"...Bisa yakini Sayyid Zakzaky (H) ya ke yin Addini !!!




—Shaikh Yaƙub Yahya Katsina


Ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke tunatarwa ga ba’alin ’yan’uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) na yankin Kano ma su karatu a makarantar Tahrirul Masa’il wadda Malam Aliyu Rimin Gado ke koyarwa, da wani ba’ali na ’yan’uwa daga Zariya. Duka sun ziyarce shi ne a muhallin Markaz Katsina, domin jajanta ma sa na rashin lafiyar da ya ke fama da ita, wanda yanzu haka ya ke jinyar aikin da aka yi ma sa.


Shaikh Yaƙub Yahya a jawabinsa garesu ya na cewa: “Kowace al’umma ta na da jagoran da ta ke girmamawa, kuma ta na ganin shi mai kama hannunta dan samun mafita, to amma gaskiya namu jagoran ya ban-banta. Ta ina ne ya ban-banta da sauran jagorori? Shi ne; Manzon Allah (S) ya ce Ya raba komai Ya baiwa kowwa, sannan Allah  da  maɗaukakin Sarki ba marowaci ba ne, amma akwai abinda ya bada kaɗan, (Allah ba Ya rowwa amma akwai abinda Ya bada ɗan kaɗan). 


Allah na bada tawali’u ga mutane da yawa, Allah na bada kyauta (ka ga mutum mai kyauta), Ya na bada rahama da tausayi... abinda Allah ke badawa ɗan kaɗan shi ne yaƙini. To mu jagorammu (Sayyid Zakzaky (H) ya ban-banta da yaƙini. Abu ne wanda bayyananne ya ke ba ɓoye ya ke ba, daga imani sai yaƙini. 


Eh! duk waɗannan jagororin (na sauran fahimtoci) muminai ne ma su imani, amma yaƙini ya kan ban-banta. Mutumin da yaƙininsa (da Allah) ya kai zai sadaukar da kansa da rayuwarsa da iyalinsa da matansa da iyalinsa da komai nasa saboda ganin addinin Allah Ya tabbata to wannan ya ban-banta da sauran wanda shi ba haka ya ke ba. Idan kuma akwai wani da yake jin ya na da jagora irin namu to ya zo ya yi irin abinda ya ke yi, dan mu gane yaƙininsa, shi ma ya sadaukar da iyalinsa da komai na sa sannan ya ce ya na da yaƙinin abinda ya ke yi shi ne mafitar al’umma.


To amma shi (Jagorammu) dan ya gaskata ma na cewa abinda mu ke yi mu na yi ne da yaƙini, kuma a kan dai-dai mu ke, sai ya aikata ma na a aikace ya sadaukar da rayuwarsa da komai nasa. To wannan shi ne ya ban-banta namu jagoran da na saura, dan haka kai (ɗan’uwa) ka da ka yarda a yi maka 419 a raba ka da Jagora, kada a zo ma ka da wani abu ya raba ka da jagora. Maganganunsa su na nan kawwane, wasu na nan rubuce, wasu a kaset jawabai daban-daban an killace an kiyaye. Akwai Tafsiri, akwai Nahjul Balagha, akwai munasabobi daban-daban da karantarwa daban-daban to ba ka da wata shubuha, kuma kada wani ya zo ya ce ma ka akai matsala (to) shi ne matsalar.


To mun gode wa Allah da ya saka mu cikin wannan tawaga, Allah Ya sa mu rayu cikinta, mu ƙarƙare cikinta, mu koma wajan Allah maɗaukakin Sarki a cikinta".


   #SYYK

Dec162022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post