Babban Abinda yake Saurin rugurguza rayuwar d'a Namiji Shine Hakkin Iyaye..!


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 


Wannan d'an abin da ka raina kake ganinshi ba komai ba,Shine ya ke tasiri wajen illataka, haka kawai karinqajin rayuwa tama qunci ka rasa dalilin faruwar hakan, ko samunka ya rinqayin baya, ko ya zama baida Albarka, da ka samu sai ya mutu batare da ka amfana dashiba, karasa me ma kayi dashi. 

Yã Dan'uwa, Ka tina lokacin da iyayenka suke zama da yunwa dan tafiyar da yunwarka, Sukan zama da kishi dominsu tafiyar da Kishinka, Sukan zama da damuwa ko su boye damuwarsu don kawai suga wanzuwar farin ciki da murmushi afiskarka. Dukkanin buri da fatansu ya dauru akanka, dare da rana suna gwagwarmayar ganin sun ingantamaka rayuwa maikyau cikin jin dadi da yalwa, Hatta kayan dakin mahaifiyarka tana Sayarwa idan basuda Qarfin Aljihu dik dan ganin kasamu ilimi ingantacce ka ginu da kanka ta yadda al'umma zasu yi alfahri da amfana da kai. 

Amma lokaci daya da kasamu budurwa ka maisheta itace Uwa da Uba gareka, Akullum kana cacar turamata Credit or data a qalla na dari 500, Mahaifiyarka kuma  kona fire water ka gagara bata. 

Qannenka sun tambayeka kace baka dashi, da zaran budurwarka ta tambayeka jikinka har rawa yake koba ka dashi zaka nemo ko bashi ne kace ta turo account number ka Sambada mata dubu 10,000/20,000. Ahakan ma kana lallashinta wai tariqe da haquri.  Mahaifiyarka ko idan ka hadata da 100, ko 200, ko 500. A kayi qoqari 1000. A hakan kana ganin kayi bajinta.

Ka sayawa budurwarka Wayan dubu Hamshin, Amma iyayenka ko Nokia basu dashi.

Ka dinka wa budurwarka Hijabi Kala 3, Amma mahaifiyarka hijabin kanta ya kode/ya tsufa.

Ka sayawa budurwarka Zanin 15,000. Amma qanwarka tana ta binka ka sayamata Zanin 2500 kace baka da kudi. 

A hkn kullum iyayenka suna yimaka fatan Alkhairi. Anya munayi wa kanmu adalci kuwa? 


Ya 'Yan'uwa, Musanifa Kaf duniya babu wanda yafi cancanta mu kyautata musu Sama da iyayenmu, tananne zamu samu Addu'a da Albarka daga garesu, kuma sune ticket dinka nashiga Aljanna idan ka kyautata musu kamusu biyayya sabida Allah, Albarkar bakin iyayenmu yana da tsada ba haka kawaine ake samunshiba, Idan kayi sa'a kasameshi to tabbas ka samu dafa'i acikin rayuwarka duniya da lahira.

Yã 'yan'uwa,Idan muka kyautatawa iyayenmu Arzikinmu zai bunqasa, zamufi samun nustuwa da kwanciyar hankali da albarka acikin rayuwar mu.  Albarkacin Addu'a da Albarkar bakinsu, Sai gaka Allah ya kareka daga sharri Mata da Zamani.

Su maza masu irin wannan dabi'ar idan akayi Sa'a ya samu Mace ta gari, Saita rinqa sassaita tinaninsa tana nunamishi muhimmanci kyautata wa iyaye, koda bayayi zai fara ta dalinta.

Ga wadanda iyayensu suka rasu, Suna iya kyautatawa wasu, ladan Zai riski iyayensu. 
 
ALLAH YASA MUDACE... 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post