Musulunci ya Magance Kabilanci Don Haka Bama Da Bukatar Kabilanci_Cewar Sheikh Yaqoub Yahaya Katsina.



___Daga Hassan Abubakar Ahmad Ɗan Sister Kt.

Tana Iya Yuyuwa Mutum Yace Ta Fuskanci Addini Duk Cikanmu Mu Ba Musulmi Bane Baki Ɗayan Mu, Duk Cukarmu Akwai Musulmi Akwai Waɗanda Ba Musulmi Ba Wato Akwai Kiristoci. Misali; To Ya Za Ayi, Ayi Zamantakewa Tsakanin Musulmi Da Kirista?

To Ai Sassauƙan Abu Ne, Shi Yafi Komi Sauƙi Saboda Miye? Su A Halil Kitabune Ma'abota Littafine Ma'ana. Muma A Halil Kitabune Ma'abota Littafine, Suna Da Littafi Muna da Littafi. Wanda Ya Saukar Da Littafinmu Da Wanda Ya Saukar Da Littafinsu Kwara Ɗaya Ne, Shi Ne Allah Ta'ala.

Ba Yuyuwa Allah Ta'ala Ya Saukar Da Littafi, Ya Saukar Da Attaura, Ya Saukar Da Injila, Ya Saukar Da Al'Qur'Ani, Ya Saukar Da Zahura, Kuma Yace Kowa Yana Da Dama Yayai Masa Adddin Bisa Fahimtar Sa, Duk Da Dai Ance Mu, Mu Kira Wasu In Sunzo Falil-lahi-hamdu. In Basu Zo Ba Mu Barsu Kan Abunda Suke A Kai.

"Ya Ku A Halil Kitabi, Ya Ku Ma'abota Littafi Kuzo Mu Haɗu Da Ku A Kan Kalma Guda Daya Ita Ce La'ila-Wa'Illallah, Sanan Karda Ku Riƙemu Iyayen Gijinku, Karda Mu Riƙeku Iyayen Gijinmu. Wato Duk Cukarmu Bayin Allah Ne."

To Ba Yadda Za Ayi Wanda Ya Saukar Da Waɗannan Littatafai Ya Zama An'namimi, Ba Zai Yuyuba. Yace Kowa Yana Damar Ya Yi Dai-dai Gwargwadon Abunda Ya Fahimta Ko Yai Imani, Ya Bautawa Allah Da Abunda Ya Fahimta Sannan Kuma Allah Ya Hadamu Faɗa. Zaiyuyu? Ba Zai Yuyu Ba Don Ba A Taɓa Yi Ba.

Na'am Zai Iya Yuyuwa A Samu Faɗa Amma Da Sharadi, Lokacin Da Kirista Yace Sai Ya Mayar Da Musulmi Kirista Da  Ƙarfin Tuwo Ana  Iya Samun Matsala. Lokacin Da Musulmi Yace Sai Ya Mai Da Kirista Muslim Da Ƙarfi Tuwo Ana Iya Samun Matsala. Wanda A Yanzu Wannan Kasar Bama Wannan Maganar Akeyi Ba. Ita Wannan Maganar Rabon Da Ayi Ta Har An Manta, Bama Ita Bace Gaban Mutane Ba.

Amma Kuma A Lokaci Guda Suna Faɗa, Sai Ace Ana Faɗar Addini Ana Faɗa Tsakanin Kirista Da Musulmi. Sai Muce A'a Kuna Dai Faɗanku Na 'Yan Siyasa, Faɗan Siyasa Kukeyi Wacan Yanki Ko Wancan Ƙabila Ko Wancan Mai Addinin Yafi Samu Kuri'a Ko Yafi Yasamun Bajat, Ko Yafi Samun Kudin Shiga, Ko Yafi Samun Tasiri, Ko Yafi Samun Muƙami. Sai Wannan Yaji Haushi Sai Wannan Yaji Haushi. Haka Haka Har Faɗa Ya Fara Sai Kashe-kashe, Sai Ace Anyi Faɗan Addini Ƙarya Ake Ma Addini Ba Faɗan Addini Ba Kenan.

Faɗan Addini Kamar Yadda Nayi Bayani; Shi Ne Wani Yayi Kokarin Mai Da Wani Addinsa Da Karfin Tuwo. Jahadi Kenan, Toh Yanzu In Kace Azo Ayi Jahadi Sai Ka Samu Musulmi Ka Raba Mashi Makaimai Kace Aje Ayi Jahadi, Kana Tsammanin Ina Za'a? Wani Masallaci Zayaje Ya Buɗe Wuta Saboda Ma Yana Gani Dukkansu Bama Musulmai Bane. Ko Ba Ka Lura Ba, Wani Coci Zai Je Ya Buɗe Wuta Basuyi Masa Lefin Komi Ba Sai Yaje Ya Buɗe Masu Wuta.

Saboda Miye Saboda, A Irin Wannan Yanayin Da Muka Samu Kanmu Cikinsa Mutane Basu San Waye Ma Maƙiyinsu Ba. Da Ace Mutane Sun San Maƙiyansu Da Kirista Da Musulmi Fa Sun Haɗe Kansu A Matsayin Su Na Masu Mutunci Da 'Yanci, Su Kwaci Ƴancinsu. Amma Basu Sani Ba Shiyasa In Kabasu Makami Kansu Zasu Kashe.

Dukk Lokacin Da Mutane Suka Gane Waye Makiyinsu Zasu Gane Cewa; A Lokacin Zasu Ga Ne Ashe Ma Ba Kirista Bane Maƙiyinsu Ba. Ashe Bama Ƙabila Kaza Bane Maƙiyinsu Ba, Ashe Ma Ba Kaza Bane Maƙiyansu Ba. Zasuga Haƙiƙanin Maƙiyinsu, Haƙiƙanin Maƙiyinsu Shi Ne Zalunci Da Tsarin Da Zalunci Ya Kafa. Shi Ne Haƙiƙanin Makiyinsu Kowaye Yake Jan Wannan Ragamar Ta Zalinci Kirista Ne Ko Musulmi Shi Ne Maƙiyinku...

Wanda Ya Rike Tattalin Arziƙin Ku A Hannu, Wanda Ke Kaɗa Rayuwar Ku Yadda Yaga Dama, In Ya Ga Dama Yace Karfe Goma Ku Shiga Gida Ku Rufe In Ba Haka Ba Zai Buɗe Wuta. Wannan Shi Ne Maƙiyinku Shi Ne Azzalumi Kenan... Ba Inda Allah Ya Hana Dokar Hana Yawo Da Dare, In Kace Ai Babu Tsaro Suwaye Suka Kawo Rishi Tsaron.? Su Masu Kawo Hari Suwa Suka Samar Dasu:? Wa Sukeyi Ma Aiki? Ma'aikatane Masu Kawo Harin... Mi Ya Kawo Su? Akwai Waɗanda Suka Kawosu..

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post