Yan Uwa Mu Kula, Wannan Hakkin Jagora Ne..!!  -Shaikh Abubakar Muktar


Da yake gabatar da Ta'alimi yau Alhamis 3/11/2022 a babban Masallacin Juma'a na garin Dukku, Gombe. Wakilin 'yan uwa na garin Dukku Shaikh Abubakar Muktar ya bayyana cewa "Yadda jiki yake shutuwa ayi jinyarsa, haka ita ma zuciya tana shutuwa, kuma ana jinyarta. Shutukan zuciya sune: Rowa, Hasada, Kariya, Fushi, da sauransu.

Duk wanda ya anka yaga ya kamu da shutar Hassada, ko Rowa etc yana da kyau ya natsu wajen ganin ya magance shutar data kama shi. Idan ka ankara kana da Rowa, sai ka danne zuciyarka ka rinka yin kyauta. Idan yazama kayi jayeyya da wani, sai ka gane ya fika gaskiya to yana da kyauta kayi itirafi da rashin gaskiyarka. Dan haka dole muyi kokarin kawar da duk wata shutar zuciya da zata hana mu kaiwa ga Allah madaukakin Sarki.A wani bangaren kuma Shaikh Muktar ya bayyana bukatar 'yan uwa su lizimci halartan Ta'alimi, gurin addu'a, da sauran tarukan Harkar Islamiyya. Wanda hakan shi zai baima Dan uwa damar samun tabbata a cikin wannan harka. Akwai wadan da suna da uzuri baza su samu damar halartan ba, to ba a kansu muke magana ba. Dan haka 'yan uwa mu kula wannan hakkin jagora ne mu masa biyeyya, kuma shi ya assasa wadan nan taruka.


Umar Babagoro Dukku

3/11/2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post