Tarbiyyar Juna Biyu (Ciki) Da Yaro




Daga Sayyid Nuru Darut-thaƙalaini:


Ya zo daga daga Imamul-Hasan ɗan Aliy (A) a abinda ya naƙalto daga Annabi Muhammad (S):


"Ku ciyar da cikkunanku (Juna biyu) Madara (Ta shanu ko ƙananan dabbobi), domin idan aka ciyar da Jariri madara yana cikin babarsa hankalinsa zai tsananta. (Wasã'ilush-shí'ah). 


*Abubuwan da suka dace ga mai juna biyu:*


Daga Shaikh Muhsin As-shí'í. 


1) Idan Uwa na da Juna biyu to ta kasance a cikin tsarki koda yaushe, ta na fuskantar alƙibila, kuma ta ƙauracewa zantukan banza da maganganu marasa amfani. 

Domin yin Istigfari da komawa ga Allah Maɗaukakin Sarki zai yi tasiri ga tsaftar zuciya da ruhin yaron da ake sauraron zuwansa da Umman tasa.


2) Samun damar karatun Al-ƙur'ãni ko saurarar karatunsa koda ta Kaset ne, idan hakan ya gagara to mafi ƙaranci kallon ayoyin da ido. 


3) Yin iya ƙoƙarin gabatar da ayyukan farillai a farkon lokacinsu, da yin nafilfilu musamman nafilar dare wanda bai dace ta barta ba ko da da ramuwa ne ta yi, kuma da zata bari bata yi ba, to da sai tayi sadaƙa a maimakon barin da bata yi ba. 


4) Dawwama a cikin bayar da sadaƙa kowace rana. 


5) Tarayya a mafi ƙaranci sau ɗaya a sati a wajen Ta'aziyyar da ake yi ta Ahlulbaiti (A), ko kuma yin majalisin ta wannan fuskacin koda da gudunmawar mutane biyu ne. 


6) Dawwama a karanta Ziyarorin Ahlulbaiti (A) waɗanda suke litattafan (Mafãtihul-jinãn) kuma ƙari da sha'awar yin ziyarar Áshúrah kowace rana. 


7) Karanta surar Yãsin koyaushe da rana, da karanta Suratul-wãƙi'ah sau ɗaya, da Ƙulhuwallãhu ƙafa goma mafi ƙaranci kowane dare, da karanta Surartu Ș a daren Juma'a, wannan surar tana da tasiri sosai wajen ƙarfafa Tunani da jawo natsuwar rúhi, wanda wani abu ne da dole ga uwa da jaririn nata. 


8) Yawaita Salati ga Annabi da Alayensa (A) kullum, da bayar da ladan salatin ga Ahlulbaiti (A), kuma hakanan lamarin yake tare da sauran ayyukan Mustahabbi. 


9) Dawwama akan wankan Mustahabbi, musamman ma wankan Juma'a, da daren Juma'ar.


*Wasicin Cin Abinci a yayin da ake da juna biyu:*


1) Bincike da bin diddigi ta fuskacin halasci da tsarkin abincin ko abin Sha wanda uwar zata yi amfani da shi. 

 

2) Shan Madarar Dabbobi kwatankwacin Lita ɗaya kowace rana. Shan Madarar ya zo a Hadisi:


Ya zo daga daga Imamul-Hasan ɗan Aliy (A) a abinda ya naƙalto daga Annabi Muhammad (S):


"Ku ciyar da cikkunanku (Juna biyu) Madara (Ta shanu ko ƙananan dabbobi), domin idan aka ciyar da Jariri madara yana cikin babarsa hankalinsa zai tsananta. (Wasã'ilush-shí'ah).


3) Amfanuwa da alherin da aka ci domin ƙarfafa tunanin yaron da kuma ƙarawa mace mutunci a idon mijinta.


4) Dawwama wajen amfani da kayan marmari ɗanye da yawanta hakan. 


5) Dabino na da matuƙar tasiri wajen ɗaure cikin yaro da kuma ƙara masa ƙarfin motsi da nishaɗi, kuma ba shakka cin wasu ƴaƴan itatuwa ɗanyu zai rage yawan zubar gashi.


6) Don yawan gashin Yaron da kamewarsa da ƙarfinsa, uwar ta ringa amfani da ɗanyar Hulba, musamman ma daga wata na biyar zuwa bayan haihuwar, domin kada Yaron ya ringa Cin abincinsa daga jikin uwar ya janyo mata zubewar gashi ko kuma fitowar Amosani. 


7) Kalar yaron yana da alaƙa ne da lafiyar hantar uwar da nau'in abincin da yake isa ga hantarta, don haka, muna ganin yana da amfani mu yi la’akari da waɗannan abubuwan: Yin amfani da man zaitun, man kifi, gyaɗa, man shanu, kokwamba, salak, karas, lemon tanjirin, citta, da minti - na'ana'a, Musamman wanda yake da ƙafafu.

 

*Abin lura:* yayin shan ruwa ana tsotsa ne a hankali, ba wai kwankwaɗa ba, don kada a haifar da cutuwa ga hanta. 


8) Kaucewa daga tsoro, idan mace taji tsoro to ta sha lemon kankana mai zaƙi, ko lemon ƴaƴan itatuwa masu zaƙi, kuma ta guji yayin tsoron amfani da kayan da aka ajiyesu a cikin abu mai tsami kamar "Vinegar", ko gishiri, da abinda yayi kama da haka, da kayan marmari masu tsami, wanda hakan don yana haifar da bayyanar alamar haihuwar a fatar yaron da aka yi za a haifa.


9) Baƙin buƙatu (Kasancewa da sha'awar wani abinci yayin da aka ɗauki ciki), idan sun kasance masu dacewa, shaida ne na buƙatar jikin mahaifiyar da jaririn ga wannan abu,  to dole ne biyan waɗannan buƙatun domin hana ciwo ga jaririn..... 


10) Dalilin jarrabar jaririn da wata rashin lafiyar ta ƙyasbi shine amfani da kayan yaji yayin da ake da ciki. Ya zama wajibi ga uwa gujewa hakan musamman a watannin ƙarshe, hakanan ma dai ƙauracewa Man wanke baki masu ƙarfin ƙamshi. 


11) Dole ne a adana sinadarin calcium ga jikin jaririn, in ba haka ba zai raunana, kuma ya raunana mahaifiyarsa, don haka za su kasance masu rauni ga ciwon mahaɗai da ciwon ƙashi.


12) Lamurjen Inibi da Tuffa da Ruman masu zaƙi suna da tasiri sosai wajen bada kariya ga lafiyar Jaririn a jikinsa da ruhinsa da hankalinsa. 


*Na biyu tarbiyyarsa bayan yazo duniya:*


Sayyid Ƙa'id (D) ya kawo cewar:


*Tausayawa da Soyayya ga Yara waɗanda suka zo a nassosin addini:*


Musulunci yayi nasiha a ɓangaren tarbiyyar Yara da tausayawa da Soyayya. Kuma ya kasance keɓantaccen waje ne mai muhimmanci bayyananne ta yanayin da yake a sarari a tarihin Ma'asumai (A). Yazo daga Manzon girma (S) a abinda ya keɓanci Soyayya ga Yara da Tausayi garesu, yace (A):


"Kuso Yara kuma ku jiƙansu, idan kuka yi musu alƙawarin wani abin to ku cika musu; domin basu san komai ba sai kune kuke azurtasu". Hakanan Imam Aliy (A) ya ƙarfafa lalurar bayyana jinƙai ga Ƴaya, yayin da yake cewa a cikin Wasiyyarsa (A) yayin Shahadarsa:


"Ku jiƙan Ƙanana daga Ahalinku". 


Harwala iyau an ruwaito daga Imamus-Saadiƙ (A):


"Lallai Annabi Musa (A) ya tambayi Allah maɗaukakin Sarki: Ubangijina!! Wane aikine yafi falala agareka? Ya bashi amsa da: Son Yara, domin Ni na ɗabi'antar da su akan Kaɗaitani. 


Hakanan a wani Hadisin daban da aka ruwaito dai daga gareshi (S) har wala iyau:


"Haƙiƙa Allah Maɗaukakin Sarki zai gafartawa mutum saboda tsantsar sonsa ga ɗansa". 


Hakanan daga tarin yanayan ayyukan da suke taimakawa wajen bayyana jinƙai da tausayi ga Yara sune kamar haka:


Zan kawo a yanyanke ne a taƙaice ba sai na kawo bayanin ba a ƙarƙashin kowanne don akwai tsayi. 


1) Rarrashin Yaron ta shafa masa kai. 


2) Rungumar Yaron. 


3) Sumbatarsa. 


4) Wasa da Yaran. 


5) Daidaito da Adalci. 


*Sharaɗan Soyayya*


Dole ne cika jumla daga sharaɗan soyayyar da ake baiwa Yara, Musamman ma:


1- Ta kasance soyayya ce ta haƙiƙa kuma wacce take fitowa daga zuciya, kada ta zamo ƙirƙirarta aka yi; yayin da shi kansa yaron zai gane irin wannan soyayyar bata gaske ba ce sai dai ba zai iya magana ba. 


2- Ya kamata ya kasance soyayyar ta yanayin da shi Yaron zai ɗanɗana zaƙinta ne, wanda wannan lamarin yayinda iyayen suka bayyana ainahin soyayyarsu gareshi. Kuma a dangane da shi, bai isarwa wanzuwar soyayyar Yaron a zuciya ba tare da bayyanata ba, a'a ya kamata sai Yaron yaga bayyanar soyayyar dangin nasa, kuma ya ji a sarari kyarmarsu a cikinsu na jin son nasu na tausayin nasa. Wanda wannan lamarin a al'ada akwai yiwuwar hanyar taimakon iyalin ga Yaron ta wajen cin abinci, da bibiyarsa, da bada hankali gareshi, da bashi ƙwarin gwiwa, da bayyana burgewarsa da gamsuwa, da yin wasa tare da shi. Da makamanta haka. 


3- Bai kamata bayyana So ga Yaron da ƙirƙirar abu ne mai kyau ba, ko kuma jin a gashin kansa abu ne mai kyau ba, kuma gundarinsa abune mai kyau ba.


Kuma a ɗaya ɓangaren idan soyayyar ta wayar da kan yaron ne da sanin ya kamata, ko don a gida yana wasu ayyuka masu kyau..... To lallai waɗannan ɓangarorin suna ƙara shirya fagen soyayya ne, sai dai kuma ba wai akan cewa waɗannan abubuwan sun zama mallakarsa ba ga soyayyar. 


4- Ya kamata ya kasance soyayyar dangin ga Yaransu ta yi daidai da yayinda suke nan. 


5- Bai kamata ga Uba da Uwa su kewaye soyayyar yaron da tausayi gareshi ga ɗayansu ba kawai, a'a garesu su buɗe hanyar don sauran yaran su sami soyayyar sauran har wala iyau. 


6 - Iyaye mata suyi sonsu ga Ƴaƴayensu Yara ta fuskaci na ɗabi'a sai dai kuma bai kamata hakan ya kai ga yadda zai nuna ko in kula ga babban ɗansu ba. Yayi zaton Ummansa da Abbansa sun manta da shi, hakan zai sanya ya ɗauki sabon Yaron maƙiyinsa ne a ganinsa. 


7 - Gwargwadon son Yara yana danganta ne da matakin shekarunsu ne. 


8 - A bisa al'ada yana kasancewa soyayyar iyaye ga Yaransu a shekarun su ne na farko yafi ginuwa akan shekarunsu na gaban, duk da dai ba zata haifar da wani muhimmanci sosai ba, akwai buƙatar bayyana soyayyar da tausayawar garesu a shekarun balaga da samartaka. 


9 - Bai kamata ga soyayyar iyaye biyu ta kasance ta hana ayyukan umarta da hanawa ba. Ta yadda ba makawa su tausaya ga Ƴaƴansu ta guraren tausayi da soyayya, kuma su umarcesu su hanesu yayin da hakan ya kama. 


A cikin abubuwan da Sayyid Ƙa'id (D) ya kawo sai dai ba zamu kawo bayanai ba akai suma akwai:


10 - Amana da Kurantawa. 


11 - Kwaɗaitarwa da kuma ladabtarwa, sannan mu sani duka baya cikin ladabtarwa. 


*A Shi'a ba a dukan Ɗa idan ba Waliyyinsa ba ko kuma shi yayi izini koda Malaminsa ne kuwa - sune Mahaifi da Uban Mahaifin.*


Kuma ko Waliyyin an iyakance masa kada ya doki Yaron ya wuce duka uku, shima kuma kada ya zamo mai raɗaɗi haka dai yaf-yaf, domin idan ka doki Ɗanka har yayi Ja ko Baƙi ko Shuɗi akwai Diyya wanda mafi ƙarancin diyyar dukan yana kaiwa Naira dubu Casa'in da biyu. 


Akan doki Yaro akan ƙin Sallah, sai dai kafin aje ga muhallin dukan yaro akan sallah, akwai wasu matakai da ake fara zuwa tukunna na tarbiyya sannan a zo kan dukan idan baya sallar, shima dukan akwai kwatankawacinsa, bawai irin jibgar da Mutanen Najeriya ke yiwa Ƴaƴansu ba!


Idan muka duba cikin littafin Sayyid Ƙa'id (H) da yayi magana akan Tarbiyyar yara, ya kawo mataki-mataki, kamar haka:


1) na farko: Koyar da Yara.


2) na biyu: abubuwan da suke faruwa ga ƴan adamtaka da suke da tasiri ga tarbiyya.


3) na uku: Dukan Yaran.


Wanda kowanne a cikin waɗannan yana ƙunshe da tarin ɓangarori wanda yin magana akansu ba zai yiwu ba a wannan tambayar, domin bahasi ne da yake da buƙatar littafi guda.


A ɓangare na farko akan  Koyarwa, Sayyid ya kawo abubuwa da yawa yace:


1- Koyar da rubutu.

2- Koyar da Ƙur'ani.

3- Koyar da Aƙidu na gaskiya.

4- Koyar da hukunce-hukuncen shari'a.

5- Koyar da Sallah.

6- Umartar Yara da Jam'in Sallah (Haɗa azahar da la'asar, da haɗa magariba da isha).

7- Koyar da su waƙoƙin dangin Abu Ɗalib.

8- Koyar da su iya ruwa da Harbi (Yaƙi).


To wannan kenan a ɓangare na farko, wanda kowanne anan akwai bayanai masu yawa akansa, sannan kowanne a sauran biyun ma haka suke ɗauke da bayanai masu yawa da gamsarwa.


Idan muka lura shi Duka ma a ƙarshe yake bayan iyaye sun sauke waɗancen haƙƙunan na Ƴaƴaye da yake kansu.


Sayyid ya kasa Duka kala biyu ne, Dukan da Musulunci bai yarda da shi ba, da Dukan da musulunci ya yarda da shi.


Dukan da musulunci ya yarda da su akwai har da dukan mata da ƴaƴa, amman kowannensu yana da gwargwado, wanda babu daga cikinsu da aka yarda ka doki mutum ka wuce gona da iri, ko ka illata shi, a baya kaɗan mun kawo dukan da ko ɗanka ne ka doka zuwa wannan haddin akwai diyya kuma ɗan da aka doka shi za a baiwa diyyar.


*Dukan Yaro don yayi Sallah*


Sayyid Ƙa'id (H) yana cewa:


Musulunci bai yarda da duka ba a matsayin wata hanya ta farko domin maganin matsalar Yara, sai dai ba makawa Uba da Uwa suyi amfani da hanya sauƙaƙƙa daga dukan kafin su koma ga dogara ga dukan. 


Kuma ita hanyar ma'anar ita ce ta mu ji irin rashin jin daɗi, domin ita Uwa ko Uba waɗanda suke da damar su cika shi Yaron da sha'awa da tausayi, zasu iya gasa a wannan tasirin wannan aɗifar (jin) yayin da suka bayyana wannan damuwar tasu akan yaron.


Sai su ɗan ƙaurace masa domin Yaron ya girgiza daga cikin halinsa a cikin zurfin tunaninsa, ya hana shi daga abin da yake aikatawa. Wanda wannan hanyar ta zo akan harshen Al-Imam Abul-Hasan alaihis-salam yayin da wani ya kai kukan ɗansa, yace alaihis-salam: "Kada ka doke shi ka ƙaurace masa". 


Kuma nusas-shewar Imam (A) da kada a tsawaita a ƙaurace masan kada tsawon lokaci ya jawo ƙeƙashewar Yaron.


Idan wannan bai amfana ba, kuma duk wani gargaɗin baki bai amfanar ba, to anan sai a yi amfani da dukan a matsayin maganin. 


Sai dai amman tare da kiyaye al'amuran da suke tare da Dukan, na dukan ya zamo kyakkyawa.  Kuma yana da wani aiki da zai yi tasiri ga yaron, amman idan babu wani tasirin da zai yi, ba za a yi ba.


Wanda Sayyid Ƙa'id ya kawo sharaɗan dukan da suke da tasiri:


Wanda sharaɗi na farko: dukan ya kasance da ƙudurin ladabtarwa ne, ba da nufin da zai bada tasiri ga yaron ya bashi muhallin da zai ɓata masa halaye ba. 


2- Yaron ya gane wannan dukan da hukuncin an yi masa ne don wannan aikin da yayi ne na kuskure. Wanda hakan sai ya tsoratar da yaron daga laifin da yayi da tsoron Ubangijinsa da yake ganinsa bawai Uwa ko Ubansa ba, wanda tsoro idan ya kasance daga Uba ne ko Uwa ba laifin ba, to lallai Yaron zai maimaita wannan laifin yayin da baya gani, da saɓanin a tarbiyyantar da shi daga tsoron laifin kuma Allah na kallonsa a duk abinda yake yi, kuma zai kasance ne ana bibiyar aikata mummunan aikinsa har tare da iyayen basa nan, kuma ƙari akan hakan shi tsoro daga laifi da jin Allah na bibiyarka yana ganinka to ana kiyayesu abisa siffata ƙoƙari da rashin tsoron wasu, domin Imam Amirul-mumina alaihis-salam yana nuni ga irin wannan tarbiyyar a faɗinsa: "Kada ku yi raja'in wani daga cikinku sai Ubangijinsa, kuma ba a ɓoye komai sai laifi".


To haka dai da sauran abubuwa da Imam Khaamina'iy yayi bayanansu da yawa, wanda lokaci da wuri ba zai bamu damar kawowa ba, zamu tafi ga abu na gaba.


Na'am akwai ruwaya bayyananniya a cikin ruwayar Abdullahi bn Fadhaalata, daga Abu Abdullah ko Abu Ja'far - Alaihimas-salam - a cikin Hadisi yace: na ji shi yana cewa: "Ana barin Yaro har sai ya cika shekaru bakwai, idan ya cika shekaru bakwai sai ace masa: wanke fuskarka da hannayenka, idan ya wankesu sai ace masa: kayi Sallah, sai a barshi sai ya cika shekara tara, idan ya cika sai a koya masa alwala kuma a doke shi akai, kuma a koya masa sallah kuma a doke shi akanta, to idan aka koya masa alwala da sallah Allah zai gafartawa iyayensa in shaa Allah (Uwa da Uba).


Hakanan kuma an ruwaito daga Sayyid Fadhlullah Ar-raawandiy a cikin Nawaadir ɗinsa: da isnadinsa daga Musa bn Ja'far daga iyayensa (A) yace: Manzon Allah (S) yace: "Ku umarci Yaranku da sallah idan sun kasance ƴan shekara bakwai, kuma ku dokesu idan sun kasance ƴan shekaru tara".


Na'am, a baya mun kawo abinda Malamai suka faɗa akan yaya za a yi dukan, zuwa wane haddi ne, kuma idan ka wuce iyaka akwai diyya da cewar Yaron da aka doka za a baiwa diyyar, don haka akwai buƙatar a bibiya domin sanin yadda za a yi dukan kada a wuce gona da iri.


*Dukan mata daga miji, ko Ɗa koda daga Uba ne*


*1) Sayyid Ƙa'id (H) ya kawo yake cewa:*


Kuma mataki na uku:


﴿وَاضْرِبُوهُن﴾:


Ba abin nufi da Duka cutarwa ba, a'a yana da sharaɗai (dukan) na shari'a, ta yadda ba zai zamo mai kaushi ba, wanda ba zai bada shaida ba a jikin yayi shuɗi ko Ja ba gurin dukan, domin ya zo daga Imamul-Baaƙir (A) a wajen bayani akan Dukan: "duka ne da Asuwaki", wanda Asuwakin kuma wani ɗan Ice ne ƙarami wanda ake cuɗa haƙora".


Shima wannan ɗin ana yi ne idan matar taƙi cikawa miji haƙƙunansa na wajibi - a'a ba kawai don ta daina dafa maka abinci ba ka kama dukanta, a'a wannan ba wajibi ne ba akanta -  ta zama tana "shuzuuz" ne.

Kuma shima sai duk kabi hanyoyin masalaha don ta gyara abin yaci tura ne zaka ɗan doketan irin wannan mai sharaɗin.


*2) Sayyid Sistaniy (H) yana cewa:*


Baya halasta dukan mata kuma idan aka dokenta har gurin yayi Ja to akwai zunubi, kuma wajibi ne ga mijin ya biya diyya akan hakan. 


Yace dukan anayi ne bisa sharaɗin idan tayi Shuzuuz ɗin ne, ta hana kanta gaba ɗaya ga mijin, to bayan haka wajibi ne yayi mata wa'azi da nasiha, da duk wata hanya da zai shawo kanta har da ƙaurace mata daga kwanciya, idan hakan bai bayar da wata fa'ida ba ya san idan da zai ɗan doketan dukan zai bayar da fa'ida to ya halasta yayi, idan kuwa yasan dukan ba zai bayar da fa'ida ba bai halasta ba, shima dukan tare da sharaɗan dukan da ɗan Asuwaki, ba tare da ramuwa yake son yi ba, kuma ba tare da duka mai tsanani ba, kuma wanda ba zai nuna Ja ba ko wata shaida, wanda kuma idan ya tsananta har yayi Ja to akwai Diyya akansa da zai bawa matar, kwatankacin alamar da dukan ya nuna.


Diyyar tana saɓawa da kwatankwacin yin Ja ko Yelo ko Baƙi kuma a fuska ne ko a hannu.


Idan yayi Ja Dinare da Rabi ne na daham a fuska, da kuma rabinsa ga jiki, ga kuma idan gurin yayi shuɗi Dinare uku ne a fuska da rabinsa idan a jiki ne, amman kuma yin Baƙin gurin dukan Dinare shida a fuska da rabinsa (uku kenan) idan a jikine abisa Ihtiyaɗi - Sayyid Sistaniy (H). 


Amman tare da shakku a gwargwadon ya halasta taƙaitawa ga abinda ake da yaƙini, sai dai ta kowane yanayi akwai yiwuwar yardar wanda aka dokan, ko neman kuɓuta akan laifin - neman yafiya - daga gare shi yayin da ya balaga idan Yaro ne. 


*Diyyar dukan Mata da Ƴaƴa duk ɗaya ne!*


*Lissafin dinare a ranar Asabar 16/04/2021:*


*Dinare*:


Dinare yayi daidai da ƙimar Gwal (Gold) mai nauyin (4.265 grams) a wajen Sayyid Ƙa'id. Amman a wajen Sayyid Sistaniy daidai yake da (4.64 grams).


Gwal kuwa mai 24carat  $63.47 ne.


Dinare ɗaya = $63.47  x 4.64 = $294.5008


Dinare ɗaya = $295.


Dala ɗaya a farashin Gwamnati tana kaiwa:


N414. 52


Dinare ɗaya 414.52 x 295 =

*N122,283. 40.*


Zamu tsaya anan, don wannan kamar yadda na faɗa ne littafi ya kamata ayi akai don ya gamsar da komai da komai. Allah ya datar da mu kan daidai albarkacin Manzo da Alayensa alaihimus-salam.


Wallaahul-aalim.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post