ANA MAGANA:- Kira Ga Duk Wani Masoyi Da Mabiyin Sheikh Abduljabbar Na Duniya. !! _Barrister Ibrahim Garba Carefor

 


SHAWARA/KIRA GA MABIYA SHEIKH ABDULJABBÃR DA SAURAN MASOYA


DAGA BAKIN KWARARREN LAUYAN KARE HAKKIN DAN  ADAN


(Barrister Ibrahim Garba Carefor) Assalamu Alaikum Warahmatullahi 


Yan Uwa mutanen Dr, Abduljabbãr Kabara ya kamata Mutane Susa Zuciyar su a sanyi akan Wannan Hukuncin da aka yanke,na Farko ya kamata kusani a Tsarin mulki na kasa da kuma Tsarin Tafiyar da kotuttuka na kasa  Wannan Kotu ta shari'ar Musulumci ta Sarki Ibrahim Yola batada hurumin yankewa wani Hukuncin kisa Kuma Hukuncin ya tabbata Tsarin Mulkin kasa Yana Gaba da duk wata Kotu ta customary ko wadda ake Kira ta shari'ar  Musulumci magana na abinda ya Shafi na blasphemy kwata~kwata baya daga Cikin abinda za'a iya yankewa Mutum Hukuncin kisa Hukunci irin  wannan,


Wanda Yake Mutum yanada dama ko a Jihar kano akwai kotuttuka Guda biyu wadanda za'a iya daukaka Kara Kuma akwai Babbar kotun kasa wadda akwai dama ta daukaka Kara wadda Tsarin Mulkin kasa yaba Dr. Abduljabbãr


So in akabi Wannan Hanyar za'asami nasara saboda Haka Mutane su kwantar da Hankalin su Wannan abin ma kamar  Ina kallon shi kamar ma Zan Kira shi Kamar Wasa ne bazai taba yiwuwa ba,Kuma Mutanen Dake a Cikin Tafiyar ya kamata Susa Zuciyar su a sanyi Kuma a Guji Yin zage~zagen Abubuwa da Suka Shafi  Gwamnati ko Suka Shafi wasu hukumomi ayi amfani da tantagaryar doka ma'ana shine dama ta daukaka Kara da akaba Dan Adam  a Cikin Tsarin Mulkin Kasar nan Kuma wannan damar tabbatacciyar dama ce wadda babu abinda  zai iya kankare ta sannan Maganar wani Hukunci wanda zai dauki Rai wadannan kotuttuka na Tarayya Sunada  Adadin irin laifuffukan da Za'a iyayima dan Adam  Hukuncin da Za'a iyayima dan Adam Akan laifin da yayi da zai iya daukar ranshi saboda Haka Inaso Jama'a su kwantar da Hankalin su Kuma Suyi abinda yadace su cigaba da Adduo'i su Saurara abita Hanyoyin da yadace na doka a daukaka Kara Kuma in an  daukaka Kara Ni inada tabbacin Za'ayi Nasara 


Wassalamu Alaikum


Rubutawa


Bun Ibraheem Abu Muhammad


+2347036969347

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post