Rayiwata tare da samarin zamani na yi nadamar abin da na aikata._ Zainab Yunis
Tare da ni Zainab Yunis


A lokacin da burin  kowacce ya mace ta samu muji na gari, me hakuri, ilimi, sanin ya kamata da duk kan wata suffa ta kamar cikar dan adam da kowacce ya mace ta ke hankoran ta sa mu a rayiwarta.


    Amman ni sai ya sha banban da ra'ayina

 Sau da yawan yan mata, ko nace mata masu irin fahimta irin tawa, sun sha ban-ban da sauran rayiwar sauran yan mata masu burin samun miji nagari. A ko da yau she babban burin masu irin fahimtata ya za'ayi mu aure wanda ya ke da kudi ba wanda ya ke da Kyawawan dabiu uba.


  Hakama, ta bangaren manema aure wato samari ko ma nace maza, akan samu acikin su, burin su shi ne, ya za'ayi su auri mace me kyau, doguwa me kyawun diri da tsarin halitta. Tare da cewar masu irin wannan ra'ayi basa, la'akari da cewar abu mafi muhimmanci ga da namiji, abu na farko shine, ya fara duba kyawawan dabiu, ilimi, tarbiya da makamantan su, sa'an nan koma menene ya biyu baya.


   A rayiwata na taso a gaban iyayena, duk kan wata tarbiya, da ta dace da cikar kamala ta dan adam, iyayena suna iya bakin kokarin su dan ganin na suffantu da irin wannan dabiu. Haka kuma mahaifina ya kasance me iya bakin kokarin sa akan mu dan ganin ya faranta mana da kyautatawa garemu domin babu laifi, mahaifina ya na da rufin asiri daidai bakin gwargwado, ta yadda babu abin da ya gaza wajan sauke hakkokinsa, da ya ke wuyan sa.

  Sai dai kash! Duk irin kokarin da iyayans su ke yi akaina tare da dukkan kannena, amman haka nasa kafa na yi fatali da shi,  a sakamakon tarayya da kawaye da muka hadu da su a makarnta tun ina matakin karatu na babbar secondry, bugu- da-kari tarayya da masamarin banza sun ta ka, muhimmiyar rawa wajan ruguzamin tarbiya ta. 

   Ko da ya ke, kamar yadda malam bahaushe ya ke cewa sai hali yazo daya ake abota, ko shakka babu haka abin ya ke.

A sakamakon irin burikan da kawayena suke naganin cewar  babban burin su shine su auri me kudi, domin shine abu da da ya fi da cewa da mu.


  Hakan ya sa ko da yaushe bani da wani burin da ya wuce ace na samu saurayi dan bana bakwai me kudi, wanda ake yi mu su take da suna, saurayi da kudi.

  Idan kuwa mu ka dawo  maganar zubi da tsari, da hasken Fata da kyawun halittar ya mace, babu abin da zan ce sai dai Godia, domin duk irin abin da ya mace ta ke bukata dan ganin ta burge na miji, to ni nasamu wannan damar.

 Hakan yasa samari daban daban, ke zarya a kofar gidan mu, wanda na tabbatar da cewar bazan iya sanin adadin samarin da nayiba, tun  kafin ace na kammala karatun babbar secondary. Duk da irin samarin da suke turu-ruwar zuwa wajana, neman aure na, wasun da gaske su na sona da gaskiya kuma suna burin aurana, amman babban  ma'aunina shi ne, ya ya nauyin aljihuka kadarori nawa ka mallaka? ko kuma me mahaifinka ya mallaka? Wanene babanka ?.

   Duk sa'ar da iyayena suka bikaci na fito da wanda na ke so, su yimin aure, duba da yadda ake tururuwan zuwa wajena,  neman aurena, amma haka zan nunuwa iyayena cewa ni duk cikarsu har yanxu babu wanda yayimin. Madamar ban samu yadda na ke so ba.

  

   Domin ni a bisa tsarina ina son na auri me kudin da za'ace, yau mu na, Dubai, gobe,  mu na USA, citta mu na Switzerland, da dai sauran kasashen da suka cigaba, domin dai don yawan bude idanu. Tare da cewar duk irin wannan burin nawa da na ke cike da shi fal zuciya, iyayena ba wasu ba ne, sai dai rufin asirin da mu ke dashi. 


  A kwana a tashi yau da gobe kamar yadda malam ba haushe ya ke cewa yau da gobe, ta fi karfin gaban wasa, shakka babu, na yi samari masu yawan gaske, yayan masu kudi wanda ni kaina bazan iya taskace adadin suba, tun ma kafin na karasa babbar secondary. Takai idan iyayena suka turani makaranta, ba na zuwa sai dai nabi saurayin da muka shirya fita da shi a wannan rana, tun ina yi aboye, harkai ga iyayena sun fara gane me nake aikatawa. Har sai da takai ina bayar da kaina ga maza, indai na tabbatar da cewar zan ssmu kudi, masu yawa, wanda ba iya samari kadai ba, a wasu lokutan har da manyan mutane, wasun a haife sun haifeni, wasun su ma, sun yi jika dani, amman haka su ke har dani sabo da irin kyawun da Allah yayimin da tarin farin jini da na ke dashi, duk da cewar ina da mafi karancin shekaru a wancan lokacin, da bazan iya gaza shekara 20 ba, zuwa shekara 22 ba. Amma haka mu ke wannan harka ni da kawayena. 


  A mafi karamin farashi ga duk wani mutumin da zan bashi kaina, saurayine ko babban mutum, shine Dubu Hamsin sai kudin magunguna na mata, wanda ba zai gaza dubu 30 ba, wanda irin wadannan magunguna, matar aurece ya kamata ace ta yi amfani da su a inda ya da ce domin mijinta, amman mu haka muke amfani da su duk inda mu ka ji labarin wani magani mata, haka za mu nufi wannan wajan, domin mu habbaka har ko kin mu na yau da kullum da mu ke ai katawa, idan kuwa a ka ce babban mutum ne, na kansamu kudi fiye da yadda ake biya na.


   A irin wannan harka ne, yau da gobe da irin mu'amala da maza daban daban da na ke ne ya sa har ta kai, da ya jani da na fara shaye-shaye, tun bani da ra'ayin haka har bin ya zamomin jiki, ta kai ma idan ma ban sha ba, ba najin dadin gudanar da dukkan wasu harkokina shakka babu kawayena sun taka muhimmiyar rawa wajan jefani cikin irin wannan ya na yi da na tsinci kaina. 


  A kwana a tashi, da iyayena su ka fahimci irin halin da na shiga, duk irin Nasiha, Fada, kai wani lokacin har da duka amman duk da haka bai sa, na sauyaba, idan ma na sauya kwana biyu ne daga nan sai na koma gidan jiya, halin da yasa su ka yanke shawarar, za su saurar da ni, ga duk wanda suka aminta da shi. 

  Da jin irin yadda iyayena su ke da niyar aurar dani, karshe, naga cewar na gudu daga gidan mahaifana na shiga duniya, wanda nasamu wannan karfin guwane daga cikin samarin da muke irin wannan harka da shi, da ya ke ya kasan ce me kawomin abokan harka masu kudi musamman ma manyan mutane, karshe dai haka ya kwararamin guwa nabar gidan mu, na shiga duniya, domin mena rasa a rayiwata, da dukkan wata ya mace take nema a duniya ni me na rasa, da wannan dalili ne yasa, yasa na bar gidan mu ya kara da cewa "me zaisa iyaye suke takuramana? baza abar mutum ya sakata ya walaba". hakan tasa karshe na karbi duk irin zigarsa da yayimin karshe haka na tarkata kayana na gudu babban birnin da ke kasar mu, 

Ta sanadiyar wani babban mutum da ya ke wulda da ni, wanda shi wannan babban mutum mun hadu da shi a wani wajan shakatawa da ya ke jahar mu.


   Ta kai da cewar shi wannan babban mutum duk lokacin da nayi burin barin kasar da na ke domin muje yawan shakatawa ko wacce kasa na ke so haka zai siyamana tikiti na jirgi muje shan mushakata, idan ma bikin karin shekarane to a can za muje muci duniyar mu da tsinken mu. iyayena kuwa tun suna kirana a waya su yimin nasiha kan cewar na dawo gida, karshema na dai na daga kiran su kwata kwata, har sai da Takai sun fauwala Allah al'amuran su. 

 

   A irin wannan lokaci yau da gobe, na debu shekaru masu dama da shiga ta danuyi, iyayena duk irin yadda zasuyi suga cewar sun tseran da ni daga cikin irin wannan yanayi takaima da sun hakura sun fauwala Allah. A na cikin haka mahaifina ya rasu, bayan wata 5 da sati uku itama mahaifiyata ta bishi, wanda ba na raba dayan biyu cewar bakin cikina ne yasa suka rasa rayiwar su, amman duk da mutuwar su, ko gida ban taba tunanin najuyaba, domin daula ta zauna, auran ma ni bashine a gabana ba, domin ina ganin cewar ko zan yi aure sai na shakata da walawa in yaso daga bisani nayi aure.  Su kuwa kannena  mata, tuni suka koma hannun yayan baban mu, har sun girma an aurar da su. Tabbas, mutuwar iyayena lokaci bayan lokaci ta na raina, amman hakan baisa na sadudaba. 


  Wata rana bazan mantaba daran asabar wayewar garin asabar, mun shirya wa fita ta musamman ni da wani saurayina da muka hadu da shi a babban birnin tarayya na kasa ta, daga bisani  bayan mun kammala siye-siye da muka yi, a wani babban katafaran kasuwar zamani, da misalin karfe 8:45pm na dare daga nan mu ka zarce wani babban Otal, wanda shine Otal mafi tsada a wannan babban birnin kasata. Isar mu ke da wuya da misalin karfe 9:21pm na dare, duk da cewar mun saba zuwa, isar mu ke dawuya aka bamu number dakin da zamu kwana tare, bayan mun isa dakin da aka bamu, shigar mu ke da wuya mu ka ajiye kayayyakin da muka siya, batare da bata lokaciba mu ka yi wanka muka ci abin ci me rai da lafiya mukasha lemuka na alfarma. Karhe muka gudanar da abin zamu aikata na lalalat. Bayan mun kammala bacci ya dauke mu gaba daya. 


   Ba mu dauki wani lokaci me tsayiba da bacci ya kwashe mu, ni dai bansan me ya faruba kawai sai na yi mafarki da mahaifiyata a cikin wani irin mummunan yanayi me tayar da hankali, ta yadda ban san irin yadda zan iya kwatan ta, halin da naganta s ciki ba, ta na kuka matsanan cin kuka, me ts yar da hankalin duk wanda ya jishi, a yanayin kukan da take sautin kukan ta ya kasance duk ilahirin wajan ya na amsawa, cikin irin wannan hali ta dube ni ta ce da ni, "yanxu  wance irin  abin da ki ke, aikatawa ke nan? A yayin da ta ke fadar haka, gaba da ya wajan ya amsa, nan ta ke tsananin hali na tsoro da figici ya dada kamani bansan lokacin da na kece da matsanancin kuka a cikin wannan mafarki ba. Nan ta ke na nufi wajan da mahaifiyata ta ke a tsaye, na nufin wajan da gudu, nan ta ke sai naji an dakamin tsawa da wata  murya, gaba daya wajan ya amsa, aka ce na tsaya kar na karasa wajan ta, ga shi ga ba daya wajan baka iya ganin komai a wajan sabo da tsananin duhu, sai a wurin da Mahaifiyata ta ke tsaye anan zakaga wani haske kadan ba wani me yawaba, ya nayin gurin kuwa wani irin gune wanda hatta kasar wajan bakikirin ce ta na, kyalli kamar bakin tabo ne da yayi tudu da kwari gaba daya wajan haka ya ke, ga  wani irin nau in zafi, hade da turiri da ya ke tasowa daga cikin karkashin wannan kasar. Na tafi da gudu kenan zan nufi wajanta wannan sauti da aka dakamin tsawa da shi, nan ta ke na yanke jiki na fadi, a irin wannan ya nayi ina rusa kuka kamar raina zai fita, ina kiran sunan mahaifiyata da karfi, ina mika hannuwana domin neman tai mako, amman sai sautin dariya ka keji cikin isa sautin dariyar ta kai ga na iya jure sauraro haka na toshe kunnuwan hannu bibbiyu, amman ji ku ke kamar an zo kusa da kunnuwan ana yimin wannan dariya. Amman duk da irin wannan dariyar baisa na dai na jin muryar mahaifita ba, ta ciga da cewa, "yan zu kina ganin wannan abu da kike aikatawa ya da ce da irin  tarbiya da muka baki"? Me ki ke so a duniya haka? Mene bamu yi miki ba? Wanne hakki ne ba mu sauke a wuyan kiba? Wanne hakkine muka gaza sauke miki shi? nan ta ke mahaiyata cikin kuka me tsanani, ta ce ki tuna da cewar, ita duniya ba wurine na tabbata ba, duk irin abin da kika aikata na alkhairi da sharri idan kinzo sai kin ganshi, ita rayiwar duniyr kwana nawane? Duk irin tsawan ran da aka baki za su kare kizo kiriskemu, ita duniya kwatankwacinta kamar kasuwa ce, kowa ya ci kasuwa gida ya ke ta fiya, a lokacin da wasu suka tafi gida a lokacin wasu suke shigowa, kuma idan sun gama duk cikarsu gida jansu zasu koma. Irin yadda naji mahaifiyata ta ke irin wannan maganganu haka yasa na dada rushewa da kuka, mahaifita ta na kara cewa da ni, ko kinsan adadin mutunan da suka ci kasuwa suka dawo gidajan su duk muna tare da su? Ita al'amarin duniya da abin da ke cikinta, kamar kamar kayayyakin da ake siyarwane akasuwa, yau da gobe komai zai kare kasuwar ma za a rasata ne, wanda ya ci riba ya ci wanda ya yi asara yayi asara, ita mutuwa ba gaggawa ta ke ba bakuma ta manta da kowa bane, tana sane da kowa. 

 domin duk ilahirin gurin da mahaifiyata  take ciki duhune dindin dan hasken ma da ke wajan ta ya bace baki daya babu wani haske acikin sa, sai zatin mutum ne kawai zaka iya gani, duk irin kalmar da take fada duk gun haka ya ke amsa kuwa a wajan. 

Ta dubeni ta ciga ba da cewa "wance ki tuna rayiwar duniya rayiwa ce gajeria idan har kina mantawa da mutuwa to tsufa yanan a lokacin da babu wani me shawar ki da zai kusance ki a wannan lokacin, an manta da ke zamanin ki ya wuce, sai dai idan ana maganar  tarihi a tuna da ke, a lokacin ne za kiyi da na sanin da baki cikin abin da kika aikata abaya, a kuma lokacin da zaki bikaci yin aure a lokacin mijin aurema zai gagare ki. kafin ta karasa can a gefe guda sai naji wani irin sautin kuka me ratsa kwakwalawa, kukan ya zamo duk kan wajan ya na amsawa, ga wasu irin abubuwa daba zan iya musulta kamaninsu ba, suba jajaye ba su ba bakakakeba duk sun mamaye ilahirin wajan, da jin sautin wannan kuka kamar ance dani na duba gefena kawai sai naga maifina nanane ya tsaya akaina ya na matsanin cin kuka, duk da ina kwance a wannan wurin sakama kwan wannan tsawar da aka da kamin takai ga na fadi na kasa tashi, sabo da tsananin tsoro da nake ji a wannan lokacin ina neman tai mako, domin wanda zai taimakamin jin muryan mahaifina na tafi da jan jiki zuwa wajansa, ina me cewa Abba ka taimakamin cikin sauti me tayar da hankali dauke da kuka me gigigitarwar gaske, na yi yin kurin na tashi domin na nufi wajan abban na, amman ina tashi ma ya gagara sabo da tsananin tsoro, duk irin kuka da nake da neman taimako amman abban na bai saurareni ba, shima kawai kuka ya ke, sai jimla da ya da naji ya fada cewar " wance ke ma za kizo gurin da mukazo, karshe da shi da mahaifiyata suka ka da kai sukata fi abin su, suka barni ina kwance irin wannan yanayi, ina kuka ina kiransu da karfi amman ko su waiwayo su kalleni tun ina ganin zatun su takai da na dai na ganin komai, nan ta ke naji wani irin rugugugi me karfin gaske takai ga naji kasar wajan ta na amsawa halin da wannan abu ya kara firgitartar ni fiye dada, ga wata irin mummunar dariya na yin kura zan tashi na bisu amman ina tashin ya gagara haka na ke mika musu hannuwana ina ihu domin  neman taimakon su, amman inaa, halin da dukkan wajan ya ke amsawa cikin babbar murya da kuma karamar murya kasa kasa takai da kunnuna sun kasa sauraran wannan mummunar dariya haka na toshe kunnunawa ina ihu kamar raina zai fita. Haka na farka a gigice, zan fita da gudu. 


 Nan ta ke naji wanda mu ke tare da shi a gado guda, a cikin wannan Otal ya rikene ya na cewa da ni wance lafiya me ya faru, amman duk irin maganar da yake dani ya kideme nima na kideme ina kokarin na tashi na fita da gudu shikuma ya na rirrikeni amman ihu na ke yi, tambaya ta ya ke wance menene me yasameki amman bana iya sauran abin da ya ke fada banda kuka babu abin da nakeyi tare da rusa uban kuka. 


A dai dai wannan lokacin a she gari ya waye, wanda ni bazan iya tantance karfe nawa ma a wannan lokacin, shi kuwa wanda mukaje tare da ni da shi, tambaya ta ya ke me ya faru, amman ko sauraran sa ban yiba haka ya biyoni da ga shi sai zanin dauraya karshe dai da yaga za a fahimci wani abu karshe ya koma ya sawo kayansa kafin ma yafito tuni na samu abin hawa na nufo gidan da aka kamamin haya dake babban birnin kasa ta, a ranar haka na tarakata inawa inawa na dawo garin mu gidan yayan mahafina sai ganina su kayi  bazato ba tsammani Allah yasa yayan maifina ya na gida a wannan rana, na je na rungumeshi ina kuka ma tsanin cin kuka, in cewa baffa ka gafaratamin na yi na damar abun da na aikata halin da yasa yadda matansa da sauran yayan sa sukaga halin da nake ciki suma abin yasa su kuka. 

  Karshe dai bayan kwanabiyu na ke bayar da labarin abin da ya faru yanxu haka ina gidan yayan babana duk lokacin da natuna irinwannan mafarkida na yi, da irin abubuwanda na aikata a baya duk irin farin cikin da nake gabadaya sai ya rikede ya koma bakin ciki sai dai aga awaye ya na zubawa a idanuwana,


Ina fatan wannan zai zamo darasi ga yan baya..


Rubutawa da tsarawa Habib Nasrallah

Email habibrabiu81@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post