KA FAHIMCI HADAFINKA, KUMA KA SAN ME KAKE YI!

 


Wata magana da Malam (Zakzaky) yake yi, ina yawan nanata ta; cewa kai kasan ina ne zaka, ka san me kake yi. Wannan maganar tana da muhimmanci!


In kai kasan inda zaka toh don wani bai gane inda zaka ba kai kana da matsala? Baka da matsala. Matsalarsa ce, shi ne ya ganka bai gane inda zaka ba. Kai dai ba kasan inda zaka ba? Kasan me kake yi? 


To kullum mushkilarmu ita ce bama sanin me muke yi. Shiyasa wai sai mutum ya samu shakka, ya rikice, ya samu ishtibahi akan wani abu da yake yi, saboda dama bai san me yake yi ba. Wanda yasan hadafin harkar nan ba yanda za'a yi ya bar harka, in dama can ya san me yake yi.


To kai dama ka ɗauko abunda baka san inda zaka bane? Kai mahaukaci ne kenan! Abunda mutane keyi kenan! 


Ya kamata kafin ka ɗaura ƙafarka akan wani abu a matsayinka na mai hankali, mai ilimi, ka san meye (wannan abun), ko a mene ne.


Misali sai kaga wani yana zuwa makaranta, sai kawai ka gamu da wani sai yace maka ka daina zuwa makaranta. To dama kana zuwa makaranta baka san me kake yi ba kenan? Baka san ina zaka ba! Kaga ka samu matsala. Kwata-kwata bai kamata ɗan Adam ya zama haka ba. Ɗan adam ba tinkiya bace!


Wata rana sun kama Malam (Zakzaky), sai yake ce musu ina ne zaku je dani? (Sai suka ce karka damu). Sai yace: A'a! Ni akuya ce? Ko ni buhun dawa ne da zaku kama ni ku tafi dani ban san inda zaku ba? Kaga wanda yasan kansa kenan. Haka ya kamata ɗan Adam ya zama. 


Kafin ka ɗaura ƙafarka a wani wuri kasan meye (wannan), ta yanda in har ka ɗaura, ruwa da iska da rintsi baza su saka ka faɗi ba (ka bar hadafi). Kuma duk waɗanda suka ci nasara a rayuwa haka suka zama. Suna sanin hadafinsu ne.


In kasan inda zaka, wallahi haushin mai haushi ba zai saka ka sauya ba.


- Mal. Luqman Alfa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post