Babban Taron Tinawa Da Shahadar Sayyada Fadimatuz Zahara(A's) A Birnin Najaf-Iraq!!!


  

[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

Obafemi

Tunda Safiyar yau Talata 3/ ga watan Jumadha Thani, 1444H , Miliyoyin mutane daga ciki da wajen Iraqi suka haɗu farfajiyar Sauratul Ishriin dake tsakiyar birnin Najaf mai Alfarma , kamar dai yadda aka saba kowacce Shekara domin gabatar da taro da Tattakin tunawa da Shahadar Sayyida Faɗimatuz Zahra (a.s) .


Bayan an fara buɗe taron da karatun Alkur'ani mai Girma , sai kuma aka gabatar da Aza (Makokin) Sayyida Zahra (a.s.) inda aka yi kuka da juyayin wannan Babbar Musibar .

 Daga bisani kuma Ayatullahi Muhammadul Ya'aƙubi ya gabatar muhimmin jawabi ga mahalarta , jawabi ne da ya shafi al'ummar Musulmi baki ɗaya musamman ma mabiya Ahlul Baiti (a.s) da suke jiran bayyanar Imamin wannan zamani (a.j ) , sannan aka yi Gamammiyyar Addu'a kuma dukkan Mahalartan suka hau sahu aka yi jerin gwano domin takawa zuwa ga Haramim Imam Ali (a.s.) domin yi masa Ta'aziyya. An gabatar da wannan tafiyar ne cikin alhini da juyayin Shahadar shugabar Matan Duniya (a.s) .


Alhamdulillahi, cikin nufin Allah mun samu halartar wannan taro da wannan Tattaki, kuma munyi addu'a ga dukkan yan uwa Muminai da basu samu halarta ba . Muna roƙon Allah Ta'ala ya haɗamu a cikin ladan , ya kuma sanya mu a ceton Sayyida Faɗimatuz Zahra (a.s) da Mahaifinta da Ƴaƴanta .

Allah ya ƙara dawwamar da Azabtarsa ga waɗanda suka zalunci tsokar jikin Manzon Allah (a.s) .


السَّلامُ عَلَيْكِ يا مُمْتَحَنَةُ ، إِمْتَحَنَكِ الَّذِي خَلَقَكِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَكِ ، وَكُنْتِ لِما امْتَحَنَكِ بِهِ صابِرَةً ، وَنَحْنُ لَكِ أَوْلِياء مُصَدِّقُونَ ، وَلِكُّلِ ما أَتى بِهِ أَبُوكِ صلى‌الله‌عليه‌وآله ، وَأَتى بِهِ وَصِيُّهُ عليه‌السلام مُسَلِّمُونَ ، وَنَحْنُ نَسأَلُكَ اللّهُمَّ إِذْ كُنّا مُصَدِّقِينَ لَهُمْ ، أَنْ تُلْحِقَنا بِتَصْدِيقِنا بِالدَّرَجَةِ العالِيَةِ ، لِنُبَشِّرَ أَنْفُسَنا بِأَنّا قَدْ طَهُرْنا بِوَلايَتِهِمْ عليهم‌السلام .


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post