Kiran sistoci Ga burazu::- Kamar yadda kukeson muzama muma haka mukeson kuzama_ Fatima Adamu Tinja



@MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE 


- 'Yar gajeruwar tunatarwa ga Matasanmu/Mazajenmu. 

Yana da kyau, Ko wane Saurayi Matashi ya kamata ya tsoraci Allah alokacin samartarsa,ya zama mutumin kirki na gari, Kuma ya kiyaye kansa daga gurbata zuri'arsa da wasu manyan zunubai,Ya san da cewa an halicce sa da Shugabanci, Sai ya dauki hanyar zama Shugaba na gari.


A naso ya zama Mai matuqar tinani da hankalin rayuwa,Mai nemo hanyoyin da zai bi na ganin ya zamewa Matarsa ta duniya miji na gari,Uba na gari kuma ga 'Ya'yansa. 


Kada kullum kace burinka kasamu ta gari,kai kana son gangariya wacce ta hada komai,ta iya komai,lafiyayyar budurwa,wacce ta tsare kanta daga dikkan Maza,take kokarin kiyaye dokokin Mahaliccinta.


Amma kai in aka dauke ka da halinka aka sanyaka a microscope din rayuwa,aka tankadeka aka taceka da kyau, Za'aga baka yi ko Qanqanin cancanta da samun irin wannan Macen ba.


Ashe kenan kana ta cafanen rayuwa ne,amma kamance da wani sinadari mafi Muhimmanci a rayuwarka.


Dan'uwa mai daraja, Ka cire son zuciya ka ajiye gefe, Kacire rudun rayuwa ka yar dashi, Ka debe karatuttukan daka koyo ko ka gani a wurin wasu,wadanda basu dace da koyarwan Muslunci ba.Ka riqi gaskiya, Ka rungumi dai-dai, Kayi d'amara Ka kuma zage damtse, Ka binciko irin Zamantakewar Manzon Allah(S), da kissan zama Miji na gari.


Kayi dubi cikin rayuwar Magabata, Ka karanta littattafansu, Kasan Menene rayuwar aure da yadda akeyi aji dadi nsa, Ka gargade kanka, Ka shirya fuskantar wata rayuwa mai cike da Albarka da Ni'imomi Mai cike da Jarabawowi, Kada ka Shiga kai tsaye ba tare da ka koyi zama da tarbiyyan zaman ba.


Kamar yanda mata muke da kil bi-bi, da kissa da salon sace zuciya, Haka kuma ya kamata ace ku ke, Wajen soyantar da Mata kanku, da Sanya su jarabtuwa daku, da Son rayuwa inuwa daya daku, da biyayya.


Sau dayawa zakaji sun ce Mata suna wasu abubuwa, Amma shima in kaduba Mu'amalar sa da ita sai kaga dumbin gyara da baima san yana yiba,Wani kuma ya sani amma yana jin shi Shugaba ne dole tamar biyayya koda tana quntace, Domin mafi yawa na qasa shi ke quntata Sai ya qi yima shugaba biyayya, Amma in shugaba ya tsayu, Ya zama mai tarbiyya, Ya zama mai adalci da gaskiya, Ya kuma cire son ransa,Sai kaga mabiyi baya ko tunanin yi masa tawaye, Domin bai samu dalilin yin hakan ba in har shi din na kirki ne.


Kamar yadda kukeson Mace ta shiga Makarantar koyon ginin gidan Aure ta koyo tsarin gini ta gina muku gida Mafi kyawu da jin dadi, ta baku Nutsuwa da Rahama ta Kawar muku da dikkanin Qunci,To haka Zalika ku ma yaka mata ku shiga Makarantar koyon tuqa Motan Aure da sanin Qa'idojin tuqi da hanya.


Domin Namiji shine driver na gidansa, Mota da fasinjojin dik a qarqashin ikonsa suke, Dole ka koyi Motar da kyau, ka koyi saita ta akan titi, ka koyi kwana da dawowa baya, Ba wai kace fasinjojin ne zasu koya da gyara ba, Idan gyara ya kama kace duk su zasuyi, To Idan ma sunyi ba zai fa yi kyau ba har sai driver ya saka hannunsa aciki,Sunyi zufa da wahalar tare wajen ganin ta gyaru an cigaba da wannan tafiya mai Muhimmanci.


kuma dole ne Namiji ya rinqa sabis din Halayensa, da canza inda ya kamata a canza,da gyara abinda ya kamata agyara,Domin samun daman yin tafiya cikin sauqi cikin kwanciyar hankali, Kamar yadda Mace take yiwa Maigidanta kwaskwarima da sake mishi fenti dan yaji dadinsa. 


An baku daraja da fifiko, An baku Shugabanci Mai Muhimmanci, An baku Nauyi Mai wuyar dauka, An baku Kiwo abin tambaya. Kuma ko shakka babu idan kuka qi sauke wannan nauyi yanda yadace, Ku ka qiyin Shugabancin ku da adalci, To Allah zai Muku Hukunci dai-dai da irin hukuncin da zai yiwa wacce ya sanya aqarqashin ku, Domin Allah sarkin adalci ne. 


Maza 'Ya'yan goyo ne! Bama goyo ba, A'a Masu dadin goyo ne, Goyon da ba'agajiya dashi. To in har kuna son Matanku su goyaku, Sai ku zame musu yanda addini ya koyar kuma yace kuzama.


Allah Yasa Mudace.

4 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post