Bayyanar Izala Alama Ce Ta Tashin Alqiyama !!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SUN RIQI MASALLATAI ABIN ADO DA KASUWANCI 


Masallaci guri ne wanda Allah (T) ya umarci bayinSa da yin sallah a cikinsa, kuma Annabi (S. A. W. W) ya kwadaitar wajen rayar dashi da yin ibada ta hanyar haduwa ana sallah a cikinsa. Yin hakan na taimakawa wajen hada kan al'umma da kuma sanin halayyar da mutane ke ciki. 


Allah bai umarci bayinSa da yawaita gine-ginen masallatai ba, haka ma AnnabinSa (S. A. W. W) bai kwadaitar da yin hakan ba. Abinda kawai ya kwadaitar shine a gina shi don samar da gurin haduwar al'ummarsa don yin ibada da kuma tattauna wasu abubuwa don cigaban muslimci da musulmai.


Sabanin wannan sai ya zamana bayyanar Izala ya haifar da rarrabuwar kan al'umma da kuma tsintsinka ta gida-gida . Ba ma cikin al'ummar ba har ma cikinsu (Izalar) masu da'awar aqida iri daya. 


Za ka samu ko ina sun kakkafa masallatai wadanda kowannensu na kallon juna tare da ji daga junansu, alhali babu wata tazara ko lalura ta yin hakan, sai dai don samar da shi a matsayin guri (center) na kasuwanci (business). 


A duk inda aka ji labarin samun wani sabon masallaci sai kaga sunyi katutu wajen mamaye shi don ya dawo qarqashin ikonsu/jagorancinsu.


Yin haka na daga cikin alamomi na tashin alqiyama. 


Ya zo cikin riwayoyi daga littafan Ahlus-Sunnah wanda ke nuna hakan ba cigaban muslimci bane, sai dai wata alama ta kusantowar tashin alqiyama. 


Bari kai-tsaye mu kawo riwayoyin don taqaita rubutun namu. Ga su kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


باب تشييد المساجد: 


788- حدثنا عبد الله بن معاوية الجمحي حدثنا حماد بن سلمة عن أيوب عن أبي قلابة عن أنس بن مالك قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((لا تقوم الساعة حتى يتباهى الناس في المساجد)). 



Ibn Majah ya riwaito cikin  Sahihi nasa cewa, Abdullahi Bn Mu'awiyata Al-Jamhiy ya bamu labari, Hammad Bn Salamata ya bamu labari daga Ayuba daga baban Qilabata, daga Anas Bn Malik yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace :


" QIYAMA BA ZA TA TSAYA BA HAR SAI MUTANE SUN RIQA YIN FAHARI CIKIN MASALLATAI . "


-Sunan Ibn Majah, J:1, Sh:244, Hadisi mai lamba  788.


-Sunan Abu Dawud, J:1, Sh:123.


-Musnad Ahmad, J:3, Sh:134


Idan muka kalli wannan hali da muke ciki za muga babu wasu masu fahari da masallatai kamar 'yan Izala. Shi yasa suke gina shi suke fahari dashi a matsayin cigaba a wajensu, alhali ba cigaba bane sai dai bayyanar wata babbar alama ta tashin alqiyama. 


A wata riwaya kuma yake cewa, 


789- حدثنا جبارة بن المغلس حدثنا عبد الكريم بن عبد الرحمن البجلي عن ليث عن عكرمة عن ابن عباس قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((أراكم ستشرفون مساجدكم بعدي كما شرفت اليهود كنائسها وكما شرفت النصارى بيعها)). 


Jabbarata Bn Maghlasi ya bamu labari, Abdul-Kareem Bn Abdurrahman  Al-Jabaliyyu ya bamu labari daga Laithi, daga Ikramata, daga Ibn Abbas (R. A) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce :


" INA GANINKU DA SANNU ZA KU 'DAUKAKA MASALLATANKU A BAYANA KAMAR YADDA YAHUDU SUKA 'DAUKAKA (qawata) GURIN IBADARSU, KUMA KAMAR YADDA NASARA SUKA 'DAUKAKA WAJEN IBADARSU. "


Ibn Majah, Hadisi mai lamba 789


Cikin wannan hadisi ana kawo mana zargi ne kan yadda ake mayar da masallatai a wannan zamani wanda hakan ke sanadin yin fahari na samar dashi. 


Cikin riwayar qarshe da muke son kawowa cikin wannan rubutu namu ita ce wacce Ibn Majah ke cewa, 


790- حدثنا جبارة بن المغلس حدثنا عبد الكريم بن عبد الرحمن عن أبي إسحاق عن عمرو بن ميمون عن عمر بن الخطاب قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((ما ساء عمل قوم قط إلا زخرفوا مساجدهم)).


Jabbarata Bn Maghlasi ya bamu labari, Abdul-Kareem Bn Abdurrahman ya bamu labari daga baban Ishaqa, daga Amruu Bn Maimuna, daga Umar Bn Khaddab yace : Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce :


" AYYUKAN MUTANE BAI TABA BACI BA FACE (ta hanyar) QAWATA MASALLATANSU. "


Ibn Majah, Hadisi mai lamba : 790


Cikin wannan maganganu da aka riwaito su daga wadannan Sahabbai uku :


Anas Bn Malik, 


Ibn Abbas da 


Umar Bn Khaddab 


Suna nuna mana ne illar yadda ake mayar da masallatai a wannan zamani wanda ke sanadin nisantar da juna da kuma bata ayyuka sakamakon yadda ake ake qawata su. 


Lalle akwai abin nazari cikin wadannan riwayoyi in har sun inganta. 


Allah ya kyauta 🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


16th November, 2022/  22nd Rabi'us-Sani, 1444.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post