ANA WATA GA WATA: YA HALATTA AYI WANKAN JANABA DA SABULU sabuwar fatawar Sheikh Idris Abdul'aziz Bauchi


Ustaz Idris Abdul'azeez Bauchi Ustazun Malamin ya tabbatar da cewa lallai za'a iya yin wankan Janaba da Sabulu, a cikin wani faifain bidiyo da kafar -Gaskiya Dokin Karfe- ta wallafa a shafinta na Facebook Malamin ya ce har Muƙabala sai da suka yi da manyan malamai a garin Bauchi dangane da wannan mats'alar.


Babbar hujjar da malamin ya bayar akan halaccin yin wankan Janaba da Sabulu ita ce "SABULU BA NAJASA BA CE"!


Malamin ya ce a lokacin da Malaman suke ƙalubalantar sa dangane da wannan mats'alar sai ya tambaye su cewa shin Sabulu najasa ce? Kowa sai ya zaro idanu.


Tambayar da masu hankali suke yi dai ita ce; da ma duk abin da ba Najasa ba ne za a iya yin wankan Janaba da shi???


Me za ku ce dangane da wannan sabuwar fatawa ta Ustazu?


[ MA'ASUMAH TV// mnnu/Ng0026 ]

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post