Shehu Ibrahim Yaqub Zakzaky (h) Ayar Allah Ga Al'ummar Africa: Da'awarsa Sak Data Annabi Salihu (as).




✍✍Anas Isah Ismail.

Sayyid Zakzaky (H) ya taso da kyakkyawar tarbiyya mai aikata hali na gari wanda kowa ke sonsa yara da manya. Ya taso da jin tausayin qanana da kuma girmama manya tamkar dai dabi'un na fiyayyen halittu Manzon Allah (s) a aikace.

Wadannan kyawawan dabi'u na sheikh Ibrahim yakub EL-ZAKZAKY sun sa jama'a da dama na ganin qimarsa, tun daga samartakarsa har ya zuwa girmansa ya zama daya daga cikin wadanda za'a lissafa cikin wadanda ake sauraron maganarsu.

Manyan mutane basu fara juya masa baya ba har sai lokacin da ya shelanta cewa ba zai bi wannan tsari na kwansitushan ba matuqar ba a dawo kan tsarin Allah ba. Kuma ya soma kiran mutane da su bijirewa wannan tsari na kafirci wanda ba zai jawo musu komai ba sai qasqanci da kuma hasara a lahira.

Ganin wannan ra'ayi nasa da kuma dagewarsa a kansa yasa masu kudi, mulki da miyagun malamai suka soma qalubalantarsa, da canza masa suna da kuma yi masa zagon qasa ta kowacce fuska tare da bayyanar da adawarsu gare shi a fili karara.

Shi kuwa bai fasa kiran da yake yi ba, kuma yana nuna musu cewa shi fa yardar Allah yake nema, kuma binsu ba zai zama komai gare shi ba face hasara. Akan haka suka cigaba da cutar da shi har zuwa yanzu, wanda hakan yayi sanadin fadawar al'umma cikin musifa da bala'i wanda na gobe ya fi nayau.

ANNABI SALIHU (as)

Annabi Salihu (as) ya taso cikin mutanensa da kyawawan dabi'u, basu taba zarginsa da wani hali na muni ba, kuma suna ganin mutuncinsa a idanuwansu da kuma yi masa kyakkyawan fata. Suna nan cikin wannan yanayi har zuwa lokacin da Allah ya aiko shi a Manzo zuwa gare su sannan suka soma ganinsa a matsayin marar tunani da hankali.

Allah (t) yana cewa:-

قَالُواْ يَٰصَٰلِحُ قَدۡ كُنتَ فِينَا مَرۡجُوّٗا قَبۡلَ هَٰذَآۖ أَتَنۡهَىٰنَآ أَن نَّعۡبُدَ مَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا وَإِنَّنَا لَفِي شَكّٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ مُرِيبٖ ٢٦

" Suka ce, " Yaa Salihu ! Ka kasance cikinmu wanda muke yiwa kyakkyawan fata kafin wannan lokaci da ka soma irin wadannan maganganu naka, yanzu kana hana mu mu bautawa abinda ubanninmu suke bautawa ? Lalle mu muna cikin shakku daga abinda kake kiranmu gare shi masu kokonto ne ."

Jin wannan magana daga bakinsu sai yace:-

قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَءَاتَىٰنِ'ي مِنۡهُ رَحۡمَةٗ فَمَن يَنصُرُنِي مِنَ ٱللَّهِ إِنۡ عَصَيۡتُهُۥۖ فَمَا تَزِيدُونَنِي غَيۡرَ تَخۡسِيرٖ ٣٦

" Yace, "Yaa mutanena! Kuna gani yanzu in na kasance akan hujja bayyananniya daga Ubangijina , kuma ya bani rahma daga gare Shi, to, wa zai taimakeni daga cikinku a wajen Allah in har na saba masa umarninsa ta hanyar bin son zuciyarku? Wannan maganar taku ba za ta qare ni da wani abu ba face hasara ."

وَيَٰقَوۡمِ هَٰذِهِۦ نَاقَةُ ٱللَّهِ لَكُمۡ ءَايَةٗۖ فَذَرُوهَا تَأۡكُلۡ فِيٓ أَرۡضِ ٱللَّهِۖ وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابٞ قَرِيبٞ ٤٦

" Kuma Yaa ku mutanena! Lalle wannan Taguwar Allah ce babbar aya gare ku, ku barta tana ci daga qasar Allah, kada ku shafeta da wani cutarwa, sai azaba makusanciya ta shafe ku ba tare da kun sani hakan za ta faru gare ku ba ."

فَعَقَرُوهَا فَقَالَ تَمَتَّعُواْ فِي دَارِكُمۡ ثَلَٰثَةَ أَيَّامٖۖ ذَٰلِكَ وَعۡدٌ غَيۡرُ مَكۡذُوبٖ ٥٦

" Sai suka soke ta . Sai aka ce musu, ku zauna ku dan ji dadi kadan cikin gidajenku na kwana uku kuna jin dadi na qarshe. Wannan wani wa'adi ne wanda ba a qaryata shi in ya zo ."

فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا صَٰلِحٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَمِنۡ خِزۡيِ يَوۡمِئِذٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ ٦٦

" A yayin da al'amarinmu na saukowar bala'i  yazo sai muka tseratar da Salihu tare da wadanda suka yi imani tare da shi da wata rahma daga gare Mu, kuma muka tseratar dasu daga tozarci wannan rana. Lalle Ubangijinka mai qarfi ne mabuwayi. "

وَأَخَذَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلصَّيۡحَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دِيَٰرِهِمۡ جَٰثِمِينَ ٧٦

" Sai tsawa ta kama wadanda su kayi zalunci, sai suka wayi gari cikin gidajensu a gurgurfane !

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post