Rabon gado a Musulunci: Kason da babu 'Awl' a cikinsa


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KASON DA BABU AWL CIKINSA

Kamar yadda muka kawo wani kaso jiya wanda aka sami tawaya (decreased) cikinsa sakamakon kason da aka bawa kowa bai kai kasonsa wanda aka ambata cikin Qur'ani ba har muka kira shi da Awl, yau da iznin Allah za mu kawo irin wanda Awl ba ya aukuwa cikinsa.

Yawanci Awl na aukuwa ne idan aka sami dukkan magada an ambaci kason da za a basu, kuma ya zama kason wadanda suka fada cikin magadan yafi qarfin abinda aka bari. Wato idan ance za a bawa kowa wani zai rasa kaso mai yawa daga abinda aka ce a ba shi.

Amma idan ya zama an sami magada wadanda ba a ambaci kasonso ba, to, iya wadanda aka ambata za a bawa, abinda ya saura kuma sai a bawa sauran magada wadanda ba a ambaci nasu kason ba.

                 MISALI 

 تفسير العياشي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مُسْلِمٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: قُلْتُ لَهُ مَا تَقُولُ فِي امْرَأَةٍ مَاتَتْ وَ تَرَكَتْ زَوْجَهَا وَ إِخْوَتَهَا لِأُمِّهَا وَ إِخْوَةً وَ أَخَوَاتٍ لِأَبِيهَا قَالَ 

لِلزَّوْجِ النِّصْفُ ثَلَاثَةُ أَسْهُمٍ وَ لِإِخْوَتِهَا مِنَ الْأُمِّ الثُّلُثُ سَهْمَانِ الذَّكَرُ فِيهِ وَ الْأُنْثَى سَوَاءٌ وَ بَقِيَ سَهْمٌ لِلْإِخْوَةِ وَ الْأَخَوَاتِ مِنَ الْأَبِ- لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏ لِأَنَّ السِّهَامَ لَا تَعُولُ وَ لِأَنَّ الزَّوْجَ لَا يَنْقُصُ مِنَ النِّصْفِ وَ لَا 

الْإِخْوَةُ مِنَ الْأُمِّ مِنْ ثُلُثِهِمْ‏ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ‏ وَ إِنْ كَانَ وَاحِداً فَلَهُ السُّدُسُ وَ أَمَّا الَّذِي عَنَى اللَّهُ فِي قَوْلِهِ- وَ إِنْ كانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلالَةً 

أَوِ امْرَأَةٌ وَ لَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ واحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ‏ إِنَّمَا عَنَى بِذَلِكَ الْإِخْوَةَ وَ الْأَخَوَاتِ مِنَ 

الْأُمِّ خَاصَّةً[19].

Ya zo cikin Tafsir na Ayyashi, daga Muhammad Bn Muslim, daga Abu Ja'afar (A.S) yace: Nace masa; " Me za kace game da matar data rasu ta bar Mijinta da 'yan'uwanta na bangaren mahaifiya (uttering brothers and sisters) da kuma 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata ta bangaren mahaifinta (consanguine brothers and sisters) ? Yace:

" MIJI NA DA RABI, KASO UKU NE, SU 'YAN'UWA TA BANGAREN MAHAIFIYA NA DA KASO 'DAYA CIKIN UKU, MAZA SUKE KO MATA DUK 'DAYA NE. SAURAN KASON DA YA RAGE KUMA NA 'YAN'UWA MAZA DA 'YAN'UWA MATA NE NA BANGAREN UBA, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA KASON MACE. DOMIN SU MASU KASON BA ZA AYI MUSU AWL BA, DOMIN SHI MIJI BA ZA A TAUYE MASA (wani abu) DAGA RABI BA, HAKAMA 'YAN'UWA NA BANGAREN UWA BA ZA A TAUYE MUSU WANI ABU NA DAGA CIKIN 'DAYA BISA UKU BA:

" IDAN SUN KASANCE SUNFI HAKA YAWA SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU, IDAN KUWA YA KASANCE SHI 'DAYA NE, TO, YANA DA 'DAYA BISA SHIDA." (Qur'an)

AMMA WANNAN WANDA ALLAH YAYI MAGANARSA CIKIN FADINSA:

" IDAN MUTUM AKA GAJE SHI A MATSAYIN KALALA (wanda bai haihu ba kuma ba shi da dayan mahaifa), KO KUMA MACE ALHALI YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA, TO, KOWANNE DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BISA SHIDA, IDAN KUWA SUN KASANCE SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN KASHI 'DAYA DAGA UKU."

TO, ABIN NUFI ANAN MAGANA CE KAN 'YAN'UWA MAZA DA 'YAN'UWA MATA NA BANGAREN UWA A KEBE."

               ABIN LURA

Su 'yan'uwa wadanda aka hada Uba dasu anan hukuncinsu daban ne, wato su suna samun abinda ya rage ne komai yawansa kuma komai qanqantarsa, domin hukuncinsu hukuncin 'ya'ya ne idan babu 'ya'ya ne idan babu 'ya'ya. Shi dan'uwa namiji na cin dukiyar dan'uwansa gaba daya idan ya zama ba shi da magada a dabaqar farko ('ya'ya ko mahaifa), ita kuwa 'yar'uwa na cin rabin abinda 'yar'uwa ko dan'uwanta ya bari ne in ba shi da magada mafi kusa. Idan kuma suka hadu 'yan'uwa maza da mata ne sai su zura ido su saurari abinda ya rage, sai kuma namiji ya dau kaso biyu na mace daga sauran abinda suka samu kamar yadda 'ya'ya ke yi.

Da ace cikin wannan magada babu dan'uwa namiji ta bangaren Uba sai dai 'yar'uwa, to, da ita ma za ta shiga cikin wadanda aka ambaci kasonta kenan, wato rabi. Amma tunda tana da dan'uwanta ko 'yan'uwanta maza dole ne su koma gefe su jira abinda ya rage. Shi kuwa miji da 'yan'uwa Li'ummai za a basu cikakken abinda Allah yace a basu.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

3rd January, 2022/ 29th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post