Rararraban kai da sabani a tsakanin al’ummah. Domin kuwa duk al’ummar da yada jita-jita,karairayi ya yi yawa to da wuya a samu hadin kai a tsakaninsu. Sobada haka yana da muhimmanci idan mu ka ji magana ko a ka bamu labari to mu yi bincike.

Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

ILLOLIN YADA JITA-JITA DA MAGANGANU MARASA TUSHE A CIKIN AL’UMMAH.


Assalamu Alaikum warahmatullah Wa barakatuhu.


Bismillahi Rahmanir-Raheem


Allah Mabuwayi da Daukaka wanda bisa baiwa da hikimarSa ya yi halitta kuma ya tsara yadda za su tafiyar da rayuwansu, ta tafi daidai ba tare da wani matsala ba. Kuma idan suka saba, suka ki bin wannan tsarin to sai su fada cikin rayuwan kunci tun a nan duniya sannan Ranar Lahira su kasance cikin masu hasara. Allah ma daukakin Sarki yana cewa a cikin al-qur’ani mai girma (( وَأَن لَّوِ اسْتَقَامُوا عَلَى الطَّرِيقَةِ لَأَسْقَيْنَاهُم مَّاءً غَدَقً6 “Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa.” ( لِّنَفْتِنَهُمْ فِيهِ ۚ وَمَن يُعْرِضْ عَن ذِكْرِ رَبِّهِ يَسْلُكْهُ عَذَابًا صَعدا “Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa.” A cikin wadannan ayoyi za mu iya fahimtar cewa idan Dan Adam ya tsayu a kan hanyar da Allah (T) ya dora shi, Allah zai shayar da shi arzaqi mai yawa, kuma zai yi rayuwa kyakyawa idan kuma ya saba zai yi rayuwa na kaskanci da wahala duniya da lahira.


Daga cikin hikima da baiwa irin ta Allah Mabuwayi da Daukaka akwai;halittar namiji da mace kuma ya yi su kabilu daban-daban,kuma ya yi wasu mawadata wasu kuma mabukata. Kuma ya sanya mutane suka kasance kasashe daban-daban da kuma garuruwa, kuma ya tsara cudanya da zamantakewa da mu’amala a tsakaninsu. Dan haka sai ya san ya masu tsari (dokoki) yadda za su yi mu’amala da juna ba tare da wani ya danne hakkin wani ba. Kuma ya haramta Cuta (Zalunci) a tsakaninsu. Dan haka ne ma idan muna karatun Al-qur’ani mai girma za mu ga ayoyi da dama su magana a kan yadda za mu kyautata zamantakewa a tsakaninmu ya kuma yi bayanin a kan hakkokin kowa, da yadda za mu yi mu’amala da junanmu. A lokaci guda kuma ya nusashemu babuwan da ka iya haddasa rikici da sabanin har ma da yake-yake a tsakanin al’ummah.


Wannan shi yasa za mu ga addinin Musulunci ya hana (haramta) yada jita-jita, karairayi da maganganu marasa tushe. Kuma a lokaci guda ya umurce mu da cewa idan a ka Kawo mana labari mu yi bincike mai zurfi domin tantancewa, shin labarin gaskiya ne ko ko karya ne. Domin kamar yadda Malaman Mandik suke cewa ne ” ita labari tana iya zama gaskiya kuma ta iya zama karya”. Bincike ne kadai zai iya sa a tantance. Dan haka idan aka baka labari, ko a ka gaya maka wata magana da ya shafi wani ko wasu to ka yi bincike don kauce wa cutar da mutane bisa rashin sani. Ga abin Allah madaukakin Sarki yace dangane da wannan: ( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِن جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَن تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ ( Al-Hujuraat 6) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma. Idan muka yi nazari da ta’ammuli na wannan ayar za mu fahimci cewa ta na magana ne a kan abu mai gayan muhimmanci na zamantakewar al’ummah kuma abin da yake da tasiri sosai wurin dukule al’ummar wuri guda da kuma hadinkanta. Domin ita al’ummah ta na samu labaruruka daban-daban kuma suna musaya tare da yadawa wadannan labarurukan a tsakaninsu kuma yana da tasiri sosai a zamantakewarsu. Kasancewar dole a samu musayan bayanai (communications) a tsakaninsu. To a wannan ayar da muka ambata a baya, sai ya yi magana da Muminai cewa idan fasiki (wanda ya fita daga biyyayar Allah kuma yana saba masa) ya zo ma ku da babban labari to ku yi bincike shin labarin gaskiya ko karya ne kada ku yi gaggawa aiki da ita. Domin kada ku cuci mutane a cikin jahilci. Malaman tafsiri sun ce wannan ayar ta sauka ne a kan Walid dan Ukuba dan Mu’id a lokacin da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S) ya aike shi ya je wurin Banul- Mustalik ya karbo zakkah, da suka samu labarin Dan Sakon Manzon Allah (S) sai suka fito tarbansa domin farincikin zuwansa. Kuma daman a jahilaya a kwai gaba a tsakaninsu saboda haka ko da ya hango su, sai ya yi zaton suna yunkurin kashe shi ne, sai ya koma wurin Annabi (S) yace masa ai sun hana shi zakkah, amma al’amarin ba kamar yadda ya fada bane! Wannan ya sa Manzon (S) ya so ya yake su. ( Majma’ul bayan j.9 S.122). Wanda hakan ta sa Allah (T) ya saukar da wannan ayar da muka Kawo.


Idan muka lura sosai za mu ga cewa yada jita-jita, karairayi da maganganu marasa tushe suna haddasa illoli a zamantakewarmu kamar haka:


1- Rararraban kai da sabani a tsakanin al’ummah. Domin kuwa duk al’ummar da yada jita-jita,karairayi ya yi yawa to da wuya a samu hadin kai a tsakaninsu. Sobada haka yana da muhimmanci idan mu ka ji magana ko a ka bamu labari to mu yi bincike.


2- Yana haddasa kisan kai ba bisa hakki ba. Domin sau tari, idan a ka fada ma wasu managa a kan wani sai su hau (dauka) ba tare da bincike ba, wannan ka iya kai su da kisan kai ba bisa hakki ba. Alalmisali: Wani ya ta ba bada labari a kafafen yada labarai a kan wani abun da faru da shi. Yace wata rana ya taba daukan police cikin farin kaya, da nufin ya rage masa hanya zuwa police station din su. Suna cikin tafiya sai suna hira sai dan sandan ya ke ba shi shawara da ya yi takardun mashin din sa, sai yace masa au kaga kuwa banyi ba. Da dan sandan ya ji haka sai kama shi. To shi da ya ga haka sai ya yi masa ihu cewa ya zagi Manzon Allah (S) ai kau sai a ka yi ca a kan wannan dan sandan da kyar ya sha. Shi kuma ya samu ya gudu. To ka ga Wannan yana da muhimmanci idan mun ji magana/labari mu yi bincike.


3- Yada jita-jita na iya haddasa yake-yake: Misali idan mun yi nazari dalilin saukar ayar da muka ambata to za mu ga cewa da ba’ayi bincike ba,da an yaki wadannan mutane (Banu Mustaliq).


4- Yada jita-jita na san ya mutane cikin nadama (Danasani). Duk mutumin da ke dauka jita-jita to zai yawaita yin Nadama. Kuma zai rika hasara abokan arzaqin da masoya.


Dan haka yana da muhimmanci mu guji yada jita-jita da karairayi a tsakanin mu.domin duk abin da mutum ya fada ko ya aikata to lallai mala’iku na rubutawa kuma zai tsaya gaban Allah gobe kiyama a yi masa hisabi. Wasallallu Ala sayyidina Muhammad wa alihi attayyibinal-tahireen. Daga Dan uwanku Baban Bakir Ushiba. 28/07/2017.



DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 





Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post