TAFIYAR HARKAR MUSULUNCI DA TARNAKIN DA KE DAMUNTA

 


Dr. Shamsudeen Hassan Zuru

Harakatul Islamiyyah, ko kuma muce Harkar Musulunci, karkashin Jagorancin Maulana Sayyid Ibraheem Al-Zakzaky (H), mosti ne na kokarin ganin cewa, Addinin Musulunci ke Jagoranci a cikin dukkan bangarorin rayuwar Musulmi, a Addinance, Siyasance, Zamantakewance da cikin Tattalin Arziki, da dai sauransu, domin samun yardar Allah (SWT). 


A wata Ibarar, ita Harka Islamiyyah Idea (Fikira) ce na ganin tabbatar da Addini, ya zama cewa Addinin Musulunci ne madubi a cikkin dukkanin Lamurran Musulmi, domin samun Uzuri wajen Allah a kan kokarin sauke Nauyi na Shimfida dokokin Allah, da bin Tsarin Allah, a doron kasa.  


Da yake tafiyace ta Addini, ba kungiyanci ko bangaranci ko Mazhaba ba. Kokari ne na aikata Musulunci ne gwargwadan Iko, wannan yasa duk wani mai ra’ayi, ko yake ganin cewa makomar Musulmi a duk inda suke, ya wajaba ya zamo Musulunci ne yake da iko da Suldani a kansu, ba waninshi ba, kuma yake kokarin tabbatuwar haka, a bayyane ko a boye, to shi Dan Harka Islamiyyah, ne.  Mai yi a boye, shi Passive Member ne, wanda ya bayyana kuwa, ta hanyar bada Lokaci da Jiki ko Dukiya, to shi Active Member ne. Duk Musulmi nata ne, Haka Duk wani mai Hankali to abokin Tafiyarta ne.


Fadinta da Zurfinta, dai-dai yake da Fadin Musulunci da Zurfinshi. Yadda bashi da Boda ko Iyaka, haka itama Harkar Musulunci.

Wannan ya sa cikin tafiyar Harka Islamiyya, babu kalar musulmin da babu, wadanda suka fito daga Kungiyoyi da Mazhabobi da Dariku kala daban-daban, kuma kowanensu Tunaninshi da mahangar shi game da Addini yana iya, ban-banta da na waninshi, domin mashaya ba guda ba. Mahadar da ta hadasu, ta dauresu waje Daya, itace, Kokarin ganin Al-Qur’ani ya zamo Jagoran Musulmi a wannan Nahiyah. Ta hanyar Dunkulewa karkashin Inuwarshi, Domin yakar Makiyanshi, domin cimma Hadafin hailttar Bayi  a Doron kasa.

Don haka, ba karamin Kuskure bane ga duk wani wanda ya fahimci harka Islamiyya, aca bayada aiki illa ya dinga kokarin ala dole sai ya mayar da ita ta dace da abunda ya sani, abunda ya saba da shi, na fahimta da fikira, a tafiyar kungiyarshi ko Darikarshi ko Mazhabarshi wadda yake a kai, ko kuma wadda ya baro. Al-hali ita harkar tana da tata Fikirar da nata Tunanin. Haduwa a kan Asalin Musulunci, shine Hankoron Harka, ba tada Sabani da rura wutar Gabar Mazhaba ba, wadda ta dade tana Lakume Rayukan Miliyoyin Musulmi. Fahimtar Reshe, wanda Sanadinsa shine, Sabanin Fahimta, da Shishigin Shuwagabannin Danniya a cikin Musulunci, bai kamata ya zamo shingen da zai hana aiki tare a tsakanin Musulmi ba. Balle Dan Gwagwarmayar tabbatar Addini. Balle a yi maganar fahimtar Usulubin isarda sako a matayin tarnakin hadain kai Tsakaninsu. Wannan shine gayar rashin sanin ina aka dosa.


Wannan itace tafiyar harkar Musulunci a Dunkue.


Illa dai kawai, a wasu lokutan, tsawon fakuwar Jagora daga haduwa da mabiya, a lokutan da yake tsare a hannun Azzaluman Mahukunta, shima ya janyo wasu a cikin ‘Yan harka, suyi kokarin ganin sun shata nasu Tunanin, wanda suke ganin shi yafi  dacewa a tafi a kai, wasu bisa kyakkyawar niyyah, wasu kuma domin cimma wata boyayyar manufa tasu. Wannan shima babban Tarnaki ne, mai hana wasu su fahimci Tafiyar.


Haka kuma Uwa-uba, ga ‘Yan leken Asirin hukuma, masu kokarin ganin sai sun dagula tafiyar, sun mayar da ita kungiya, ko Mazhaba, domin su iya datsata gida-gida, ta yadda za ta yi musu saukin wargazawa. Suma suna ta kokarin sai sun canza Tunani da Nizamin Harka Islamiyya, sai sun mayar da harka ta koma Ta’addanci, ko Bangaranci, domin killaceta da mayar da ita saniyar ware, domin ta rasa farin jini da goyon baya a cikin Al-Umma. Tarnaki na Uku kenan.


Haka suma mabiya masu Azarbabi da bin son rai, masu karancin sani game da inda aka fito da inda aka dosa, a kullum so suke sai sun mayar da tafiyar karkashin son ransu da ra’ayinsu, domin ta dace da tunanin su, ba su dace da tunanin ita harkar ba.


 Sanadiyyar haka, sai ga miyagun Akidu da gurbatattun ra’ayoyi na neman yin kutse a cikin tafiyar, wanda hakan ba karamar barazana bace, ga duk wani mai hankali da tunani. 


Ita harka Islamiyya tafiya ce wadda a ka dora saman Nizamin Musulunci, karkashin koyarwar Al-Kur’ani, da aiki da hankali, ba karkashin Gurbatattun Al-adu ko Son rai da Hauka da Harigido ba. 


Wannan Tsokacin, kokari ne na fadakar da ‘Yan gwagwarmaya, mabiya Sayyid Al-zakzaky (H), dama sauran Musulumi, da masu Hankali, musamman cikin Kiristoci,  masu ra’ayin Shimfida ADALCI da Salama, da tabbatuwar Addini, a kan aiki da tunani da nizami, domin Inganta Hankali, ta yadda za’a iya gujewa fadawa tarkon Adifa (Son rai), da kuma hattara game da hadarin yada kungiyoyanci da Bangaranci a cikin Tafiyar Addini da Zamantakewa. 

Haka domin samun kariya daga hukumomin Shedan, masu sace tunani da gurbata zuciya, masu sanya rauni a tafiya, masu jefa shakku da rudu game da koyarwar Addini ta hakika.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post