Abin Da Muke Ziyarta Ya Wuce Kabari, Annabi Muke Ziyararta A Nesa Da Kusa.




— Inji Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) 


“Ka tambayi duk wanda ya je ziyarar Annabi (S), ka zo ka bauta masa ne? Zai ce maka a’a. Yanzu ka samu duk mutane ka bincika, a duniyar nan kaf akwai masu cewa suna bautawa Annabi (S)? Ko mutum daya babu. Ba sabani a kan wannan.


“Kuma ko a kabarinsa ba wanda zai ce maka shi Kabarin yake bautawa, ko kuma shi Manzon da ke ciki yake bauta ma wa. Ya zo gaishe shi ne. Ya zo ya ziyarce shi ne.


“To kuma akwai masu da’awar wai a dena cewa ma an ziyarci Kabari. Nace mu abin da muke ziyarta ma ya wuce kabari, mu Annabi (S) muke ziyarta a nesa da kusa! Mu har yanzu muna ziyarar Annabi, a nesa da kusa.


“(Hatta masu wannan sukan) suna ma da ruwaya cewa, Manzon Allah (S) yace, duk wanda ya yi sallama a gare shi, Allah zai jiyar da shi sallamar, kuma (Annabi) zai maida masa da sallamar.


“Ta yiwu kace a wannan duniyar tamu ba zai yiwu (a ji) ba, amma a duniyar Arwah mai yiwuwa ne. Yanzu ta yiwu kowane mutum yace Assalamu Alaika Ya Rasulallah duk ya ji? Tambaya nake yi. Allah zai yiwu ya jiyar da Annabi sallamar da aka yi masa? Eh. Yauwa. Sai dai in za ka ce Allah ba zai iya jiyar da shi ba. 


“In kace Assalamu alaika Ya Rasullah a ko ina kake, Allah Ta’ala zai jiyar da Annabi (S). Kuma Annabi zai ce maka "Wa’alaikas Salam", sai dai kai ba za ka ji ba. Ko kuma nace ba lallai ka ji ba, don idan wasu bayin Allah suka ce mana sun ji ba za mu yi musu ba.”


— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin ganawa da yan uwa a gidansa da ke Abuja ranar Laraba 16 ga Rabi'ul Auwal 1444 (12/10/2022).a 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post