Amfanin Dabino a Muslunci.


 

@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 

Dabino yanada matukar amfani a jikin dan Adam, domin Manzon Allah (SAWW) ya kasance mai son Dabino, har ma yace "Idan kunyi azumi, to Dabino ya zama abunda
zaku fara ci (buda baki) dashi, idan babu dabino, to ku samu kankana" 

AMFANIN DABINO 

1. Yana saurin narkarda
abinci.

2. Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure.

3. Yana taimakawa wajen kara jini.

4. Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata.

5. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi. 

6. Yana karawa Ido lafiya. 

 7. Yana Rage Nauyin kiba. 

8. Yana Maganin Gudawa. 

 9. Yana Saurin Saukarda Hawan jini.

10. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun basira.. 

11. Yana kariya daga Sihiri.

12. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun sauqi wajen haihuwa. 

YADDA ZA'AYI AMFANI DA DABINO. CIWON NONO GA WACCE TA HAIHU;- Anacin dabino guda 7 asha man tafarnuwa karamin cokali sau 1 arana kwana uku. 

DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA;- Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin a kwanta. 

GA MATA MASU JUNA BIYU;- Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan anyi kusan haihuwa Wannan yana hanawa macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin Allah. 

GUDAWA; Ana daka garin dabino a saka a ruwan zafi a sha In shaa Allahu yana tsayar da gudawa. 

SAMUN KUZARI; Ana cinh dabino guda ukku a sha zuma cokali 1 da safe da yamma. 

SAMUN LAFIYAYYAR FATA:- Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska awa daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan yana saurin gyara fuska. Bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon CANCER ko wacce iri.

Haka Kuma MANZON ALLAH (saww) YACE DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA KACISHI,BABU WATA CUTA DA ZATA SAMEKA AWANNAN RANA, KO KUMA SAMMU KO SIHIRI. 

Wasu Malaman Musulunci kuma sunce Manzon Allah (saww) Yana nufin kowanne dabino ba wai sai Ajwaba (Wallahu A'alam). 

GODIYA GA ALLAH (swt) daya Saukar mana Abubuwan Yau da kullum. 

YA ALLAH KA KARA MANA LAFIYA A JIKIN MU WAYANDA BASUDA LAFIYA KUMA ALLAH BASU LAFIYA. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post