Fudiyya Ta Shirya Mu'utamar Na Wuni Daya A Garin Jos

Daga Almustapha A Abdullahi.

A a jiya Alhamis ne, Nigeria tayi bikin cika Shekaru 61 da samun 'Yancin kai wanda ta fita daga sahun budurwa ta shiga sahun tsofi wanda kuma baza mu kirata da komai ba sai tsohuwar najadu, babu wani cigaba da za,ace gashi guda daya wanda aka samu tsawon wannan shekarun da aka dauka.

Duk da naga Shugaban kasa Buhari a wani "video cliff" yana cewa babu wani shugaba da akayi a Nigeria wanda yayi aikin da yayi, sai nace eh kwarai kuwa babu! Amman ta wani janibi? Ta wajen shekar da jini da sace arzikin kasa da tabarbarewar tsaro ta kowani janibi.

Lokacin da turawan nan sukazo sun raba al'ummar Nigeria da Addini sannan kuma an wayi gari a tsawon wannan shekarun da ake ciki a wannan kasar kullum abubuwa kara baya sukeyi al'umma kara nisantar Allah take!







Cikin Ikon Allah aka wayi gari sai Allah ya tayar mana da Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) wanda su Mallam kullum burinsu a tsawon shekarunnan shine yazama al'umma ta farka ta ilimantu har aka wayi gari Malam ya fara karatu da daikun mutane har mastawa takai Malam yace a bude Fudiyya, a wancan lokacin sunan makarantar (Dan Fodiyo) sai daga baya wasu suka bude makaranta suma suka sa mata Dan Fodiyo shine Malam yace to muma zamuyi Fodiyanci kenan shine daga lokacin ta koma suna (Fudiyya).

Dan haka su wakilai na ilimomi da muke dasu a da'irori yakamata susan cewa babban aikine yahau kansu mai girman gaske, saboda 'Ya'yan mu sune jarin mu sune fatan mu, dole ne yazamana mun ilimantar dasu. Wadannan makarantu sune muke fatan su gajemu su faranta ran Malam ta wajen Ilimantar da 'Ya'yan mu, yazamana an ilimantu kuma an sami ingantacciyar Tarbiya.

Daga karshe Sheikh yayi kira ga wakilai akan cewa ya kamata ya zama ana shirya irin wadannan tarurrukan akai akai bawai a dauki dogon lokaci ba kafin asake gabatar da irin wannan taron ba.

 Kadan daga cikin jawabin da Sheikh Adamu Ahmad Tsoho ya gabatar a wajen Mu'utamar na wuni daya wanda Fudiyya ta shirya a garin Jos ranar Asabar wanda yayi daidai da 2/October/2021. 25/Safar/1443H

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post