An karrama Dr. Ibraheem Zakzaky matsayin mutumin da ya fi kowa Son Zaman lafiya .

 



An Karrama Shaikh Zakzaky a Matsayin Mutumin Da ya Fi Kowa Son Zaman Lafiya Tun daga Shekarar 2015 Zuwa 2019


Daga Yahaya Muhammad Soje


Da safiyar yau talata ne wasu gamayyar Jaridu suka karrama Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky a matsayin mutumin da yafi kowa son zaman lafiya a Nijeriya.


Gamayyar Yan Jaridun sun bayyana Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky a matsayin wanda yafi kowa son zaman lafiya a Nijeriya duba da irin Ta'addancin da aka masa tun daga Shekarar 2015 zuwa yau karshen shekarar 2019 amma duk da tarin mabiya da Shaikh Zakzaky yake dasu amma bai basu Umurnin suyi tashin Hankali da kowa ba a Kasar nan.


Malam Muhammad Ibrahim Gamawa da Injiniya Abdullahi Muhammad Musa ne suka karbi wannan Lambar girmamawa, tare da Jinjina ga wadanda suka shirya wannan taron kana kuma sun bayyana cewar Shaikh Zakzaky mutum ne mai son zaman lafiya tun tashinsa da kuma fada da zalunci da tabbatar da adalci.


Daga karshe Almajiran Shaikh Zakzaky da suka karbi wannan lambar girma sun shelanta ci gaba da Gwagwarmayar tabbatar da addini karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky kana kuma sunyi kira da a Saki Shaikh Zakzaky da gaggawa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post