Idan ka wayi gari da Janaba haramun ne ka yi Azumi, – In Ji Abu Huraira



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

UMMUHATUL-MUMININA SUN QARYATA WANNAN ZANCE NASA

Mu kanyi magana ne kan irin wadannan maganganu don don mu 'yanto marar sa karatu daga zurfin jahinci ko kankare musu tsatsar da aka dasa musu cewa wai dukkan Sahabbai adalai ne, domin susan cewa ba a sanya maqaryaci cikin adalai.

Wannan magana da suke yi wai " KULLUHUM UDUULUN " ta taimaka sosai yadda aka shigar da qarerayin maqaryata cikin addinin gaskiya don cutar da addini da wanda yazo da addinin.

An samo cikin qare-rayin Abu Huraira yadda yake cewa wai haramun ne ga wanda ya wayi gari da janaba cikin Ramadan yayi azumi, sai dai Ummuhatul-Muminina sun qaryata wannan zance nasa. Za mu kawo riwayar don kuji yadda ta kasance.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(1)- An bani labari daga Malik, daga Sumayya bawan Abubakar Bn Abdurrahman Bn Haarith Bn Hishaam: Cewa ya ji Abubakar Bn Abdurrahman Bn Haarith Bn Hishaam yana cewa: " Mun kasance ni da banana a wajen Marwan Bn Hakaam, lokacin shine Gwamnan Madinah, sai aka ba shi labari cewa Abu Hurairata yana cewa:

" DUK WANDA YA WAYI GARI DA JANABA YA SHA RUWA A WANNAN RANA ." 

Sai Marwan yace: " Ina yi maka rantsuwa yaa Abdurrahman, lalle za ku tafi zuwa ga Ummul-Muminina A'ishata da Ummus-Salamata ku tambaye su game da wannan magana."

Sai Abdurrahman ya tafi, ni ma na bi shi, har sai da muka shiga wajen A'ishata mu kayi mata sallama sa'an nan yace:

" Yaa Uwar muminai, lalle mu muna tare da Marwan Bn Hakaam sai aka ambata masa cewa lalle Abu Huraira yana cewa: " DUK WANDA YA WAYI GARI DA JANABA YA SHA RUWA A WANNAN RANA." Sai A'ishata tace:

" BA KAMAR ABINDA ABU HURAIRA KE FADA BANE (qarya ne) YAA ABDURRAHMAN. YANZU ZA KU QYAMACI ABINDA MANZON ALLAH (S.A.W.W) KE AIKATAWA?" Sai Abdurrahman yace: " A'a wallahi !" 

A'ishata tace: " NA SHAIDA CEWA MANZON ALLAH (S.A.W.W) YANA WAYEN GARI DA JANABA NA JIMA'I KOMA BAYAN MAFARKI SA'AN NAN YA AZUMCI WANNAN RANA."

Yace: " Sa'an nan muka fita har muka shiga wajen Ummus-Salamata muka tambayeta game da haka, sai ta fadi misalin abinda A'ishata ta fada."

Yace: Sai muka fita har muka zo wajen Marwan Bn Hakaam, sai Abdurrahman ya ba shi labarin abinda suka fada. Sai Marwan yace:

" Ina yi maka rantsuwa yaa baban Muhammad, za ka hau dabbata tana bakin qofa, ku tafi zuwa ga Abu Huraira, yana can qasarsa a Aqeeq, ku ba shi labarin haka (abinda kuka ji daga Ummuhat)."

Sai Abdurrahman ya hau, nima na hau tare da shi har muka jewa Abu Huraira, Abdurrahman yayi hira dashi na tsahon lokaci (ba tare da ya fada masa abinda ke tafe damu ba), sannan ya ba shi labari game da haka. Sai Abu Huraira yace masa:

" NI BANI DA MASANIYA GAME DA HAKA, WANI MAI LABARI NE DAI YA BANI LABARI."

(Muwadda-Malik, Kitabus-Siyaam, babin da yazo cikin wanda ya wayi gari da janaba cikin Ramadan, hadisi mai lamba 640)

To, cikin wannan hadisi za muga cewa abinda Abu Huraira ya riqa yadawa cikin jama'a ita qarya, kuma haramun ko laifi ne mai girman gaske ga mutum ya riqa zabga qarya da sunan addini.

UMMUHATUL-MUMININI SUN QARYATA SHI

Za mu kawo wasu riwayoyi cikin Asahhul-Kutub muji abinda aka kawo kishiyar wannan qarya ta Abu Huraira.

الصائم يصبح جنبا

(1926) - حدثنا عبد الله بن مسلمة، عن مالك، عن سمي، مولى أبي بكر بن عبد الرحمن ابن الحارث بن هشام بن المغيرة: أنه سمع أبا بكر بن عبد الرحمن قال: كنت أنا وأبي حين دخلنا على عائشة وأم سلمة (ح) أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يدركه الفجر، وهو جنب من أهله، ثم يغتسل ويصوم 

وقال مروان لعبد الرحمن بن الحارث: أقسم بالله لتقرعن بها أبا هريرة، ومروان يومئذ على المدينة، فقال أبو بكر: فكره ذلك عبد الرحمن، ثم قدر لنا أن نجتمع بذي الحليفة، وكانت لأبي هريرة هنالك أرض، فقال عبد الرحمن لأبي هريرة: إني ذاكر لك أمرا، ولولا مروان أقسم علي فيه لم أذكره لك، فذكر قول عائشة وأم سلمة، فقال: كذلك حدثني الفضل بن عباس، وهو أعلم 

وقال همام وابن عبد الله بن عمر، عن أبي هريرة: كان النبي صلى الله عليه وسلم يأمر بالفطر."

(2)- Bukhari yace: Abdullahi Bn Muslamata ya bamu labari, daga Malik daga Sumayyi bawan Abubakar Bn Abdurrahman Ibn Haarith Bn Hishaam Bn Mugeerata cewa ya ji Abubakar Bn Abdurrahman yace: " Mun kasance ni da banana yayin da muka shiga wajen A'ishata da Ummus-Salamata, cewa alfijr yana riskar Manzon Allah (S.A.W.W) alhali yana da janaba daga iyalinsa, sannan yayi wanka kuma yayi azumi.

Sai Marwan ya cewa Abdurrahman Bn Haarith: " Ina yi maka rantsuwa da Allah lalle sai an tabbatarwa Abu Huraira (wannan magana don ya guji shirgawa mutane qarya). Shi Marwan a wannan lokaci shine Gwamnan Madinah. Sai Abubakar yace masa: " Sai Abdurrahman ya qyamaci haka, sa'an nan ya tilasta mu cewa mu hadu a Zul-Hulaifa, ya kasance lokacin Abu Huraira ne ke da wannan yanki. Sai Abdurrahman ya cewa Abu Huraira:

" Lalle ni zan ambata maka wani al'amari, da ba don Marwan yayi min rantsuwa a kansa ba, da ba zan baka labarinsa ba. Sai ya ambaci maganar A'ishata da Ummus-Salamata, sai (Abu Huraira) yace:

" AI KAMAR HAKANE FADHAL BN ABBAS YA BANI LABARI, KUMA SHI YAFI SANI."

Sai Himaam da Ibn Abdullahi Bn Umar suka ce daga Abu Hurairata:

" ANNABI (S.A.W.W) YA KASANCE YANA YIN UMARNI DA SHAN RUWA."

(Bukhari, Kitabus-Saumi, Babin mai azumi ya wayi gari da janaba, hadisi mai lamba 1926)

               NAZARI

            ____________

Idan muka nazarci riwaya ta cikin Muwadda-Malik za muga cewa Abu Hurairata ya qi ya ambaci wanda ya fada masa, sai dai yace mai bada labari ne dai ya ba shi labari.

Sannan cikin wannan riwaya ta Bukhari kuma yace Fadhal Bn Abbas ne ya fada masa, wanda hakan ke nuna cewa ba daga Annabi (S.A.W.W) yaji maganar ba. Sai kuma a qarshen riwayar wacce Himaam da Ibn Abdullahi Bn Umar suka fada daga Abu Hurairata shine, wai Annabi (S.A.W.W) yana yin umarni da asha ruwa, wanda hakan ke qara tabbatar mana da qaryarsa qarara !

(3)- Cikin riwayar Muslim kuma cewa yayi

حدثني محمد بن حاتم حدثنا يحيى بن سعيد عن بن جريج ح وحدثني محمد بن رافع واللفظ له حدثنا عبد الرزاق بن همام أخبرنا بن جريج أخبرني عبد الملك بن أبي بكر بن عبد الرحمن عن أبي بكر قال سمعت أبا هريرة رضي الله عنه يقص يقول في قصصه من أدركه الفجر جنبا فلا يصم فذكرت ذلك لعبد الرحمن بن الحارث لأبيه فأنكر ذلك فانطلق عبد الرحمن وانطلقت معه حتى دخلنا على عائشة وأم سلمة رضي الله عنهما فسألهما عبد الرحمن عن ذلك قال فكلتاهما قالت كان النبي صلى الله عليه وسلم يصبح جنبا من غير حلم ثم يصوم قال فانطلقنا حتى دخلنا على مروان فذكر ذلك له عبد الرحمن فقال مروان عزمت عليك إلا ما ذهبت إلى أبي هريرة فرددت عليه ما يقول قال فجئنا أبا هريرة وأبو بكر حاضر ذلك كله قال فذكر له عبد الرحمن فقال أبو هريرة أهما قالتاه لك قال نعم قال هما أعلم ثم رد أبو هريرة ما كان يقول في ذلك إلى الفضل بن العباس فقال أبو هريرة سمعت ذلك من الفضل ولم أسمعه من النبي صلى الله عليه وسلم قال فرجع أبو هريرة عما كان يقول في ذلك قلت لعبد الملك أقالتا في رمضان قال كذلك كان يصبح جنبا من غير حلم ثم يصوم ."

 ...................................................Sai muka tafi har muka shiga wajen Marwan, Abdurrahman ya ba shi labari game da haka. Sai Marwan yace: 

" Na lazimta maka sai ka tafi wajen Abu Hurairata ka tabbatar masa abinda (qaryar) abinda ya fada." Yace: Sai muka jewa Abu Hurairata Abubakar nanan gaba dayansa. Yace: Sai Abdurrahman ya ba shi labari, sai Abu Hurairata yace:

" SHIN, SU BIYUN NE (A'ishata da Ummus-Salamata) SUKA FADI HAKA ?" Yace: " Eh !" Yace: " SU SUKA FI SANI ."

Sa'an nan Abu Hurairata ya mayar da abinda yake fada zuwa ga Fadhl Bn Abbas. Sai Abu Hurairata yace:

" NIMA NA JI HAKAN NE A WAJEN FADHL BN ABBAS, BAN JI SHI A WAJEN ANNABI (S.A.W.W) BA."

Yace: Sai Abu Hurairata ya dawo daga kan abinda yake fada (na qaryarsa) game da haka.

Na cewa Abdul-Malik, shin, sunce cikin Ramadan ne ? Yace: 

" Kamar hakane yana wayen gari da janaba ba ta hanyar mafarki ba kuma yayi azumi."

(Muslim, Kitabus-Saumi, babin Ingancin azumin wanda ya wayi gari da janaba)

Kunji cikin wannan riwayar ma ya qara cewa daga Fadhl Bn Abbas yaji, kuma ya tabbatar ba daga Annabi (S.A.W.W) yaji wannan magana ba.

(4)- Riwaya cikin Sunan Tirmidhi

 «784» حدثنا قتيبة حدثنا الليث عن ابن شهاب عن أبي بكر بن عبد الرحمن بن الحارث بن هشام قال أخبرتني عائشة وأم سلمة زوجا النبي صلى الله عليه وسلم أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يدركه الفجر وهو جنب من أهله ثم يغتسل فيصوم. قال أبو عيسى: حديث عائشة وأم سلمة حديث حسن صحيح. والعمل على هذا عند أكثر أهل العلم من أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم وغيرهم وهو قول سفيان والشافعي وأحمد وإسحاق. وقد قال قوم من التابعين إذا أصبح جنبا يقضي ذلك اليوم. والقول الأول أصح.

.........................................................Abu Isah (Tirmidhi) yace: " Hadisin A'ishata da Ummus-Salamata hadisi ne mai kyau ingantacce. Kuma aiki da wannan a wajen mafi yawan ma'abota ilimi daga Sahabban Annabi (S.A.W.W) da ma wasunsu shine fadin Sufyan da Shafi'i da Ahmad da Ishaq. Kuma haqiqa jama'a daga tabi'ai sunce : " Wanda ya wayi gari da janaba zai rama azumin wannan rana. Amma dai maganar farko (ta cewa za ayi azumi) ita tafi inganta." (In ji Imam Tirmidhi).

باب ما جاء في الجنب يدركه الفجر وهو يريد الصوم:

(Sunan Tirmidhi, Kitabus-Saumi, babin abinda yazo na janaba kuma alfijr ya riske shi alhali yana nufin yin azumi, hadisi mai lamba: 784)

(5)- Cikin Sunan Nisa'i, ya zo kamar haka;

184- أَخْبَرَنَا مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ الأَعْلَى قَالَ: حَدَّثَنَا خَالِدٌ قَالَ: حَدَّثَنَا ابْنُ جُرَيْجٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يُوسُفَ عَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ يَسَارٍ قَالَ دَخَلْتُ عَلَى أُمِّ سَلَمَةَ فَحَدَّثَتْنِي أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يُصْبِحُ جُنُبًا مِنْ غَيْرِ احْتِلاَمٍ ثُمَّ يَصُومُ. وَحَدَّثَنَا مَعَ هَذَا الْحَدِيثِ أَنَّهَا حَدَّثَتْهُ أَنَّهَا قَرَّبَتْ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ جَنْبًا مَشْوِيًّا فَأَكَلَ مِنْهُ ثُمَّ قَامَ إِلَى الصَّلاَةِ وَلَمْ يَتَوَضَّأْ. 

باب تَرْكِ الْوُضُوءِ مِمَّا غَيَّرَتِ النَّارُ: 

(Sunan Nisa'i, Kitabus-Saumi, babin barin alwala daga abinda abinda wuta ta jirkita, hadisi mai lamba: 184)

NB:- Mun taqaita fassara sauran hadisan ne daga farkonsu don gudun tsawaita rubutun namu, shine muka kawo fassarar qarshensu wanda anan darasin ke ciki.

Daga wakilanmu na Bauchi Zone.

Tare da Ado Isah Guda.

     (08137925034)

15th November, 2021/ 10th Rabi'us-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post