ALKALAMI KA FI REZA KAIFI-: Shaikh Abduljabbar: Katimi a gaban Katurmuji.

 **


M. I. GAMAWA

A satin da ya gabata duniya ta ji hukuncin da aka yanke wa Shaikh Abduljabbar da Kotun "Musulunci" ta mai shari’a Yola ta zartar. Hukunci mai cike da al'ajabi da abin kaito, wanda ba kasafe mutum mai hankali ke son a danganta shi da wanda ya aikata wannan kasassaba. Da ma shari'ar ta tasar ma shekaru biyu ana tata-burza a kanta. A tufka, a warware, don a kai ga hadafi. Hadafin na iya zama daidai ko barna, hakan ba ta dami wadanda suka kulla wannan makircin ba. Suna gidajensu suna hidima a cikin iyalansu, amma sun hana bawan Allah samun wannan dama, kai ka ce ba su taba samun labarin kiyama ba, balle yakini da ita. 


Maganar Malam Abduljabbar ba bakuwa bace ga duk wanda ya damu da addinin Musulunci a Najeriya. Tun yana yi shi kadai da ’yan tsirarun almajiransa, har ya samu magoya baya daga cikin gida da ketare. Wannan sai ya wajabtar masa da abubuwan da Mumini ke fuskanta. Wadannan abubuwa suka saki linzaman dawakansu zuwa gare shi da dukkanin makamansu na yaki. Suka doshe shi ta dukkanin sako da kwararo mai iya isa jikinsa da mutuncinsa. 


Ga duk wanda ya saurari jawabansa ko ya karanta littafansa da ya rubuta kamar MUKADDIMATUL AZIFA da JAWFUL FARA, tabbas zai tabbatar da cewa, Shaikh Abduljabbar ya dauki kaya mai nauyi, kuma mai wuyar kaiwa inda ake so a kai. Na farko Shaikh Abduljabbar ya bayyanar da abin da malamai suka boye don tsoron rayuwarsu da ta iyalansu. Bayyana abin da ba a sani ba na iya zama babban laifi a gun wadanda ke amfana da abin da ake kai tun dauri. 


Bayan wannan, sai kuma hassada daga malamai da wadanda ba su ba. Tabbas hassada da mahassada, dukkanin su kayan wanda ya fara yi wa Allah tawaye ne, imma akwai wadanda suka jahilce shi ba su da yawa. Ba Shaidan din suka jahilta ba, hanyoyin da yake bi ya riske su suka jahilta. Duk lokacin da yara suka gaza kammala aiki, dole babba ya sa musu hannu don aiki ya kamala. Shi kuma babban shi ke mulkin duniya a yau. Shi ne ya makantar da Ganduje da Alkali Yola har da Maluman Fada masu fatan a yi kisa. 


Ga dukkan alamu Shaikh Abduljabbar ya fara samun sakamakon da ya dace da mutane irin sa masu ganin gaskiya su fade ta komai dacinta. Alkali Yola ya zartar da hukuncin wanda ya yi batanci wa Annabi a kan wanda ke kare Annabi da sunan tsarkake Annabi. Da ma ya ce zai yi abin da aka sa shi ya yi, ba wai abin da doka ta ce ya yi ba. Ga shi ya yi kamar yadda wadanda suka sa shi suke so. Watakila mu bi maganar daki-daki mu ga ko haka Alkali Yola ya kamata ya yi a matsayinsa na Alkali da ya rantse da Alkur'ani cewa zai yi adalci ma kowa?


Da farko bari mu yi tsokaci kan abin da mutanen kasar nan suka kira kotunan Shari’a don fahimtar inda suka fito da dalilin kafa su a takaice. Su dai irin wadannan kotuna da ke ikirarin suna shari’a sun samo asali ne daga kasashen Musulmi da Turawan mulkin-mallaka suka kwata da karfi. Domin kada su hana Musulmi aiki da shari’a, nan take sai suka samu muggan maluma suka ba su aikin yi wa shari'ar asali kwaskwarima. Malaman kasar Indiya ta waccan lokaci da kasar Sudan sun taka rawa sosai a wannan aiki. Wani babban dalilin yin haka ta bangaren haddi shi ne nuna cewa shari'ar Bature ta fi ta Musulunci adalci, nesa ba kusa ba, kamar yadda masu karatu za su gani, in Shaikh Abduljabbar ya daukaka kara zuwa Kotun Bature. 


Wani abu muhimmi da mutane suka manta shi ne an yi dokokin Najeriya ne don ’yan Najeriya. Kare jinainensu, mutuncinsu da kadarorinsu, ba wai don wani wanda ba Banajeriye ba. Duk wata kasa akwai abin da ake cewa "’yankasanci," wanda duk wata doka da ake kafawa ana la'akari da wannan ginshiki mai karfi. Shin Dokokin Najeriya sun yarda a kashe dan kasa domin dan wata kasa? Shin ana iya kashe rayayyen dan kasa don ya yi batanci ga matacce, musamman in mataccen ba dan Najeriya ba ne, kai ko ma dan Najeriya ne? 


Me ya sa a yau wadansu masu tunanin da ke juya duniya suke yakar hukuncin kisa da dukkan karfinsu na fada-a-ji? Me ya sa suka karkata ga wannan tunani? Ga daya daga abin da suke kafa hujja da shi, cewa suke, "idan wani ya kashe wani, an yi asarar wanda aka kashe, to don me za a sake asarar wanda ya kashe?" Wannan na iya zama wani kakkarfan dalili a gare su, wanda sabanin dokokinmu ne. Abin tambaya wadanne irin dokoki Najeriya ke ko yi da su, Musulunci ko waninsa? Mene ne abin da ba Musulunci ba? 


Bisa mahanga irin ta dokokin Najeriya, Manzon Allah ba shi da muhalli, sai dai matsayin mutumin da wasu mutane masu tarin yawa suke girmamawa. Wannan matsayi na dokokin Najeriya shi ne ya sa mabiyin doka sau da kafa, Muhammadu Buhari ya kira Manzon Allah da "Wani Mutum" a lokacin da yake yi wa wadanda suka hukunta wata da ta yi batanci ga Manzo a Kano. Abin tambaya shi ne, shin Buhari na iya kiran Sardauna, Zik Tafawa Balewa ko Awolawo “wani mutum”? Amma ga shi ya kaikasa kasa ya kira Annabi da haka. Me ya sa? Don Annabi ba Banajeriye ba ne. Wannan ta fuskacin dan kasanci ke nan, kafin mu shiga wani fagen daban. 


Duk mutanen da muka ambata a sama akwai ukubar da za a yi wa dan kasa in ya yi batanci gare su domin gwarazan Najeriya ne. In ka musa, ka wulakanta takardar Naira, wanda hotunsu ke jikinta ka gani. Giyar ’yankasanci ita ce ta ta da Gwamnan Kano Ganduje ya tafi kasar Ibo don rarrashin su kan hukuncin da wasu masoya Annabi suka zartar kan wata mata da ta yi batanci ga Ma’aiki. Bai tsaya a nan ba, sai da ya biya diyya da alkawarin daukar dawainiyar makarantar ’ya'yanta daga Firamire har Jami'a. Wato inda za su gama Jami'a yana mulki, da ya dauke su aiki a jihar Kano. Amma don rainin wayo a yau shi ne ke kai malami kotu, wai malamin ya yi batanci ga Fiyayyen halitta. A lokacin da Ganduje ya dawo Kano daga ciratar zambiyar da ya yi zuwa kasar Ibo, bai bai wa ’yan Kano hujjar cewa matar da aka kashe ba ta aikata laifin batanci ba, sai ya yi mirsisi, ba tsoro, ba kunyar duniya, balle ta lahira. Me ya sa haka ta faru?


Babban dalili shi ne "’yankasanci." Manzon Allah ba Banajeriye ba ne, don me za a kashe Banajeriya domin sa? Wannan abin da na fada shi ne daya daga cikin abubuwan da za su fid da Shaikh Abduljabar daga wannan shari’ar siyasa ta Alkali Yola. 


Wani abu muhimmi shi ne irin rawar da Alkali Yola ya tafiyar da shari'ar daga farkonta zuwa karshenta. Ya sanya wa kansa rigar mai kara da ta mai ba da sheda, ya hada da rigar alkalanci a lokaci guda. Alhali ko Bature ya ce, "Ba za ka zama Alkali a shari'arka ba." Rigar da Alkali Yola bai yafa ba ita ce ta wanda ake kara kawai. Yola ya keta duk wata ka'ida ta alkalanci a shari'ar Shaikh Abduljabbar. Ba shi da bambanci da Alkalan da suka yanke wa Galilio da Hallaj hukunci. 


*Za mu ci gaba insha Allah.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post