MULKIN MALLAKAR BATURE:

 


- Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)

To, fakam da yawa idan ana magana dangane da mulkin  mallaka, mutane suna mishi hange daban-daban, suna ganin Bature ya zo nan qasar ne ya samu Sarakunan qasashen nan suna mulkin danniya. Kuma ya samu wadansu mutane musamman na kudancin qasar nan (wanda ba su da zaunannun dauloli), suna riqe da wadansu ‘taqalidai’ da al’adu wadanda suke wadansu abubuwan da su daidai ne a wurinsu, amma 

Bil’adama, ko ma mu ce; dokokin (zamantakewa) na duk duniya na ganin wannan abin ba daidai ba ne. 


Kamar kashe tagwaye, da daukarsu miyagun Alkhaba’is, da wadansu 

abubuwa da suke yi irin wannan.

Fakam da yawa mutane sukan ta kawo batun cewa kamar Bature shi ya zo ne ya kawar da wadannan abubuwa, ya kawar da zalunci ya kawo tsari na adalci a qasa. Kuma ko ba komai shi ya samar da qasar da yanzu ake ce mata NIJERIYA, shi ya kafa ta. Ba wai shi ne ya yi qasar ba, ba kuma shi ya samar da  mutanen da suke zaune a qasar ba, a’a, amma shi ne ya shata kan iyaka, wanda yake daidai nan wurin sunan qasa ce guda, sunanta NIJERIYA.


Ya fara ne da wurin da ya kira ‘Colony of Lagos’, sannan ya kama Kudu ya ce mishi ‘Southern Protectorate’, sannan ya kama Arewa ya ce masa ‘Northern Protectorate,’ wato qasashe uku daban-daban. Daga baya ne ya haxa ‘Colony of Lagos’ da ‘Southern Protectorate’ a matsayin qasa xaya, sannan kuma a 1914 ya hada wadannan bangarori biyu (‘Southern Protectorate’ da ‘Northern Protectorate) a matsayin kasa daya. Aka sakawa wannan qasa suna NIJERIYA, wanda yanzu aka bar mana gadonta.


Yanzu mu nan sunanmu wai NIJERIYAWA ne. Kuma qasar mu sunanta NIJERIYA, mu kuma sunanmu me? Wai Nijeriyawa. Kuma abin da yake gabanmu shi ne; mu ciyar da qasar mu gaba. 


Wato kenan mu yi gine-gine, mu yi dogaye daban-daban, mu yi titunan motoci, ga su nan dai, a samu  garuruwa ana ta karakaina, ana ta harkoki, a yi ta rayuwa! Ko dayake za a yi ta mutuwa ma, tunda ana rayuwar ana mutuwa, shi kenan!

 

Sai ya zama Nijeriya din nan ta zama tsarar wadansu qasashe fitattu a duniya, kila kamar irin su; Misra da Libya da Moroko da Aljeriya, kila ma idan aka yi hobbasa ma a goga kafada da Malesiya da Indonisiya, kila ma a ce ke Singafo ke ma sai mun kamo ki, kila ma a kama Indiya. 


Wato a ci gaba sosai! Kila ma ana nan ana nan sai a ci gaba sosai a shiga ajin qasashen nan da suka ci gaba. Domin yanzu qasashen duniya an raba su gida uku ne; da cigababbu, da masu ci gaba, da 

cibayayyu.


To, Nijeriya tana cikin jimlar cibayayyu. Saboda haka yanzu zata zo ta shigo cikin ajin masu ci gaba, wata rana ma sai ta ci gaba. Ta zama qasa wacce take mai manya-manyan masana’antu, wacce take qere-qere na motoci, da jiragen sama, da jiragen qasa da sauran su. Ta yi kafada da sauran qasashen duniya cigababbu irin su; Italiya da Birtaniya da Faransa da Jamus da sauransu.


- Daga Littafin Mulkin Mallakar Tuwara, wallafar Cibiyar Wallafa.


Kuna iya sauke littafin anan


https://drive.google.com/file/d/16bgt2rRJpOsBydN4RrI-PBKbjtitOIGY/view?usp=drivesdk

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post