SAKON SAYYID ZAKZAKY (H) GA WANDA ZA SU YI AURE




KARANTA KA JI DAN UWA.

Allamah Sayyid Zakzaky (H) ya ce;-

"To sai kuma (nasihata ga) wanda ba su yi aure ba, ya kama mu yi iya kokarin mu muga cewa in za mu yi aure, to tun daga neman, ya zama mun daddage, mun ga cewa lallai an bi shari'a...

"Wasu (wai) akan dan sassauta musu, na san akwai malaman Kaduna, masu dan yin sassauci haka, in shari'a ta cika tsauri, in ka samu malami, ba ruwan sanyi (kawai zai zubawa shari'ar) ba, qanqanra ma yana iya zuba mata, duk abin ma ya baje gaba daya duk a huta! (Wato in shari'a) ta cika zafi, sai a dan sassautata.

"To, bai kamata (idan gidan Amarya sun jero al'adu a lokacin aure), sai a ce ka ga sun zubo mana al'ada, amma ya aka iya? Tunda ba da ikon ka ba ne, ka dan yi al'adar kawai, tunda Allah ya san nufinka, idan aka yi auren sai a canza!

"A'a! A'a!! Ya kamata ne a dage a ce ba za a yi al'adar ba! Shari'a za a yi!! Idan da muna yin wannan dagewar, da tuntuni mun kori al'ada (a aurarrakin mu), mu ne muke wa al'adar sassauci, shi ya sa har muke jin tsoronta, har kuma ta fi karfinmu!!

"Kowa sai ya ce wai al'adar haka nan aka ce (a yi ta), don haka in ba mu yi ba za a fasa auren! Alhali da za mu dake! Mu ce shari'a kawai za a bi! To da yanzu ba wanda ma zai yi tunanin ya kawo maka al'ada (a cikin hidimar aurenka)!

"Saboda haka kar kullum mu rinka tunanin wai wasu ne za su dage ba mu ba, mu din ne za mu dage!! In duk gaba dayanmu muka dage, to insha Allah an dinga yin aurarraki ta hanyar shari'a kenan, kuma ita shari'ar ita za ta gudanar da aurarrakin namu baki daya.

"To amma kuma in har a wajan neman aure ka yi masa "Assalamu Alaikum" da Al'ada, to zai fa ci gaba a al'adance ne, in ka yarda tun a wajan neman auren aka yi Al'ada, to kana cikin zaman auren za a kawo maka Al'ada, ba ka kuma isa ka ce a'a ba!

"Amma in tun farko ka dake! To su ma (dakarun al'adar) za su ji a jikinsu (dole su hakura su sallama maka)..... Wato in tun farko suka ga an ginu akan shari'a, to ba za su iya cewa a yi Al'ada ba.

"Wannan ya kamata ya zamo mun yi shi a aikace ne!".

Daga jawabin Allamah Sayyid Zakzaky (H) a ranar walimar bikin auren Alhaji Aminu Yabo (karin aurensa), shekarun baya a birnin Kaduna.

*TAMBAYA???*

Watakil wani ya yi tambaya cewa menene al'adu a cikin hidimar aure?

To Sayyid Zakzaky (H) duk ya bada amsa a cikin wannan jawabi mai albarka, ga abin da ya ce a tsakiyar jawabin nasa.

" 'Dan karamin misalina anan shi ne, har yanzu ana wasa da Sadaki, sai a yi wasu abubuwa bisa kimar yadda Al'ada ta tanada, daga ciki akwai wani abu;-

"Wai ko kayan na gani ina so!? A kai (gidan su Amarya).

"Da wani ko Rigar Uba ne? Shi ma a kai.

"Da wani wai ko menene na uwa? Shi ma a kai.

"A je a leka (yawon gaida dangin Amarya), shi ma a yi.

"Dangin Uba ma da akwai abin miqawa (kudin daukar Amarya).

"Da wani abu wai sunansa wai Baiwa.

"A zo a yi wani abu wai sunansa wai SA RANA!

"A zo kuma a yi wani abu wai sunansa wai KAYAN ASIN DA ASIN.

"A zo kuma a yi wani abu wai KAYAN AURE (KO LEFE!)

"Zuwa can a zo a ce wai a yi TUWON JIBI!!

"Zuwa can a zo a ce wai a yi TUWON BIKO!!

"Al'aduka iri-iri dai, duk a gama wadannan, amma wai in aka zo daurin aure, sai ka ji an ce SADAKI NAIRA GOMA!!!!!!!!

"Abin da addini ya yi tanadi, sai aka maishe shi wargi da wasa! Su kuma wadancan al'adu duk an sa ka'idojinsu, kuma (an ba su karfi tamkar addini ne su, ta yadda) in ba ka yi su ba har ma sai a ce an fasa auren!!

"A ce (ya za a yi mutum) ya kawo Sadaki, amma bai kawo kayan aure (Lefe) ba!! Ko kuma in ya kawo din a ce a kidaya a ga Turmin (zani) nawa ya kawo? Nawa ya dinka? Super Shadda nawa ya sa a ciki?

"Sai a ce ai a zamanin nan yayin kaza ake yi, sai ya sa kaza (da kaza a cikin kayan lefen)!!

"...... To (abin da ya kamata mu sani shi ne), idan Al'ada ta dauki matsayin shari'a, to kar kuma mu tsammaci samun lada (cikin hidimar)!

"To kuma auren mu zai zama bai da bambancin da na Katafawa kenan, tunda su ma sunayin aure na Al'ada!!".

(Mai karatu, Jagora (H) ya zuba bayani kan aure a wannan jawabi na auren Alhaji Aminu Yabo).

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post