Cikin Hotuna: Yadda Muzaharar Maulidin Manzon Allah Ta Gudana A Jos

 


Daga Almustapha A Abdullahi.

Kaman yadda aka saba ko wace shekara ranar 12 ga watan Shawwal ana fita duk duniya don nuna farin ciki da Haihuwar Shugaba Halitta Muhammad (S) Wanda Wanda ya hada Sunna da Shi'a.

An gudanar da wannan zagayen Maulidin a garin Jos Inda aka faro daga Markazin Yan uwa inda Gomnatin Janar plateau ta rusa a shekarun da suka gabata, muzahar ta biyo da titin Unguwar Rogo inda ta dangana da bauchi round sannan aka biyo ta yan tifa sannan aka dakko hanyar Babban Masalacin Garin Jos.

Isowar Yan uwa Babban Masallacin Jumma'a na garin jos (Central mosque) Yan Fudiya hadi da yan Jaishi Amirul Mu'uminin (As) sun taka fareti don girmamawa ga Shugaban Halitta Muhammad (S) sannan daga bisani Sha'irai suka karba suka gabatar da gwalagwalan baituka ga Annabi (Saww) 

 Sheikh Adamu Ahmad Tsoho ya gabatar da jawabin rufe Muzahara a babban Masallacin garin Jos. 

Sheikh ya fara da godiya ga Allah (Swt) sannan yayi salati ga Annabi da Ahlulbait (As) Sheikh ya cigaba da taya Al'ummar Murna wanan babban rana mai tarin Albarka sannan kuma yayi kira ga Al'umma dasu bunkasa tarukan Maulidin bawai ya zama iya na yau inyi angama ba ya kamata inda hali a shirya a unguwanni da gidaje. 

Sannan Sheikh ya cigaba da cewa ya zama wajibi a kanmu kaman yadda aka raka siyasa aka jira siyasa har takai ga an kashe rai! Mu sani lallai bamu da Hujja a gaban Allah indai bamuwa Musulinci haka ba. Tunda an gwada PDP an gwada Apc duk munga inda ta kasance to maizai hana mu gwada Musulinci saboda daman tun asali anan mafita take, kin gaskiya ne da makancewar zuciya tasa aka juyawa Addini baya dan haka ya kamata mu shiga hankalinmu a Wannan kasar ko ba komai munga yadda ake kashe kashe da kone kone sakamakon sake Musulinci da akayi. 

Daga karshe Sheikh yayi kira ga Gomnatin Nigeria data gaggauta sakarwa Jagora Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) posspot din sa don yaje ya nemi lafiyar sa.

Mutanen gari sunta furta maganganu kyawawa ga wannan motsin da yan uwa suka yi a birnin jos, kadan daga ciki sun furta cewa lallai wannan fitowar naku ta kasance itace maulidin baki daya kuma muna tare daku sannan kuma muna yiwa Malamin ku Addu'a da Allah ya kara masa kariya da tsawon kwana, wani mutum daya shaida mana cewa hakika shi bai taba ganin abinda ya burgeshi ba kaman dadda yaga Yan Fudiya yau suna taka fareti ba, sannan kuma wani ma ya shaida mana cewa shi babban abinda ya sani ga Yan uwa shine babu wasu mutane dasu ka kaisu nuna kaunar Manzon Allah (S) ba.















 19th/October/2021. 12/Rabi'ul Awwal/1443H

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post