A shekarar Dubu Biyu da Goma sha Biyar 2015 ne ranar 12 ga watan Sha Biyu rundunar sojojin Nigeria sukayi dirar mikiya akan fararen hula marasa makami, ma zauna garin Zaria dake jihar Kaduna.


 

KISAN KIYASHIN ZARIYA DA KUMA TAUYE HAKKIN DAN ADAM DA RUNDUNAR SOJOJIN NIGERIA SUKAYI YA SABAWA KUNDIN TSARI NA DOKOKIN NIGERIA.

Mohammad Mahady Khamis.

A shekarar Dubu Biyu da Goma sha Biyar 2015 ne ranar 12 ga watan Sha Biyu rundunar sojojin Nigeria sukayi dirar mikiya akan fararen hula marasa makami, ma zauna garin Zaria dake jihar Kaduna.


Inda sukayi kisa- kisa irin ta mummuke ko ince ta gilla idan nace kisan kiyashi ma dukkan dai dai ne.

Kisa na ba gaira ba dalili batare da hujja ko dalili da hankalin masu hankalin zai kama ba.


Inda yayi sanadiyar rayukan mazauna Nigeria akalla Dubu 1000+ akalla.


Sakamakon binceke da masu bincike sukayi ya tabbartar da rashin rayuka kamar haka.

Mazaje == 548 Anyi musu kisan gilla.


Mata == 297 Anyi musu kisan gilla.

Yara == 192 Anyi musu kisan gilla.

Mata masu ciki == 23 Anyi musu kisan gilla.


Iyalai da kuma dangin yan shi’a a Nigeria 39 sun bace bat, ba’asan inda suke ba, kuma ba labarin su.

Wannan ne yasa kungiyoyi da dama a fadin duniya sukayi Allah wadai da nuna rashin jin dadin so akan wannan al’amari.


Kuma sukace kisan kiyashin zariya shine mafi muni kisan kiyashi a tarihin Africa.


Muhukuntan Nigeria har yanzu sun kasa daukan wani mataki akan kisan Duban Dubatan mabiya shi’a a Nigeria da kuma cigaba da tsare Passport na sheikh Ibrahim Yakubu Al-zakzaky {h} da mai dakin sa malama zeenatudden.


Muna kira da babba murya akan cewa: Gwamnati ki gaggauta sakar wa sheikh Ibrahim Yakub Al-zakzaky [h] da mai dakinsa Passport Ɗinsu batare da wani sharadi ba.


Bazamu Taɓa Mantawa Ba.


📰 Journalist

Dan Fudiyya

1 Dec 2022



Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN

SAUKE APPLICATIONS DINMU A WAYAR KA YANZU DOMIN SAMUN AYYUKAN MU AKOWACE RANA. GA APPLICATIONS DINNAN 👇👇👇👇


1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah yatsinewa buhari da. Burtai da elrufai Allah ya isa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post