MANYAN DARUSSA DAGA RAYUWAR SHAHID AHMAD ZAKZAKY (H)

 

Shahid Ahmad Ibrahim Zakzaky {H}


Shahid Ahmad Zakzaky yake cewa d ace ya taso yaga Harka daidai ya kamata ta kasance, wato yadda su Abba (H) suke so yan' uwa su kasance da bazai fara aikin da yau muke ganin shi ya assasa ba. Da wani abu daban zai dauka kuma. Saboda tunaninsa mai fadi ne kullum ayyukan da yake so yayiwa Harkar nan karuwa suke a tunaninsa. Wannan yasa na tuna da wata ka'idar malaman irfani da suke bada misalin cewa idan kana so ka zama injiniyan komfuta to kana bukatar kaje ka karanci ilimin komfuta. Haka nan idan kana so ka zama injiniya na gini to kana bukatar kaje ka karanta ilimin injiniyan gini. 


Saddu ne ga addini yin abun da kasan kai ba ahlin abun bane kazo ka babbake kace dole sai kaine zakai. Sanin ya kamata shine a nemi wanda yake da ilimin wannan abun yayi abun. Kamar yadda dakta na ilimi bazai je asibiti da sunan zai bada magani ba haka shima malamin addini bai kamata yasa baki akan abun da bashi da ilimi akansa ba. Saide kuma in Allah yasa yana da sani wasu bangarorin ba iya ilimin addini ba. 


Cikin maganganun Shahid Ahmad Zakzaky yake cewa sau tari idan muka fara wani abu na addini sai munyi nisa sai kaga abun bai kai ga natija ba. Wannan na faruwa ne saboda wanda suka fara aikin basu ya kamata suyi aikin ba, kuma sunyi kame- kame sunce su zasuyi. Har yake cewa duk wanda ya samu kansa a haka to ko yayi aikin da iklasi Allah bazai karba daga gareshi ba, tunda bai hakkakar da natijar da ake soba. Wanda kuma kila da yabar wanda ya san abun shi kuma zai hakkakar da natijar da ake bukata. 


Hatta a al'amarin addini dole ne ya zama kowane aiki ana dora ahlin abun ne akansa domin samar da natija, saboda kar tafiya tayi nisa a gaza kaiwa ga natija daga baya azo ana cewa ai munyi iya yinmu bamu iya ba. Sai Shahid Ahmad yake cewa a bisa gaskiya dai kunyi iya son zuciyarku zamuce. Tunda kun hana wanda ya kamata suyi har akai ga natija. 


Wanann yasa duk wata hanya ta neman ilimi da Shahid Ahmad ya doru akanta zaka ga yanayi ne domin samun wani ilimin da zai taimaki addini dashi. Hatta karatun da yake a China duk saboda amfanuwar addini da kuma kokarin samun kayan aiki yin aiki, saboda da zarar ya fahimci abu kaza bazai yiwu ba sai ina da ilimin kaza zai dukufa wajen sanin wannan ilimin kafin ya fara aikin. 


Toh, a yayin kuma da kake Kokarin cimma wani abu a tafiyar addini misali kai dan uwa ne, kanaso ka kawo canji a cikin yan' uwa su gane muhimmancin ilimi da aiki dashi. 


A irin wannan yanayi hadafinka ya zama guda biyu ne ; na farko shine kokarin cimma wannan buri na gyara ilimin yan' uwa. Na biyu kuma kokarin neman yardar Allah. 


To Idan mukai la'akari da ayyukan da Shahid Ahmad ya faro zamu ga a zahiri ai bai samu ya cimma hadafinsa na farko ba. Wanda shine kokarin kawo wasu gyararraki da dama cikin yan' uwa. (Wanda kuma shima zamu iya cewa kaso 60% cikin dari ya cimma shi). 


Amma kuma ya cimma babban hadafi shine samun yardar Allah. Yardar Allah kuwa itace ka koma gareshi kana a matsayin shahidi. 


Dan haka a yayin da muke aikin addini dole ne yazama wadannan hadufa guda biyu sune a gabanmu. Na daya kokarin cimma abun da mukeso na kawo gyara, da yin aiki da iklasi, na biyu kuma shine kokarin samun yardar Allah. Idan tafiya tayi tafiya, muna iya sadaukar da hadafin farko domin samun hadafi na biyu wato yardar Allah. Ko kuma mu zama yadda Ahmad ya zama, a kokarinsa na tabbatar da hadafin farko sai kuma ya siffantu da ayyuka na mai Kwadayin hadafi na biyu wato yardar Allah. 


Sai kuma ya dace da ita. 


Allah yasa anfahimceni. Allah ya karbi shahadar Shahidan mu ya riskar damu tare dasu ya baiwa dangi da iyalai hakurin rashin su Elahee. 

Bissalam



DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/


DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com





Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post