Almajiran Sheikh Zakzaky (H) Sun Ziyarci Shugaban Kungiyar Izala na Jahar Katsina.



Da Mu Aka Fara Gwagwarmayar Islam Only Karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) 


-Inji Sheikh Yakubu Musa Hassan Shugaban Izalah Na Jihar Katsina


Ranar Lahadi 20 November,2022 Yan Uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Suka Ziyararci Chairman Na Kungiyar Izalah Na Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan a Gidansa Yan Uwa Sun Fara Gabatar Da Dalilin Zuwansu Wannan Ziyarar Daga Bakin Dan Uwa Ahmad Ibrahim Yantandu Cikin Jawabin Gabatarwar Dan Uwa Ahmad Ibrahim Ya Bayyanama Malam Dalilin Zuwan Ziyarar Kanan Ya Shiga Bayyanama Malam Tarihin Da'awar Malam Zakzaky (H) Tun Farko Da Kuma Dalilin Fara Kiran, Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Fara Da'awa Tabbatar Da Addinin Musulunci a Nigeria Tun Lokacin Daya Fahimci Irin Mulkin Mallakar Da Turawan Yamma Suke Mana Tun Bayan Da Suka Kawar Da Tsarin Musulunci Wanda Shehu Dan Fodio Ya Kafa Shekaru Sama Da Dari, Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Ya Kira Dukkan Al'ummar Musulmi Zuwa Tsarin Allah (T) Qur'ani Mai Girma Da Kawar Da Zalunci Yau Sama Da Shekaru 40 Kenan An Kamashi Ya Kai Sau 10, An Kashe Mashi 'Ya'ya 6 An Kashe Mashi Almajirai Sunfi 1000+ An Rufe a Rami Daya Babu Sallah Balle Likkafani An Kone Dukkan Dukiyar Sa Bayan An Harbe Shi Da Iyalansa Aka Kullesu Shekaru 6 Wannan Bai Sanya Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Canza Daga Da'awarsa Ba Har Yau Dinnan Da Muke Magana Kuma Yace Bai Zai Taba Canzawa Inji Dan Uwa Ahmad Yantandu.


Da Yake Ci Gaba Da Magana Dan Uwa Ibrahim Mansur Alwalady Ya Bayyanama Malam Cewa Mun Zo Ne Domin Dabbaqa Umurnin Allah (T) Na Cewa Mu Hadu a Igiyar Allah Kada Mu Rarraba Ya Jawo Ayar Hadin Kai Tare Da Wasu Hadisai Sannan Ya Bayyana Hadin Kai Matsayin Hanyar Da Musulmi Zasu Bi Domin Kwatar Kansu Daga Hannun Azzalumai, Shima Malam Aminu Kabir Masanawa Ya Karfafa Maganar Zama Irin Wannan Matsayin Abu Mafi Kyau Cikin Musulmi Tare Fahimtar Inda Kowa Yasa Gaba Ba Tare Da Kayar Juna Ba.


Bayan Kammala Jawabin Yan Uwa, Sheikh Yakubu Musa Hassan Ya Yayi Godiya Ga Allah (T) Tare Godiya Ga Yan Uwa Akan Wannan Ziyarar Musanman Yadda Aka Zabe Shi Cikin Wadanda Za a Kaima Ziyara Irin Wannan, Da Yake Mayar Da Jawabin Sa Ga Yan Uwa Sheikh Yakubu Musa Hassan Ya Bayyanama Yan Uwa Asalin Da'awar Izalah Tare Da Munofofinta Shine Kawar Da Dukkan Wani Abu Wanda Allah Da  Manzon Sa Basuyi Umurni Ba Ko Suka Aikata Ba Tare Da Manyan Bayin Allah  Na Gartattu, Malam Yace Dukkan Bidi'a Kowace Iri Ce Haramun Ce Domin Aikata Bidi'a Kamar Cin Gyaran Manzon Allah (S) Cewa Akwai Aikin Da Bai Aikata Ba. Daya Juyo Akan Maganar Da'awar Malam Zakzaky (H) Sheikh Yakubu Musa Hassan Ya Bayyana Cewa Tun Kafin Kuzo Duniya Damu Aka Fara Gwagwarmayar Islam Only Karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Amman Daga Baya Ne Muka Ja Baya Bayan Shigowar Wasu Abubuwa Inji Sheikh. Malam Yakubu Musa Hassan Yace Daga Yanzu Na Bude Kofar Tattaunawa Da Ku Kowane Lokaci Zaku Iya Zuwa Musanman Idan Kunga Munayin Wani Abu Ba Daidai Ba, Haka Muma Insha Allah Idan Muka Hango Wani Abu Zamu Sanar Da Ku Domin Mu Gyara Tafiyar Juna.


Lokacin Ziyarar Yan Uwa Sun Tarar Da Baki Daga Sassa Daban Daban Da Suka Zo Wajen Malam Tare Da Sauran Dalibai Da Kuma Yan Gidansa Da Hadimai, Sheikh Yakubu Musa Ya Gabatar Da Dukkan Mutanen Ga Yan Uwa, Haka Suma Yan Uwa Sun Gabatar Da Kansu Ga Mutanen. Anyi Zumunci Sosan Gaske Cikin Farin Ciki Da Annashawa Aka Gabatar Da Kyauta Ga Malam Akayi Hotunan Tarihi Kana Akayi Bankwana Cikin Shaukin Juna Tare Da Fatan Sake Haduwa Lokaci Na Gaba.


-Yantandu

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post