Abinda Wasu Basu Sani ba:-Dalilan da suke sa wasu yam matan rasa mijin aure da wuri !!!

 



 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 
ABINDA 'YAN MATA BASU SANIBA

 Dalilan da suke sa wasu yammatan rasa mijin aure da wuri. 

Bayani na hakika ya tabbatar da cewa sau da yawa wasu ‘yan matan kan fada cikin larurar rashin samun abokin zama,  Sakamakon girman kai, wanda masu hikima kan ce rawanin tsiya, shi kuma Abubakar Imam a cikin littafinsa na Magana Jarice, ya karasa managanar da cewa, duk wanda ke wulakanta jama’a zai ga iyakarsa. Da yawan ‘yan mata yayin da suka kai wani mataki na girma tauraruwar suna haskawa a wannan lokacin wanda hakan ne yake sa wa samari su yi wo tururruwar zuwa wajen budurwa don zama masoyinta na aure da na nishadi ma.

A wannan lokaci ne budurwar ke ganin ta zama tauraruwa wadda hakan yakan sa ta girman kai wajen zabar masoyi na kwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakani ga Allah. ‘Yan matan sukan zabi masoyi yayin da suka sami wanda ya fi shi sukan canja akalarsu kan wanda idanuwan su ya gano, haka za su yi ta canzawa har su rasa wanda za su zaba.

Girman kai da rudin duniya yakan saka idanuwansu rufe wa su rasa gane ina suka dosa. Ba wani abu ba ne yake janyo hakan illah son rai da kuma son abin duniya shi yake kawo hakan wani lokacin ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu.

Da yawa a yanzu sukan dauki buri mai girma su dorawa kansu wanda hakan ko kusa ba zai samu ba, idan kuwa ya samu to! Sai an sha wuya ko kuma a same shi da sauki karshe a sha wahala. Da yawa daga wasu ‘yan mata kan saka wa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan saurayi kamar zubin Fulani irin saurayin da ake ba su labari cikin littafin Hausa za su aura. 

Sai budurwa ta saka wa zuciyarta lallai sai irin wannan namijin za ta aura wanda yake mara makusa kamar shi ya yi kansa, ko kusa babu wannan ba zance babu kwata-kwata ba amma kafin a samu za a dade ace an samu wanda ya hada komai ba shi da wata makusa kamar yadda na cikin littafin Hausa yake.

Haka kuma wasu kan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so, saboda sun riga sun bar wa zuciyarsu wannan tsari. Allah Yasa Mudace..... 
SAUKE APPLICATIONS DINMU A WAYAR KA YANZU DOMIN SAMUN AYYUKAN MU AKOWACE RANA. GA APPLICATIONS DINNAN 👇👇👇👇


Kasancewa Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post