Zai iya halatta kayi qarar wani mutum zuwa ha Ɗagutu? Amsa daga ayoyin Qur'ani



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

RAHAMCIN NA TABBATA NE KAN WANDA YA FIFITA HUKUNCIN WANIN ALLAH AKAN NA ANNABI (S.A.W.W)

Tun kwanan baya naso yin magana kan wannan qadhiyya don warware wata shubuha wacce wasu mutane jahilai suka jahilci hukuncinsa sakamakon jahilcin sanin hukuncin Allah dana Ma'aikinsa (S.A.W.W), sai dai Allah bai bani iko ba sai a wannan lokaci.

Bayan nasarar da Allah ya bawa Sayyid Zakzaky (H) akan fasiqai azzalumai kuma fajirai yayi sanadin zuriyar Banu Umayyah (L.A) suka shiga cikin dimuwa da neman dole sai sun nuna gazawar Allah na alqawarin da ya daukarwa kansa cewa zai taimaki muminai akan azzalumai ta hanyar nuna gazawar azzalumai. Hakan yayi sanadin wasu suka dauki wannan abu a matsayin makami na yaqar Allah da kuma mabiya tafarkin iyalan gidan Annabinsa (S.A.W.W) da cewa wai 'yan Shi'ah na farin ciki da hukuncin da 'Dagutu ya zartar alhali kuwa sunce suna gaba da 'Dagutu.

To, yanzu za mu koma cikin littafin Allah (T) don muga menene haqiqanin abinda yake cewa game da kaiwa qara zuwa ga 'Dagutu.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يَزۡعُمُونَ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوٓاْ إِلَى ٱلطَّٰغُوتِ وَقَدۡ أُمِرُوٓاْ أَن يَكۡفُرُواْ بِهِۦۖ وَيُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُضِلَّهُمۡ ضَلَٰلَۢا بَعِيدٗا ٠٦

" SHIN, BAKU GANI BA ZUWA GA WADANDA KE RIYAWA CEWA SUNYI IMANI DA ABINDA AKA SAUKAR ZUWA GARE KA, DAMA ABINDA AKA SAUKAR GABANINKA AMMA SUNA NUFIN KAIWA QARA ZUWA GA 'DAGUTU ALHALI AN AN UMARCE SU CEWA SU KAFIRCI MASA ? KUMA SHAIDAN NA NUFI NE YA BATAR DASU BATA MAI NISA !"

(Suratul-Nisa'i, aya ta 60)

Ba za ka iya fahintar haqiqanin abinda wannan ayar ke karantarwa ba har sai ka san dalilin saukarta. Saboda haka za mu koma cikin Tafsiri don muji menene magabatanmu suka ce game da ayar.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

- حدثني محمد بن المثنى، قال: ثنا عبد الوهاب، قال: ثنا داود، عن عامر في هذه الآية: {ألم تر إلى الذين يزعمون أنهم آمنوا بما أنزل إليك وما أنزل من قبلك يريدون أن يتحاكموا إلى الطاغوت} قال: كان بين رجل من اليهود ورجل من المنافقين خصومة، فكان المنافق يدعو إلى اليهود لأنه يعلم أنهم يقبلون الرشوة، وكان اليهودي يدعو إلى المسلمين لأنه يعلم أنهم لا يقبلون الرشوة، فاصطلحا أن يتحاكما إلى كاهن من جهينة، فأنزل الله فيه هذه الآية: {ألم تر إلى الذين يزعمون أنهم آمنوا بما أنزل إليك} ... حتى بلغ: {ويسلموا تسليما}

Muhammad Bn Muthannah ya bamu labari yace, Abdul-Wahhab ya bada labari yace; Dawud ya bada labari daga Ameer cikin wannan aya:

" SHIN, BA KU GANI BA ZUWA WADANDA SUKE RIYAWA CEWA SUNYI IMANI DA ABINDA AKA SAUKAR ZUWA GARE KA...................."

Yace; Wata husuma ce ta faru tsakanin wani Bayahude da wani mutum daga munafikai (na cikin Sahabban Annabi) . Sai munafukin yake yin kira zuwa (kaiwa qara) ga Bayahude domin ya san cewa shi (Bayahuden) zai karbi rashawa. Shi kuma Bayahuden (wanda ake yin husuma dashi) yana kira cewa akai qarar zuwa ga musulmi domin ya san su ba za su karbi rashawa (bribe) ba. Sai (musulmin) ya zabi su kai qarar zuwa ga wani Boka daga Jahinata. Sai Allah ya saukar da wannan aya a kansa;

" SHIN, BA KA GANI BA ZUWA GA WADANDA KE RIYAWA CEWA SUNYI IMANI DA ABINDA AKA SAUKAR ZUWA GARE KA.............." Har zuwa kan inda Allah ke cewa;

" KUMA SU MIQA WUYA DUKKAN MIQAWA."

           (Tafsirul-'Dabari)

Saboda haka a wannan lokaci da muke cikinsa babu inda ake yin hukunci da littafin Allah ballantana ace mutum ya zabi kaiwa qararsa zuwa gurin ko kuma ya qaurace masa. Sannan kuma babu ayar da tace kaiwa qara zuwa ga wanda ba musulmi ba ko kuma wanda ba da littafin Allah zaiyi hukunci ba ya zama haramun, matuqar dai kasan ba haqqin wani zai danne don biyan buqatarka ba.

Wannanne ya bada dama kayi qarar wani abokin aikinka ko abokin kasuwanci ko kuma abokin sana'a zuwa ga wani na sama daku (Oga) don yayi muku hukunci cikin abinda kuka sami sabani cikinsa.

Saboda haka ko da 'yan'uwa ne suka kai wannan qara don neman haqqinsu ba zai taba haramta ba ballantana su aka kai qararsu, kuma Allah ya taimake su ta hanyar qasqantar da azzalumai masu shigar da qarar. Kenan nuna farin cikinsu anan na nuna godiyarsu ce ga Allah (T) daya ba su nasara.

Wannan dai tunatarwa ce, da fatan masu rabo za su amfana ta hanyar bin gaskiya.

YAA ALLAH KA BAWA SHEIKH ABDUL-JABBAR NASARA KAMAR YADDA KA BAWA SAYYID ZAKZAKY (H) !

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

23rd August, 2021/ 14th Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post