RABON GADO (inheritance) A MUSLIMCI (21) !!!@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WA YA KAMATA A FARA CIRE MASA KASO DAGA CIKIN MAGADA  ?

Tambayar da wasu ke fara yi kenan in anzo rabo gado ga magada, wai kason wa ya kamata a fara cirewa kuma wanene zai zo a qarshe wajen cirewa ?

To, abinda dai yazo cikin Al-Qur'ani game da rabon gado shine, ana farawa ne da cire wasiyyar da mamaci yayi ko kuma bashin da ake binsa. Idan an cire wasiyya ko bashi, to, yanzu abinda ya rage/saura shine za a kasawa magada (hairs) gwargwadon kason kowa. 

WANDA ZA A FARA CIRE MASA KASONSA 

Abu na farko da za a fara dubawa shine, cikin magadan wanene aka ambaci kasonsa cikin Qur'ani daga wadanda mamacin ya bari? Idan aka sami wanda aka ambaci kasonsa, to, daga kansa za a fara, abinda yayi saura kuma sai a raba shi tsakanin wadanda ke samun saura bayan an cirewa masu kaso kasonsu, sai su din a raba musu gwargwadon yadda Allah yace a raba musu. Za mu bada misali. 

Idan kuma har ya zama cikin magadan kowa na da kaso ambatacce cikin Al-Qur'ani, to, anan babu wanda za ace ta kansa za a fara, sai dai kawai a dukiyar bisa yadda kason kowa ya nuna. Wajen dauka kuma babu wata matsala, ko ma wanene ya fara dauka ba zai zama wata matsala ba ga sauran magada. 

                   MISALI

                 ---------------

Bari mu kawo misalai a qalla guda uku (3) muga yadda abin zai kasance. 

(1)- Mutum ne ya rasu ya bar Uwa da Uba da kuma 'ya'ya maza biyu (2) da 'ya'ya mata uku (3) tare da dukiya #6,000,000.

To, anan tunda cikin 'ya'yan akwai maza zai zama dukkansu ('ya'yan) sun zauna ne a gefe su saurara a gama cirewa dukkan mai kaso kasonsa, abinda ya rage/saura kuma sai su raba, namiji ya dau kaso biyu (2) na 'ya mace. 

YADDA KASON ZAI KASANCE 

   Uba      Uwa    'ya'ya 

      1            1

     ___   +   _____   saura

      6             6         πŸ‘‡πŸ½

      1     +      1         πŸ‘‡πŸ½

    ______________     πŸ‘‡πŸ½

                 6

Kenan Uba zai sami kaso daya (1) daga cikin kaso shida (6), Uwa ma haka. 

        KASON    UBA 

  1      #6,000,000

___ *  _______=#1,000,000

   6             1

           KASON UWA 

  1    #6,000,000

 ___ *  _______=#1,000,000

   6            1

Abinda ya saura shine kaso hudu (4) daga cikin shida (6), wanda ya kama #4,000,000.

Saboda haka tunda 'ya'yan su biyar ne, mata uku maza biyu, sai a raba wannan #4,000,000 gida bakwai (7), kowacce 'ya mace a bata kaso daya (1), namiji kuma a ba shi kaso biyu (2).

#4,000,000/7=#571,428

Ya zama kowacce 'ya mace za ta sami #571,428, namiji kuma ya sami #1,142,856.

(2)- Mutum ne ya rasu ya bar 'ya'ya mata uku da Uwa da Uba tare da dukiya #3,000,00.

To, su wadannan magada kowa na da kason da aka ambata masa, wato iyaye kowa na da kaso daya (1) daga cikin kaso shida (6) na abinda aka bari, su kuma 'ya'ya mata suna da kaso biyu (2) bisa uku na abinda aka bari, wato babu wanda aka ce saura zai samu. 

Saboda haka za a kasa dukiyar ne kawai gwargwadon kason kowa, sai a bawa kowa abinda ya samu. 

YADDA KASON ZAI KASANCE 

UBA   UWA  'YA'YA MATA 

   1        1               2

 ___    _____        _____

   6        6               3

   1   +   1               4

 ___________________

                  6

Kenan za a kasa dukiyar gida shida, sai a dau kaso dai-dai daga ciki a bawa Uwa da Uba, sauran kaso hudun (4) kuma sai a rabawa 'ya'ya mata daidai-wa-daida. 

         KASON UBA 

 1     #3,000,000

__ *  ________=#500,000

 6            1

       KASON UWA 

 1   #3,000,000

__ * ________=#500,000

 6           1

Ya zama iyaye sun tashi da #1,000,000, sauran #2,000,000 kuma sai a rabawa 'ya'ya mata uku don kowacce ta sami kasonta. 

#2,000,000/3 = #666,666.

Kowacce 'ya mace tana da #666,666 kenan, gaba daya jimla ya zama #1,999,998. Abinda ya rage daga #2,000,000 shine #2 wacce ba za ta rabu ba. 

(3)- Mata ce ta rasu ta bar Miji da dan'uwa shaqiqi (full brother, whose share the same father and mother) da kuma dan'uwa Li'ummi (whose share the same mother only),  tare da dukiya #2,000,000.

To, anan za a fara cire kason Miji ne da dan'uwa Li'ummi (whose share the same mother), domin  su suna da kaso wanda aka ambata musu. Shi kuma dan'uwansa shaqiqi ba shi da ayyanannen kaso (specific share), saboda haka shi yana samun abinda ya saura/rage ne komai qanqantarsa kuma komai yawansa. 

YADDA KASON ZAI KASANCE 

 MIJI   LI'UMMI  LI'ABI 

    1           1            πŸ‘‡πŸ½

  ___        ___        Saura 

    2           6             πŸ‘‡πŸ½

    3    +     1            πŸ‘‡πŸ½

  _____________________

                  6

Za a kasa dukiyar kaso shida (6) ne,  a bawa miji kaso uku (3), dan'uwa Li'ummi (wanda suka hadu ta bangaren Uwa) kuma kaso daya (1). Ya zama an cire kaso hudu (4) kenan daga cikin shida (6), sauran kaso biyun (2) kuma shine kason dan'uwa shaqiqi (wanda suka hadu ta bangaren Uwa da Uba) .

   KASON  MIJI 

 3    #2,000,000

__ * _______=#1,000,000

 6        1

  KASON 'DAN'UWA LI'UMMI 

 1     #2,000,000

___ * ________=#333,333

  6            1


KASON 'DAN'UWA SHAQIQI 


  2     #2,000,000

___ *  _________=#666,666

  6             1

Insha Allahu kamar haka kason zai kasance. Allah ya qara ganar damu gaskiya tare da bamu ikon binta. 

πŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌ

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.

         (08137925034)

21st November, 2022/  27th Rabi'us-Sani, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post