BABU TABBATUWA CIKIN AIKIN DA BABU YAQINI !!!

 



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


YAQINE SHINE GINSHIQEN ADDINI 


Shi aiki kowanne iri daka sani ba ya yiwuwa idan ya zama babu yaqini cikinsa. Duk wani abinda kaga mutum ya dage a kansa to, haqiqa yana da yaqini ne kan cewa wannan abin shine hanya ta kaiwa ga nasarar abinda yake son samu.


Ba ya yiwuwa mutum ya cimma wani al'amari ba tare da yana da yaqini kan wannan abin ba. Duk wani abinda mutum ya riqa matuqar ba ya da yaqini kansa zai watsar dashi tun bai tafi nesa ba, ko da kuwa wannan abu mai kyau ne ko marar kyau. 


Addini shine abinda yafi dacewa mutum ya yi shi bisa yaqini, domin ta hanyarsa ne ake samun tsira ranar gobe qiyama. Wannan dalili yasa ake son mutum ya fahinci abu da kansa ya sami yaqini ba tare da lalle sai an cusa masa. Shi yasa Allah (T)  yace :


" BABU TILASCI A ADDINI, HAQIQA SHIRIYA TA BAYYANA DAGA 'BATA. "


Sayyid Zakzaky (H) ya ambata da bakinsa cikin wani jawabi nasa yake cewa :


" NA SHEKARA ARBA'EN INA YIN IBADA DA YAQINI KAMAR INA GANIN ZAHIRI. "


Ita wannan da'awa ta Sayyid Zakzaky (H) na buqatar mai binta ya sami yaqini a kanta, hakan zai taimaka maka wajen kaucewa zamewar duga-dugai, domin in babu yaqini zai iya zamewa daga wannan mafarki na gaskiya. 


Imam Ali (A. S) yayi magana ko gargadi gare mu da mu kasance masu yaqini kan abinda muke yi, domin yaqinin shine qashin bayan addini kamar yadda za mu iya gani cikin wannan kalamai nasa (A. S). 



قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):


 " عَلَيْكَ بِلُزُومِ الْيَقِينِ وَتَجَنَّبِ الشَّكَّ فَلَيْسَ لِلْمَرْءِ شَيْ‏ءٌ أَهْلَكَ لِدِينِهِ مِنْ غَلَبَةِ الشَّكِّ عَلَى يَقِينِهِ ."



" NA HORE KA DA LAZIMTAR YAQINI, DA KUMA NISANTAR SHAKKU (cikin abinda kake yi na gaskiya), DOMIN BABU WANI ABU GA MUTUM WANDA KE SAURIN HALAKAR DA ADDININSA FIYE DA  GALABAR DA SHAKKU KE YI AKAN YAQININSA. "


المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم


Idan ya zamana kana yin abu kuma kana shakku a kansa, to, da sannu wannan shakku naka zai yi gabala akan abinda kake yi. Saboda haka ka zama mai qara yaqini kan wannan da'awa ta Sayyid Zakzaky (H), domin ita ce hanyar da za ta kaika ga samun rabauta. 



A wani guri kuma ya yake cewa :


قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):


   " قَوُّوا إِيمَانَكُمْ بِالْيَقِينِ فَإِنَّهُ أَفْضَلُ الدِّينِ ."


" KU QARFAFI IMANINKU DA YAQINI, DOMIN SHI (yaqini) SHINE MAFIFICIN ADDINI  ."


المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم


Addini ba ya yiwuwa dole sai da yaqini. Allah ya datar damu. 


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


          (08137925034)


27th November, 2022/  3rd Jimada-Ulah, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post