Daren Juma'a


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Slm, yan uwa masu daraja yau Alhamis, deren da ke gaban mu zai zama deren Juma'a kenan.

Daga cikin ayyukan wannan dere ana son yawaita fadin; "Subhanallah wallahu akbar wa la ilaha illallah allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad". Sannan ana son yawaita salati wa Manzon Allah (S), yazo daga Imam Sadiq (a.s) cewa yin salati wa Manzon Allah (S) a deren Juma'a zai samar da lada dubu, goge munanan aiki dubu, daukaka daraja dubu.

Sai kuma mashahuriyar addu'ar nan Dua Kumayl, wanda Sayyid Zakzaky (H) yace tana kankare tsakanin karantata da karantata. Sai wadannan surorin da ake son karanta su a wannan dere; Al Isra'i, Al Kahfi, sai surori masu طس guda uku a jeren nan (Shu'ara, Namli da Qasas), Sajdah, Yasin, Saad, Ahqaf, Waaqi'a, Fussilat, Dhukhan, Tur, Qamar da Juma'ah.

A wani ruwayan akace idan bazai yiwu mutum ya karanta wadannan surorin duka ba, sai ya karanta daga Waaqi'a zuwa qarshen Qur'ani. Ayyukan deren Juma'a suna da yawa, wannan a taqaice ne. Ana iya nazartan Mafatihu don cikakken bayani.

Allah (T) ya kar6i addu'o'in mu, ya qara wa Maulana (H) lafiya da kariya, ya kai dauki ga'yan uwan mu na Palestine da Iran da ma duk inda musulmi suke a fadin duniya.
Ku sanya faqiri a addu'o'in ku masu albarkoki.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post