suka gana da Gwamnan Kaduna, Nasiru Elrufa’i, inda suka bayyana goyon bayansu akan faɗa da yake yi da waɗanda suka kira su da ‘Yan Shi’a a jihar Kaduna, suka kuma bayyana masa cewa hakan da yake yi wani aiki ne ga addinin Musulunci.

 

Kwanaki kaɗan bayan wannan zaman, a ranar 14 ga Junairun 2016, shi ma GOC I Division, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade, wanda shi ne ya jagoranci duk hare-haren da sojoji suka yi a Zariya, ya gana da wasu Malaman Wahabiyawa da Limamansu, inda ya yi musu bayani a kan dalilin da ya sa suka farma ‘yan Harka Islamiyya, da kuma sanar da su abin da sojoji suke buƙatar su sanar da almajirai da mabiyansu. A ƙarshe ya ba su kyautar naira dubu 500 suka raba a tsakaninsu.

  

Waɗannan abubuwan da suka riqa faruwa na cewa gwamnati na neman haɗin kan Malamai don faɗa da Harkar Musulunci ya ba wasu daga Malaman ƙungiyar Izala, waɗanda dama ba su iya ɓoye gabar su ga Shi’anci ba dama na ganin sun riƙa halatta ta’asar da sojoji tare da gwamnati suka yi a kan ‘yan uwa Musulmi. Da bayyana kashe rayuka da ɓarnata dukiyoyin da su Janaral Oyebade suka yi bisa umurnin shugaban rundunar soji Janaral Buratai a Zariya, a matsayin aiki ga addinin Musulunci da maganin masu zagin sahabbai.

 

A ranar 21/12/2015, Tubaɓɓen Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi jawabi, inda yake yabawa da kashe rayukan da sojojin suka yi a Zariya, lokacin yana sarkin na Kano, inda ya bayyana shi a matsayin faɗa da masu zagin sahabbai. Sarki Sanusi ya ambata cewa, Nijeriya ƙasa ce da aka gina ta a kan koyarwar Ahlis-Sunnah, don haka ba za su zura ido wasu su riƙa zagin Sahabbai da matan Manzon Allah (S) suna kallo ba.


Ƙungiyar Izala, musamman ta bakin shugabanninta, Shaikh Sani Yahaya Jingir, Shaikh Abdullahi Bala Lau da Shaikh Kabiru Gombe sun yi ta wa’azozi suna masu nuna murna da farin ciki kan abin da aka yi a Zariya. A rayawarsu gwamnati ta yi wannan ta’addancin ne don ta murƙushe musu waɗanda suka tare musu gaba ta maishe su manyan Malamai.

 

Tun bayan kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da sojoji suka yi a ranar Litinin 14/12/2015, a ranar Alhamis 17/12/2015 shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Janar Tukur Y. Buratai ya bayyanawa manema labarai cewa sun miqa Shaikh ɗin inda ya dace don a hukunta shi. Ba a sake samun labarin halin da Shaikh Zakzaky da matarsa, Malama Zeenah ke ciki ba, sai a ranar 13 ga Junairun 2016, kimanin wata guda cur, a yayin da wani kwamiti a ƙarƙashin Majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), wacce ta haɗa da Farfesa Ɗahiru Yahya, suka gana da Shaikh ɗin a inda ake tsare da shi a Abuja.


Za mu shiga BABI NA BIYU:


* Harkar Musulunci Ta Ɗauki Matakin Shari’a

* Shari’ar Kotun Abuja Da Umurnin Sakin Shaikh Zakzaky Da Matarsa

* Shari’ar Kotun Kaduna Da Korar Ƙara

*Bayan Hukuncin Kotu

*Wasu Matakan Da Harka Ta Ɗauka


Za mu cigaba.

—Journalist Dan Fudiyya

08/12/2022_ 14/05/1444


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/


DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post