NASARA SAKAMAKON WAQI'AR GYALLESU 2015 !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ALJANNU SUN FAHIMCI DA'AWAR SAYYID ZAKZAKY (H) 


Fadi ne na Allah (T) cewa duk wani tsanani na tare da sauqi, kuma nasara na tare da duk wanda yayi haquri yayi juriya. 


Annabi Muhammad (S. A. W. W) ya sami kyakkyawan shaida tun daga halin quruciyarsa har zuwa cikarsa shekaru arba'in (40) bai taba fuskantar qaryatawa daga mutanensa ba, amma lokacin da yazo musu da kalmar kadaita Allah shi kadai a matsayin abin bauta kuma wanda ke cewa ayi ayi, ko a bari a bari. Wannan siffa ita ce ta Sayyid Zakzaky (H) a halin quruciyarsa har zuwa lokacin da ya shelanta bara'arsa daga bin dukkan wata doka wacce ta saba ta Allah (S. W. A). 


Daga wannan lokaci ya soma cin karo da matsaloli bangaren masu mulki da kuma wadanda ke ganin kansu a matsayin maluma. 


Sayyid Zakzaky (H) ya cigaba da shelanta wannan bara'ah tasa ba tare da jin tsoron dukkan wani abinda zai same shi a rayuwarsa ba har zuwa wannan lokaci da muke ciki. 


Annabi (S. A. W. W) bai tsaya iya cikin garin Makkah da Da'awarsa, garin da ya fara shigarsa don neman mataimaka kan wannan da'awa tasa shine 'DA'IFA. Da ya shiga wannan garin ya bayyana musu dalilin shigarsa maimakon su taimaka masa ko nuna rashin amincewarsu sai suka cutar dashi iya cutarwa. 


Cikin wannan gari na 'Da'ifa aka fara zubar masa da jini har ya zama takawa/tafiya 🚶ba ya iyawa saboda raunatawar da suka yi masa. Kan hanyarsa (S. A.W.W) ta dawowa gida ya zauna qarqashin wata Bushiyar Dabino yana hutawa kuma yana karatun Al-Qur'ani. 


HADUWARSA (S. A. W. W) DA ALJANNU 


Da shike Allah ne mai yi ba wani ba, yayin da mutane suka qi taimakonsa sai ga jama'ah daga Aljannu sun taru suna sauraren karatun nasa, kuma suka koma garuruwansu suka cigaba da Da'awa irin tasa (S. A. W. W). 


Shine Allah (T) ya bamu labari da cewa :


" وَاِذۡ صَرَفۡنَاۤ اِلَيۡكَ نَفَرًا مِّنَ الۡجِنِّ يَسۡتَمِعُوۡنَ الۡقُرۡاٰنَ‌ۚ فَلَمَّا حَضَرُوۡهُ قَالُوۡۤا اَنۡصِتُوۡا‌ۚ فَلَمَّا قُضِىَ وَلَّوۡا اِلٰى قَوۡمِهِمۡ مُّنۡذِرِيۡنَ‏ ."


" KA (tuna yaa Muhammad) YAYIN DA MUKA JUYAR DA WASU JAMA'AH NA ALJANNU ZUWA GAREKA SUNA SAURAREN ALQUR'ANI. YAYIN DA SUKA HALARTO SHI (gurin da kake karatu) SAI SUKA CE : " KUYI SHIRU ". YAYIN DA KA QARE (karatun) SAI SUKA JUYA ZUWA GA JAMA'ARSU SUNA WA'AZI (a matsayin masu taimaka maka wajen isar da saqon da mutanenka suka qi amsa maka). "


And [mention, O Muhammad], when We directed to you a few of the jinn, listening to the Qur'an. And when they attended it, they said, Listen quietly. And when it was concluded, they went back to their people as warners.


            (AHQAAF:29)WAQI'AR GYALLESU 2015


Zantuka mafiya rinjaye shine, sanadin wannan waqi'ar an kashe/shahadantar da almajiran Sayyid Zakzaky (H) 1000 +, wanda Alqali bai kawo cewa sun kai 2000 ba har ma da shaidan da aka riqa samu bayan waqi'ar. 


Wani abin mamaki da al'ajabi shine, duk da irin wannan kisan gilla da raunatawa da cin zarafin da aka yiwa Sayyid (H) da almajiransa bai tsoratar da al'umma wajen fahimta da amsa wannan Da'awa tasa ba.


Adadin jama'ar da suka qaru cikin wannan da'awa sun nunnunka Adadin wadanda aka rasa sakamakon wannan waqi'a. 


Babu mai kokonto cewa duk wani Annabin da aka aiko yana samun amsa kira daga Aljannu, kuma suka taimaka maka wajen isar da saqon nasa cikin jama'arsu.


Saboda haka muminai masu yawa daga Aljannu sun sun qara fahimta da amsa kiran Sayyid Zakzaky (H) bayan wannan waqi'a fiye da wadanda suka amsa masa kafin ta.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


6th November, 2022/ 12th Rabu'us-Sani, 1444.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post