Su Sayyid Zakzaky (h) Sun Gama Dai-daita Komai..!!



Idan har Allah muka nufa, zantukan jagorammu ya ishemu mu natsu haka nan, mu aje duk wani son zuciya mu aje kalaman ɓatanci ga wani ko jefe-jefen maganganu kowwa yayi ta kanshi.


Malam Zakzaky (H) ya yabi kowwa ni a wajena, saboda su Malam sun ce; akwai waɗanda ma sun bada gudummuwarsu yadda ba a tsammani kuma ba a sansu ba suna a ɓoye ba buƙatar a kama sunansu, sannan in muna da lura su Malam (H) sun ankarar da mu cewa; waɗannan rarrabe rarraben na wane ɗan kaza, wane ɗan kaza, kawai aikin maƙiya ne. 


Kun ga tunda jagora yayi ishara kuma ya ce kowwa yayi aikin da yake iyawa ne, gwargwadon iyawarsa har ma ya bada misali da Infaƙi... Wannan ya ishemu ishara cewa; Sayyid Zakzaky (H) shi rahama ne ga kowwa da kowwa ba gurin shi wani ya fitinu ya daina harka ba, ko kuma ya ce ya kori wani ba kamar yadda wasu suke tsammani. In ban manta ba a wani jawabin Su Malam ya taɓa cewa; mu hatta ’yan tawiyya da zasu dawo mu ci gaba da tafiya ba matsala, kai ya ce ma muna masu addu'ar shiriya to balle wanda saɓanin fahimta ne ya haɗa kawai bai kamata mu ci gaba da jifar juna da jafa'i da ƙoƙarin fitinar da wani ba.


Yanzu dan Allah idan muka ci gaba da tafiya haka, ya zamu fuskanci al’ummar da  ke fuskanto mu ( Sabbin masu fahimtar da'awar a wanannan yanayi) alhali muma a junammu muna aibata juna wancan na ganin wane ya kauce wancan na kallon shi ke kan dai-dai. In har suka same mu a haka su ma fa zasu bi shanun sarki ne karshenta kuma mu ne sila kuma Allah zai tambayemu.


Ina mai tunatar da juna da mu tsaya mu yi tadabburin zantukan jagora mu ɗabbaƙa su, su Malam sun gama warware komai wallahi sai dai son zuciyoyimmu su hana mu kama abinda ya kamata. 


Allah ka ƙara wa su Malam lafiya ka kuma ƙara haɗa kan 'yan’uwa baki ɗaya. Ina neman afuwa ga wanda rubutuna ya saɓa wa fahimtarsa ni dai haka na fahimta, shi kuma ban ce nasa tunanin ba dai-dai ba ne. Allah ka tabbatar da mu ka yi mana taufiƙi cikin sabon shafin da Jagorammu yayi mana isharar buɗewa.


_Bin Yaqoub Katsina✍🏾

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah ta'ala ya sakama jagora da alheri,mukuma Allah ya ba mu ikon dafamasa sau da qafa, Allah ya kare dukkanin Yan uwa daga makircin masu san suga sun tarwatsa wannan fikra

    ReplyDelete
Previous Post Next Post