Shahid Ishaq Muhammad Sulaiman Matashi Abin Koyi


 Da sunan Ubangijin Shahidai ma'abota matsayi da girman daraja. Tsira da aminci su cigaba da tabbata ga Manzon tsira, Annabin Rahama Muhammad (s) tare da Iyalan gidansa ma'abota tsarki. Yardarsa ta kara tabbata ga Shahidan Musulumci tun daga na farko har zuwa na karshen su. (Allah Ya sanyamu daga cikin su).

Shahid Ishaq Muhammad Sulaiman, Matashine wanda aka haifesa a garin Rimin Tudu, Karamar hukumar Mafara ta Jihar Zamfara. Inda yayi karatun zamaninsa (matakin Primary da Secondary) a tsakanin shekara ta 1998 zuwa 2009. Duk cikin yankinsa na karamar hukumar Mafara.

RAYUWARSA : Ga duk wadanda suka yi mu'amala da Shaihid Ishaq koda ta awanni ne, lallai zasu shaidesa da mutum ne ma'abocin fara'a da sakin fuska da yawan wasa da dariya a tsakanin abokai, kannai, yayyai, Iyaye da sauran al’umma. Sannan shi mutumne mai sada zumunci a tsakanin al'umma. Al'umma sun shaidesa da yawaita hakuri, da kawar dakai ga dukkanin abinda bai shafesa ba, gashi jarumine ta kowace fuska.

MU'AMALARSA DA UBANGIJI : Idan muzo wannan bigiren kuwa saidai muyi fatan zama makwafinsa. Allah Ya yiwa Shahida Ishaq baiwar kulawa da dukkanin abubuwan da Allah Ya wajabta Masa. Kamar Sallah, mutum ne ma'abocin yawaita Sallar Nafila, musamman a cikin dare. Sannan an shaidesa da yawaita azumin Nafila. Ta bangaren Infaki kuwa lallai mu kanmu abokanan aikinsa na shafin Ma'asumah mun shaida hakan domin Yana daga cikin Yan uwan da basa jinkirta duk wani infaqi da aka sanya.

GWAGWARMAYARSA : Shahida Ishaq Sulaiman, mutum ne daya amsa sunan Dan gwagwarmaya da cikakkiyar ma'anar gwagwarmaya. Mutumne wanda baya wasa da abinda ya shafi Jagora Sayyid (h). Kokarinsa ne ma ya sanya yayi musharaka a bangarori da dama na cikin harka, Ya kasance shi dan Media ne, Dan dandalin Matasa da sauran wasu dandaloli na cikin harka. Yakan yawaita tunawar da abokanai dangane da al'amarin Iyalan Shahidai da sauke hakkinsu dake wuyanmu, sannan a koda yaushe bashi da burin daya wuce yaga yayi Shahada a karkashin Sayyid (h).

SHAHID DA HARKAR MEDIA : Kasancewarsa daya daga cikin jajirtattun wakilan shafin ‘Ma'asumah Nigerian News Update’ ya wadatu ya tabbatarwa da al’umma irin kokarinsa akan abinda ya shafi Media. Shahid Ishaq daya ne daga wakilan da shafin Ma'asumah ke matukar juyayin rashinsa, wanda samun makwafin gurbinsa ba karamin al'amari bane. Ya kasance ma'abocin cika dukkanin wasu sharudda da aka gindaya da wakilai, gashi mutum ne daya Kasance ma'abocin sadaukar da dukiya, lokaci da Fikhirarsa wajan ganin al'umma ta amfana ta sanadinsa. Hakika munyi kewarka Ya Shahid.

A gaba daya rayuwata, mu'amalar da nayi da Shahid Ishaq ta zahiri bata wuce ta awanni 48 ba, a lokacin damu shiga mu'utamar na Ma'asumah a garin Kano, amma a tsakanin yan awannin nan, na tasirantu da wasu daga cikin kyawawan dabi'unsa, ta yadda har zuwa yanzu ina amfana da mu'amalata dashi. Na koyi yadda ake zama da mutane cikin Aminci, mutum ne wanda baya nuna bambamci a tsakanin al’umma, shi kowa yakan nuna nashi ne, koda ace bai sanka ba, to yakan nuna maka fuskar sani, sannan yayi mu'amala dakai cikin kyakykyawan yanayi. Mutum ne wanda ba zai yiwu kaga bacin ransa cikin sauki ba, shi ma'abocin barkwanci ne domin ya kimsa farin ciki a zukatan Muminai.

SHAHADARSA : Allah sarki Shahid Ishaq, yayi shahadane a wajan baiwa harka gudummawa a bangaren Media. A lokacin da yake kokarin daukar ta'addancin gwamnatin jahar Sokoto domin ya bayyanawa al'umma. A waki'ar Ashura ta Sokoto a ranar 27 ga watan Disambar 2019 ne gwamnatin jahar Sokoto ta harbi Shihid Ishaq a hannu, inda wannan harbin yayi danadiyyar cirewar babban yatsan hannunsa na dama.

Bayan ya shafe kwanaki 14 yana jinya, a ranar 10/01/2020 Allah Ya nufesa da samun babban rabon daya dade ya jira, ma'ana Shahada. Shahid Ishaq yayi Shahada ne yana da kimanin shaikaru 27 a duniya.

Amincin Allah Ya tabbata a Gareka Ya Shahida Ishaq Muhammad Sulaiman, ranar da aka haifeka, ranar da kayi Shahada, da nanar da zaka tashi a gaban Ubangijinka a matsayin mazlumi. 

– Abbakar Ibraheem Kudan.

@ Ma'asumah Nig. News Update 

   27/12/2021.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post