Wasu falaloli ga masu yin kuka kan kisan Imam Hussaini (AS)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KADA KAYI HASARA TA HANYAR RASHIN YIN ZAMAN MAKOKIN IMAM HUSSAINI (A.S)


Al'amarin raya zaman makokin Imam Hussaini (A.S) abu ne mai girman daraja wanda baki ba zai iya kawo shi ba, hakama tunani ba zai taba kirdadon girman ladansa ba.


Ba qaramar daraja bace gare ka a wajen Allah ranar alqiyama ace hawayenka sun taba kwarara 😭😭😭 saboda tuna irin musibar da ta sami Imam Hussaini (A.S) da Sahabbansa da kuma jimlar iyalan gidan Manzon Allah (S.A.W.W).


Tuna abinda ya faru ga iyalan gidan Manzon Allah (S.A.W.W) nuna soyayya ce gare shi (S.A.W.W). Haka kuma rashin nuna damuwarka da abinda ya sami iyalan gidansa (A.S) nuna qiyayyarka ce qarara gare shi (S.A.W.W).


Dangane da falala ko fa'idar da ake samu sakamakon yin kuka 😭 na tuna irin musibar data same su (A.S) da kuma zama gurin da ake raya irin wadannan munasabobi an sami riwayoyi kamar haka:-


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


(1)- الأمالي للصدوق الطَّالَقَانِيُّ عَنْ أَحْمَدَ الْهَمْدَانِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحَسَنِ بْنِ فَضَّالٍ عَنْ أَبِيهِ قَالَ قَالَ الرِّضَا ع‏ مَنْ تَذَكَّرَ مُصَابَنَا وَ بَكَى لِمَا ارْتُكِبَ مِنَّا كَانَ مَعَنَا فِي دَرَجَتِنَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَ مَنْ ذُكِّرَ بِمُصَابِنَا فَبَكَى وَ أَبْكَى لَمْ تَبْكِ عَيْنُهُ يَوْمَ تَبْكِي الْعُيُونُ وَ مَنْ جَلَسَ مَجْلِساً يُحْيَا فِيهِ أَمْرُنَا لَمْ يَمُتْ قَلْبُهُ يَوْمَ تَمُوتُ الْقُلُوبُ‏."


Ya zo cikin Amali na Sudduq Addalaqaniyyu, daga Ahmad Al-Hamdaniyyu, daga Aliyu Bn Hassan Bn Fadhali, daga babansa yace; Ridha (A.S) yace;


" DUK WANDA YA TUNA DA ABINDA YA SAME MU (na musibu) KUMA YAYI KUKA SABODA ABINDA YAZO DAGA GARE MU, TO, YA KASANCE TARE DAMU CIKIN DARAJARMU RANAR ALQIYAMA. KUMA WANDA (yaji) AKA AMBACI ABINDA YA SAME MU (na musiba) HAR YAYI KUKA YAYI KUKA, TO, IDANUWANSA BA ZA SUYI KUKA BA A RANAR DA IDANUWA KE YIN KUKA . SANNAN KUMA WAND YA ZAUNA A GURIN ZAMAN DA AKE RAYA AL'AMRANMU, TO, ZUCIYARSA BA ZA TA MUTU BA A RANAR DA ZUKATA KE MUTUWA."


أمالي الصدوق المجلس 17- الرقم 4.


Idan muka kalli ko nazarci wannan hadisi za muga yana karantar damu ne fa'idar yin kuka na zubar da hawaye yayin da aka tuna irin musibar data sami iyalan Annabi (S.A.W.W) a ranar Karbala, da kuma falalar halartar guraren da ake raya al'amransu (A.S).


Hadisi na gaba kuma na cewa;


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


الأمالي للشيخ الطوسي الْمُفِيدُ عَنِ الْجِعَابِيِّ عَنِ ابْنِ عُقْدَةَ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ عَبْدِ الْحَمِيدِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَمْرِو بْنِ عُتْبَةَ عَنِ الْحُسَيْنِ الْأَشْقَرِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي عُمَارَةَ الْكُوفِيِّ قَالَ سَمِعْتُ جَعْفَرَ بْنَ مُحَمَّدٍ ع يَقُولُ‏ مَنْ دَمَعَتْ عَيْنُهُ فِينَا دَمْعَةً لِدَمٍ سُفِكَ لَنَا أَوْ حَقٍّ لَنَا نُقِصْنَاهُ أَوْ عِرْضٍ انْتُهِكَ لَنَا أَوْ لِأَحَدٍ مِنْ شِيعَتِنَا بَوَّأَهُ اللَّهُ تَعَالَى بِهَا فِي الْجَنَّةِ حُقُباً[6].


Ya zo cikin Amaliy na Sheikh 'DusiyAl-Mufidu, daga Ji'abiy, daga Ibn Uqdata, daga Ahmad Bn Abdul-Hameed, daga Muhammad Bn Amruu Bn Utubata, daga Hussaini Al-Ashqari, daga Muhammad Bn Abiy Umarata Al-kufiy yace; " Naji Ja'afar Bn Muhammad (A.S) yana cewa;


" DUK WANDA IDANUWANSA SUKA YI KUKA SABODA MU, KUKA SABODA JININ DA AKA ZUBAR MANA KO KUMA SABODA WANI HAQQI NAMU DA AKA TAUYE SHI, KO KUMA MUTUNCINMU DA AKA ZUBAR, KO KUMA (yayi kuka) SABODA WANI DAGA CIKIN MABIYANMU , ALLAH MADAUKAKI ZAI ZAUNAR DASHI CIKIN ALJANNAH BABU YANKEWA (saboda wannan zubar da hawaye nasa) ."


أمالي الشيخ الطوسيّ: ص 121.


Shi kuma wannan hadisi ya nuna cewa ko zafin danne haqqinsu ne da akayi ko mutuncinsu da aka zubar yayi sanadin zubar hawayenka, to, za a zaunar daka cikin Aljannah wacce dadinta ba shi da qarshe.


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda.


       (08137925034)


15th August, 2021/ 6th Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post