HAQIQANIN MA'ANAR KALALA: Rabon Gado A Muslunci



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

An sami sabani wajen sanin ma'anar KALALA tsakanin Shi'ah da Sunnah yadda takai wannan sabani ya haifar da bambanci wajen yadda ake rabon Gado kan wannan mas'ala. Qur'ani yayi mana bayani dalla-dalla yadda bai kamata ace an sami wannan sabani ba, amma sakamakon shigowar Sarakuna cikin jagorancin muslimci ya haifar da wani rikici mai halakarwa.

Bari dai mu kawo wasu riwayoyi dake nuni game da KALALA don kaucewa wannan matsala.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

1- معاني الأخبار أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ يَزِيدَ عَنِ ابْنِ أَبِي عُمَيْرٍ عَنْ بَعْضِ أَصْحَابِهِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: الْكَلَالَةُ مَا لَمْ يَكُنْ وَالِدٌ وَ لَا وَلَدٌ[1].

(1)- Ya zo cikin Ma'anil-Akhbaar na Abiy, daga Sa'adin daga Ibn Yazeeda, daga Ibn Abiy Umairi, daga sashen Sahabbansa, daga Abu Abdullah (A.S) yace:

" KALALA SHINE WANDA YA KASANCE BAIDA MAHAIFA KUMA BAIDA 'DA ."

 معاني الأخبار ص 272.

Wannan ba wai yana nufin wanda bai taba haihuwa bane, a'a, yana nufin ya mutu bai bar wani daya (1) daga cikin Magada dake cikin dabaqar farko ne, wato babu dayan mahaifa kuma babu wani daga cikin wanda ya haifa. Wannan shi ake nufi KALALA.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

2- تفسير القمي أَبِي عَنِ ابْنِ أَبِي عُمَيْرٍ عَنِ ابْنِ أُذَيْنَةَ عَنْ بُكَيْرٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ لَهُ أُخْتٌ تَأْخُذُ نِصْفَ الْمِيرَاثِ بِالْآيَةِ كَمَا تَأْخُذُ الِابْنَةُ لَوْ كَانَتْ وَ النِّصْفُ الْبَاقِي يُرَدُّ عَلَيْهَا بِالرَّحِمِ إِذَا لَمْ يَكُنْ لِلْمَيِّتِ وَارِثٌ أَقْرَبَ مِنْهَا فَإِنْ كَانَ مَوْضِعَ الْأُخْتِ أَخٌ أَخَذَ الْمِيرَاثَ كُلَّهُ بِالْآيَةِ لِقَوْلِ اللَّهِ- وَ هُوَ يَرِثُها إِنْ لَمْ يَكُنْ لَها وَلَدٌ فَإِنْ كانت [كَانَتَا] أُخْتَيْنِ أَخَذَتَا الثُّلُثَيْنِ بِالْآيَةِ وَ الثُّلُثَ الْبَاقِيَ بِالرَّحِمِ- وَ إِنْ كانُوا إِخْوَةً رِجالًا وَ نِساءً فَلِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ‏ وَ ذَلِكَ كُلُّهُ إِذَا لَمْ يَكُنْ لِلْمَيِّتِ وَلَدٌ أَوْ أَبَوَانِ أَوْ زَوْجَةٌ[2].

(2)- Ya zo cikin Tafsirul-Qummy Abiy daga Ibn Abiy Umairi, daga Ibn Uzainata, daga Bukhairi, daga Abu Ja'afar (A.S) yace:

" IDAN MUTUM YA RASU KUMA YANA DA 'YAR'UWA (shaqiqiya) ZA TA KARBI RABIN ABINDA YA BAR. SABODA AYA (verse) KAMAR YADDA 'YA KE 'DAUKA IN TA KASANCE. SAURAN RABIN KUMA SAI A MAYAR MATA SABODA ZUMUNCI (ya zama ta ci kaso FARDHAN wa RADDAN kenan) IDAN MAMACIN YA KASANCE BA SHI DA MAGAJI WANDA YA FITA KUSANCI .

IDAN KUMA A BIGIREN MACEN NAMIJI NE, TO, ZAI KARBI GADON NE BAKI 'DAYANSA SABODA AYA BISA FADIN ALLAH ; " KUMA SHIMA ZAI GAJE TA INDAN DAI YA KASANCE BATA DA 'DA (namiji ko mace) . IDAN KUMA YA KASANCE 'YAN'UWA MATA BIYU NE (suka gaje shi) SAI SU 'DIBI BIYU BISA UKU BISA YADDA YAZO CIKIN AYA, SAURAN KASHI 'DAYA DAGA KASO UKUN SAI A MAYAR MUSU BISA ZUMUNCI.

IDAN KUMA 'YAN'UWAN MAZA DA MATA NE, TO, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA MACE. HAKAN KUWA NA FARUWA NE IDAN YA KASANCE MAMACIN BA SHI DA 'DA (namiji ko mace) KO KUMA MAHAIFA KO KUMA MATA (wife/wives) ."

(3) تفسير عليّ بن إبراهيم ج 1 ص 160.

Wato idan ya kasance yana da daya daga cikin mahaifa ko 'ya'ya wani dan'uwansa ko 'yar'uwarsa basu da gado. Idan kuma yana da mata (wife/wives) sai a cire mata/musu daya bisa hudu 1/4 , abinda ya rage kuma sai 'yan'uwa su diba gwargwadon yadda bayani yazo a sama.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

3- فس، تفسير القمي‏ وَ إِنْ كانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَ لَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ واحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ‏ فَهَذِهِ كَلَالَةُ الْأُمِّ وَ هِيَ الْإِخْوَةُ وَ الْأَخَوَاتُ مِنَ الْأُمِّ فَإِنْ كَانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ فَهُمْ يَأْخُذُونَ الثُّلُثَ فَيَقْسِمُونَهُ مَا بَيْنَهُمْ بِالسَّوِيَّةِ الذَّكَرُ وَ الْأُنْثَى فِيهِ سَوَاءٌ[3].

(3)- Ya qara zuwa cikin Tafsirul-Qummiy cewa; 

" IDAN MUTUM AKA GAJE SHI BISA KALALA KO KUMA MACE , AMMA KUMA YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA, TO, KOWANNE 'DAYA DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BISA SHIDA. WANNAN SHINE KALALA LI'UMMI, SUNE 'YAN'UWA MAZA DA 'YAN'UWA MATA NA BANGAREN MAHAIFIYA (wadanda suka hadu ta bangaren mahaifiya, 'ya'yan wani gida). IDAN KUMA SUNFI HAKA ( sunfi mutum biyu), TO, (dukkansu) ZASU 'DAU 'DAYA BISA UKU 1/3 NE, SAI SU RABA SHI A TSAKANINSU DAIDAI-WA-DAIDA, KASON NAMIJI SHINE NA MACE (babu bambanci).

(1) تفسير العيّاشيّ ج 2 ص 337.

(3) تفسير عليّ بن إبراهيم ج 1 ص 160.

NB:- 'Yan'uwa wadanda suka hada Uwa da Uba sunfi qarfi akan wanda suka hadu ta bangaren Uba. Idan babu wadanda suka hadu kan Uwa da Uba, to, wadanda suka hadu kan Uba su suka fi kusa, hukuncinsu iri daya ne ana mayar musu sauran abinda ya rage ne na kaso.

Su kuma 'yan'uwa wadanda aka hada Uwa babu bambanci wajen samun kaso, yadda namiji zai samu haka mace za ta samu. Ko dai a bawa kowa daya bisa shida in su biyu ne, ko kuma su hadu kan daya bisa uku in suna da yawa, sai su raba daidai babu fifiko/bambanci.

Abinda ya rage kuma bayan sun dau kason su sai a mayar da sauran zuwa ga Imami na zamani, ba za a mayar dashi gare su kamar yadda ake mayar dashi zuwa ga 'yan'uwa shaqiqai ko Li'abai ba.

Duk misalai uku da muka kawo na sama suna cikin wadannan laittafai na qasa

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(4) نفس المصدر ج 1 ص 133.

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏101، ص 342

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

4th September, 2021/ 27th Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post