DAGA BAKIN SAYYIDA SUHAILA IBRAHIM ZAKZAKY

 



"......... Bayan wani lokaci sai muka fara jin kauri, don na tuna na ji muryar Amma Shema’u da ke aiki a cikin gidanmu, na ji muryarta, daga baya muka ji ashe tana cikin zauren, kuma lokacin Sojojin sun sa wuta. Mun ji kauri amma ba mu san meye ba. Muna nan sai muka ga hayaki yana shigowa ta bayin Abba. Abubuwan kuma suna ta narkewa. Sai muka fahimci wuta ce ta iso wajen. Sai Abba ya ce mu fita da mu kone gwara mu fita su harbe mu, domin ba za mu tsaya a ciki mu kone ba. Mun yi kokarin fita ta waje, sai muka ga wurare suna cin wuta. Mun yi kokarin fita ta wata kofa, sai kofar ta ki budewa, sai muka zagaya ta can baya.

"Lokacin da muka bude sai muka ga wasu ’yan’uwa a tsaye a wajen, da wani yana da harbi a kafa, akwai kuma Shahidai biyu; Awwal Darazo, ina tsammanin da kuma Abbas Abdullahi Abbas. Da muka bude kofa, da muka fahimci ’yan’uwa ne, sai Abba ya ce su shigo ciki. Da yake Azahar ta yi a lokacin, kuma Abba da alwalarsa sai ya ta da Sallar Azahar. A cikin ‘Brothers’ din akwai wanda yake ce wa Abba ya yafe masu, domin sun yi iyakar kokarinsu, har Umma ta ce ba damuwa su yi shiru kawai, su bar maganar tunda Abba ya ta da Sallah.

A cikin ’yan’uwa akwai wanda yake cewa ko za a fita ne a bi ta ina, a bi ta ina? Sai Abba ya ce a dakata tukunna. Sai ya kabbara la’asar. Na tuna a lokacin har Umma tana cewa su dakata, ai muna tare da Abba ne, duk abin da ya ce ‘next’ shi za mu yi. Ba dole ne ya zama wata dabara ba ce, duk abin da ya ce mu yi, shi za mu yi. A wannan lokacin muna cikin falon Umma ne, da hayaki ya fara shigowa, sai Abba ya ce mu fito, katangar da in za a shiga cikin gida duk ta riga ta fadi dama ta nan suka shigo. Sai muka koma ta bangaren Mama (Mahaifiyar Abba ke nan). Bangaren nata ba wani abu da ya same shi, sun shiga, ko ba su shiga ba, ban sani ba. Kila sun shiga sun ga ba kowa sun fita. Sai muka zauna a nan. Mun dan jima a wajen.

Tun wajen karfe 1:00nr har zuwa kusan 4:00ny. Muna wajen ana ta neman ruwa, an samu kadan, wasu sun samu sun yi alwala sun yi Sallah, wasu kuma ba su samu ba. Lokacin wannan zaman da muka yi an yi ta bugo min waya. Duk da yake tun muna dakin Abba ’yan BBC sun bugo, sun kira wayar Abba sai na dauka. A lokacin kuma Sojojin suna ta shelar in Abba yana cikin gidan ya fito. Sai ’yan BBC din suna tambayar ina Malam? Sai na ce masu ban gan shi ba. Na yi haka ne saboda na san suna neman su san ina Abba yake ne. Suna so su tabbatar sun same shi, ko ba su same shi ba. Mutane da yawa sun bugo, amma a wannan hali da yanayin da ake ciki, ba za ka iya tabbatar waye ya yi tambaya don ‘concern’ (tausayawa) ba, waye kuma yake nufin yin wani abu. Sai ya zama ni kadai na rika magana da mutane, ina ce masu ban san inda Abba yake ba.

Muna dakin Mama din, akwai wani da ya rika bugo waya wai daga ofishin Shugaban kasa, wai suna so su zo su fitar da Malam lafiya lau. Bayan mun bar dakin Mama, saboda hayaki ya fara shigowa wajen, sai muka fito tsakar gida, sai Abba ya ce mu kwanta, saboda hayaki ya yi yawa, in kuma ka kwanta a kasa zai zama ba hayakin. Da farko wutar ta dan lafa har ta mutu saboda tankin ruwa ya fashe, sai ya zama sun kara hasa wutar ta kara yawa ta ci gaba da ci. Muna barin nan wajen sai muka shiga dakin wanki, domin a lokacin sun riga sun sa wuta a bangaren yara da bangaren kicin din da ke waje da su gareji da sauran wurare. Sai ya zama wuraren ba kowa saboda wuta na ci. Sai muka zo muka wuce muka shiga dakin wanki saboda akwai dakin a dakin.

Muna cikin wannan dakin wankin suna ta kira, wai wannan da aka turo daga ofishin Shugaban kasa ya zo ya fitar da mu daga wajen, ya tambaye ni da waye, na ce masa ni da Sisters dina kwara biyu. Wajen karfe 5:00ny ya kira ni ya ce wai ga su nan sun iso kofar gida in fito. Sai na ce masa ai ba ma gida yanzu, bai ga gidan ya kone ba? Ai ba ma cikin gidan. Mun koma gidan makwabta. Ya yi ta matsawa wadanne makwabta ne, na ce ba zan fada masa ba, saboda in mu sun fitar da mu lafiya, to mamwabtan fa? Domin in har da gaske ne daga fadar Shugaban kasa ne, kamata ya yi a hana Sojoji harbi ne, ko kuma a janyesu. Don sun yi karyar cewa sun dakatar da sojojin.

Da farko da suka kira da safe akwai mutumin da ya yi tambayar cewa dama Sojojin ba su janye ba? Na ce suna nan. Ya ce a’a ku fito zai zama sun janye. Na ce masa lallai suna nan ba su janye ba. Lokacin da muke wayar, na ce masa ba ka ji harbi ba? Ya ce yana ji. Sai ya ce yana zuwa, za su yi wani abu a kai. Amma har zuwa yammacin Lahadin da wayewar garin Litinin sun ci gaba da harbin.
A wannan lokacin muna magana da su Malam Kasimu Sakkwato, kuma sun tabbatar mana da cewa Sojojin suna bin ’yan’uwa da suke wasu gidajen suna harbe su, amma kuma duk da haka suna cewa mu fito". 

— Bangaren hirar Sayyida Suhaila Zakzaky da ALMIZAN a kan harin da sojoji suka kai gidansu a ranar 12/12/2015

#ZariaMassacre
#5yearsfreezakzaky
#5yearszariamassacre

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post