NASAN BA KOWA NE DOLE SAI YAYI 'SACRIFICE' BA. IN KALILAN SUKA YI, YA WADATAR._Shaikh Ibraheem Zakzaky (h)

 


_EMSANEEY _

Na san ba kowa ne dole sai yayi 'sacrifice', ba. In kalilan sukayi, ya wadatar. Dalilin da yasa 'society' Dinnan ta zauna yadda ta zauna, saboda kalilan din sunki suyi ne; kowa yace, nafsi- nafsi; kaina-kaina! In kuma muka tafi a haka nan, to kullum zamu dinga ganin abubuwa suna dada lalacewa. Yanzu duk dan Nigeriya wanda yake mustawa shekaru, banda yara kanana, wadanda su basu san wannan ba, amma duk wanda ya san 50s ya san 60s, ya san 70s, ya san 80s, ya san meke faruwa.

Yanzu in muna ba yaranmu labarin 60s sai suyi ta mamaki. Su yi wani ha! Aka yi haka nan a nan? Wai da tafi yanzu. Don Allah a ina ake wannan banda wannan al'ummar? Wai da tafi yanzu. Ko'ina ci gaba akeyi banda wajenmu, mu ci baya muke. 'Reverse'! Kasan kuma yadda 'reverse' yake, yafi gudu. A guje ake komawa baya. Ko yanzu mun koma 1930s ban sani ba don yanzu ci baya muke yi.

A takaice sakon da muke cewa shi ne ya kamata kowannenmu yaga menene zai sadaukar? Wannan ninancin ya barmu. Kowannenmu yayi tunanin wace gudunmawa zai bayar wajen ceto al'umma? Kuma ya bayar da gwargwadon abin da zai bayar. Insha Allahu wannan al'umma baza taci gaba da zama a yadda take ba.

____Wani bangaren na jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) daya gabatar a Hussainiyya Bakiyyatullah Zariya 2014.____

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post