Kayi Reasoning kafin Feeling, Thinking kafin Sensation, idan ba haka to a shirya ganin Hauragiya, Hargitsi da Haukataku



 KUKAN KURCIYA.... 

-- Shamsudeen Hassan Zuru.

Tabbas ba wani Mujaddadi a cikin Al-Umma face ya fi su yin amfani da hankali da Nizami. Ya fi su gudun Adifa(Bin zuciya ido rufe) da miyagun Al-Adu. 


Ta haka ne kawai zai iya canza su, ya azasu bisa tafarki madaidaici, domin su yi aiki mai kyau, su samu sakamako kyakkyawa. Wannan yana yiwune, idan ya samu Mataimaka kwararri, Gagaggu, Nagartattu, masu bin Sawun da taka, da mabiya masu Hankali, masu Natsuwa, masu kaunar Juna, masu Adalci a kowanne Yanayi. Wadannan su ne Madubinshi, da sauran Al-umma za ta kalla, ta kwafa, ta yi koyi. 


Game da amfanin Tunani wajen gyaran aiki  da Inganta halayyar mutane, Sayyid Al-zakzaky ya na cewa:


Ita fikira ita ke tafiyar da rayuwar mutum, zantukan mutum da ayyukan gangar jikinsa, sakamako ne na irin tunaninsa. Zuciya ke sawwalawa mutum abu, sannan ya aikata, wato kenan idan aka samu fikira gurbatacciya, to za’a samu gurbataccen aiki, don haka in ana son kyakkyawan aiki, to dole a gina kyakkyawar fikira, don ita ce asasin kyakkyawan aiki.”  


A wani wurin kuwa Ya ci gaba da cewa: 


Kafin ka canzawa mutum aikinsa, sai ka canza mashi tunanin da ya gina aikin a kai, in har baka goge tunanin ba, to da wuyan gaske ka goge aikin.


Aiki da Zuciya, wadda itace Matattara So da Ki, ya fi komai sauki da Dadi. Domin a nan ne ake samun Sakamako amma na Gajeren zango. Yanzu za ka Biya bukatarka, yanzu za ka huce Fushi, yanzu za ka Rama. Idan Zuciya ce kadai Ma'auninka. 


Sai da bayan jin dadi na Gajeren Lokaci, to akwai biyan bashi na dogon zango. Manufa tana iya rushewa ko ta tabu, Hankali yana iya bacewa, Nizami yana iya tarwatsewa. Dadi zai koma Daci, Ramuwa ta koma Nadama. 


Tsakanin  Muhallin Kwakwalwa wadda itace Cibiyar Tunani, dana Zuciya wadda itace Matattara Soyayyah da Kiyayya,  nisansu bai wuce Taki daya ba, a cikin Jikin Mutum, idan an kalla a Zahiri. 


Amma a wajen mafi yawan mutane,  nisansu ya fi na Milamilai Biliyon. Sai ya zamo hadasu a waje daya -domin su yi aiki, aikinda shi kadai ne tsira ga Bashariyyah- ya fi komai Wuya, har yana so ya zama kamar ba abune Mai yiwuwa ba. A kullum Zuciya itace Al-kalin Mutane, Al-hali Al-Kalancin ba nata Bane ita kadai.  Na hankali ne, ita ko Mai kawo kara. Idan Mai kawo kara ya koma Al-kali to a kullum shine  Mai Nasara. 


Da Haka Adalci ke fakuwa, hakuri ke karewa, Hankali ke Gushewa, Son Rai ke Mamaya, Son Kai ke Shimfisuwa,  Tausayi ke karewa, Mutunci ke Zubewa. 

Reasoning kafin Feeling, Thinking kafin Sensation, idan ba haka to a shirya ganin Hauragiya, Hargitsi da Haukataku. 



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post