Dandalin Siyasan Harkar Musulunci A Najeriya .

 




Tun lokacin da akayi shelan tabbacin kafa 

Dandalin Siyasa na Harkar Musulunci a Najeriya karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky, dandalin ya jure kwaramniyoyi da nazarce nazarcen da ake iya ji a gani Kai tsaye da  kananan da ba'a iyaji ko a gani kaitsaye sai ta wasu hanyoyi din daga wurare daban daban.

Tun lokacin samuwan shi,  dandalin siyasan ya fuskanci tambayoyi masu yawa ciki harda tambayin halascin shi dandalin dakuma manufa.

Dandalin Siyasan tare da masu masuliyya a dandalin sun fuskanci wasu irin tambayoyin da bisa hakikani , masu tambayoyin, da sun dukufa ne wurin aikama zababbun dake rike da madafun iko a wannan kasar ta Najeriya.

Wannan kasar ta tarayyan Najeriya wanda ta dauki matakin dankwafar da muradu da manufofin Harkar Musulunci ,tayi watsi da 'yancin ma'abota Harkar ,sannan ta kakaba mata wani suna har ya kaiga ; ita wannan kasan ta Najeriya ta karkare shirinta da kawwana wani tsarin kare-dangi na share Harkadin daga doron kasa.

Bayan taron Dandalin Siyasa din da akayi a Sakwato na tsawon kwanaki 3 , daga 11 ga wata zuwa 13 ga watan Nuwanba , 2022; sa'annan Kuma kasantuwan yawan batutuwan da mahalarta taron suka bijiro dasu a lokacin, muka ga  dacewan Kara maimaitawa , da tabbatarwa tare da fayyace hadafin shi wannan dandali na siyasa din na Harkar Musulunci a Najeriya.

A watan Disemba na 2015 Sojojin Najeriya suka dukufa wurin aiwatar da kissa shiryeyyen mugun nufi na kisan kare-dangi ga Musulmi mabiya koyarwan makarantan Ahlul Baitin Annabi Shia a Zaria , Jahar Kaduna , Najeriya.

Tunda munsan cewa Sojojin Najeriya ba zaman kansu suke ba, bisa doka suma suna karkashin dokoki ne na Najeriya , dukkanin dawainiyoyin kisan gillan da sukayi ya ratayane a wiyan Gwamnati.

Dandalin Siyasa na Harkar Musulunci a Najeriya zai dukufa wurin aiwatar da wadannan:

. Kare hakkokinmu na  rayuwa a matsayinmu na mutane , dukiyoyinmu da Kuma mutuncinmu.

.  Kokari wurin bunkasa zaman lafiya da kyawawan mu'amala na rayuwa a tsakanin mutane .

. Tabbatar da dai daito wurin rabon arzikin kasa.

. Tsae rayuka da dukiyoyin jimillan 'alummanmu a muhallensu.

. Wanzarda mu'amala na zumuncin diplomasiyya da Kuma kokari na yunkurin tabbatar da adalci ga jimillan alummanmu.

. Wayar da kan alummanmu wurin sanin 'yancinsu dakuma abubuwan da suka rataya a wuyayensu a irin wannan salon mulkin da kasannan da doru akai

. Tabbatar da 'yancinmu nacewa muke da iko da hakkin fadin abunda ya shafemu da abunda  muke da bukata, imma zai shafemu ne Kai tsaye ko ta wasu hanyoyin da ba Kai tsaye ba.

Zamanmu na karshe da mukayi a Sakwato anyi shi ne domin a bada daman wayar da kai akan abunuwan da ake so a cimma dakuma hadafofin dandalin ga kowa;musamman yanuwanmu maza da mata wadanda suka dandani musiba na  ta'addancin kare-dangi.

Alummanmu na Harkar musulunci sun dandani gayan wariya ,danniya, tursasawa da cin zarafi da ake ma mutane daga mahukuntan Najeriya. Alumma Musulmi mabiya makarantar Ahalin Annabi Shia wadanda bisa doka, ya kamata ne a basu kariya.

A wurin tattaunawa na Sakwato din mun fayyace manufofinmu. Lokaci bayyiba kuma ba zai anfanar damu ba a wannan lahza din da mu fito karara mu nuna zamu marawa wani baya imma  jam'iyya ce ko imma wani dan takara.

Muyi taka tsantsan da sanya ido wurin masu sana'ar dakon yada  farfaganda domin kokarin biyan wasu bukatunsu ta hanyar dabarun juya kyawawan hadafofin Dandalin Siyasan izuwa munana.

Domin tabbatarwa ; babu wani dan takara ko wata jam'iyya izuwa yanzu da suka shirya domin daukan alkawarin aiwatar da bukatunmu na neman ayi mana adalci . Saboda hakanan  Dandalin Siyasa na Harkar Musulunci na rike  da damarsa wanda hakkin dandalinne na dakatarwa da daukan wani mataki akan hakan a wanna lokacin.

A karshe, mu yan Dandalin Siyasa mun nesanta kawukanmu daga masu yawo da sunanmu suna kirkiran zantuttuka marasa tushe , suna dangantashi izuwa ga Jagora suna nuni da cewa ya aikosu su wa'azantar da abunda munsan ya sabama koyarwan shi, Kuma bugu da kari ba zai cigabantar da hadafofin Dandalin Siyasan Harkar Musulunci ba.

Mohammed Ibraheem Zakzaky 

Fassarar Shuaibu Isa Ahmad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post