Labarin da Allah ya Baiwa Annabawa Game da Shahadar Imam Hussain (as) !!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KISAN IMAM HUSSAINI (A.S) BAI BUYA GA ANNABAWA (A.S) BA


Al'amarin kisan Imam Hussaini (A.S) bai kamata ace ya zama majhulin al'amari wajen malamai ko wajen  ma'abota neman ilimi ba.


Tun kafin a haifi Manzon Allah (S.A.W.W) wanda ya kasance shine kaka wajen Imam Hussaini (A.S) Allah (T) ya sanar da wadanda suka gabace shi daga Annabawa (A.S) , sai ya zama sunar Allah sanar da wannan al'amari ga Annabawa (A.S) tun kafin wannan waqi'a ta faru.


Bari mu shiga cikin nassi don gano wannan al'amari mai kawar da shakku ga dukkan wani mai imani masoyin Manzon Allah (S.A.W.W).


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


 الإحتجاج سَعْدُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ: سَأَلْتُ الْقَائِمَ ع عَنْ تَأْوِيلِ‏ كهيعص‏ قَالَ ع هَذِهِ الْحُرُوفُ مِنْ أَنْبَاءِ الْغَيْبِ اطَّلَعَ اللَّهُ عَلَيْهَا عَبْدَهُ زَكَرِيَّا ثُمَّ قَصَّهَا عَلَى مُحَمَّدٍ عَلَيْهِ 

وَ آلِهِ السَّلَامُ وَ ذَلِكَ أَنَّ زَكَرِيَّا سَأَلَ اللَّهَ رَبَّهُ أَنْ يُعَلِّمَهُ أَسْمَاءَ الْخَمْسَةِ فَأَهْبَطَ عَلَيْهِ جَبْرَئِيلَ ع فَعَلَّمَهُ إِيَّاهَا فَكَانَ زَكَرِيَّا إِذَا ذَكَرَ مُحَمَّداً وَ عَلِيّاً وَ فَاطِمَةَ وَ الْحَسَنَ ع سُرِّيَ عَنْهُ هَمُّهُ وَ انْجَلَى كَرْبُهُ وَ إِذَا ذَكَرَ اسْمَ الْحُسَيْنِ خَنَقَتْهُ الْعَبْرَةُ وَ وَقَعَتْ عَلَيْهِ الْبُهْرَةُ فَقَالَ ع ذَاتَ يَوْمٍ إِلَهِي مَا بَالِي إِذَا ذَكَرْتُ أَرْبَعَةً مِنْهُمْ تَسَلَّيْتُ بِأَسْمَائِهِمْ مِنْ هُمُومِي وَ إِذَا ذَكَرْتُ الْحُسَيْنَ تَدْمَعُ عَيْنِي وَ تَثُورُ زَفْرَتِي فَأَنْبَأَهُ اللَّهُ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى عَنْ قِصَّتِهِ فَقَالَ- كهيعص‏ فَالْكَافُ اسْمُ كَرْبَلَاءَ وَ الْهَاءُ هَلَاكُ الْعِتْرَةِ الطَّاهِرَةِ وَ الْيَاءُ يَزِيدُ وَ هُوَ ظَالِمُ الْحُسَيْنِ وَ الْعَيْنُ عَطَشُهُ وَ الصَّادُ صَبْرُهُ فَلَمَّا سَمِعَ ذَلِكَ زَكَرِيَّا لَمْ يُفَارِقْ مَسْجِدَهُ ثَلَاثَةَ أَيَّامٍ وَ مَنَعَ فِيهِنَّ النَّاسَ مِنَ الدُّخُولِ عَلَيْهِ وَ أَقْبَلَ عَلَى الْبُكَاءِ وَ النَّحِيبِ وَ كَانَ يُرْثِيهِ إِلَهِي أَ تُفَجِّعُ خَيْرَ جَمِيعِ خَلْقِكَ بِوَلَدِهِ إِلَهِي أَ تُنْزِلُ بَلْوَى هَذِهِ الرَّزِيَّةِ بِفِنَائِهِ إِلَهِي أَ تُلْبِسُ عَلِيّاً وَ فَاطِمَةَ ثِيَابَ هَذِهِ الْمُصِيبَةِ إِلَهِي أَ تُحِلُّ كُرْبَةَ هَذِهِ الْمُصِيبَةِ بِسَاحَتِهِمَا ثُمَّ كَانَ يَقُولُ إِلَهِي ارْزُقْنِي وَلَداً تَقَرُّ بِهِ عَيْنِي عَلَى الْكِبَرِ فَإِذَا رَزَقْتَنِيهِ فَافْتِنِّي بِحُبِّهِ ثُمَّ أَفْجِعْنِي بِهِ كَمَا تُفْجِعُ مُحَمَّداً حَبِيبَكَ بِوَلَدِهِ فَرَزَقَهُ اللَّهُ يَحْيَى وَ فَجَّعَهُ بِهِ وَ كَانَ حَمْلُ يَحْيَى سِتَّةَ أَشْهُرٍ وَ حَمْلُ الْحُسَيْنِ ع كَذَلِكَ الْخَبَرَ .



Ya zo cikin Ihtijaaj na Sa'adu Bn Abdullahi yace:  Na tambayi Qa'eem (A.S) game da tawilin haruffan farko na suratul-Maryama (S.A) sai yace (A.S);


" Wadannan harufa na daga cikin labaran Ghaibu wanda Allah ya sanarwa bawansa Zakariyyah (A.S), sannan ya bada labarinsa ga Muhammad (S.A.W.W).


Hakan kuwa ta faru ne yayin da Zakariyyah ya roqi Allah Ubangijinsa da ya sanar dashi sunayen abubuwa biyar (5), sai Jibrilu (A.S) ya sauko a kansa ya sanar dashi su (sunayen).

Zakariyyah ya kasance idan ya ambaci Muhammadu da Aliyu da Fatimah da Hassan sai farin ciki ya lullube shi, sai baqin cikinsa ya kauce.


Kuma idan ya ambaci sunan Hussaini sai firjici ya lullube shi kuma baqin ciki ya bijiro masa.


Sai wata rana (A.S) yace;


" YAA ABIN BAUTANA ! MENENE YASA IDAN NA AMBACI HUDU DAGA CIKINSU SAI DAMUWATA TA KWARANYE SABODA AMBATON SUNAYENSU ? KUMA IDAN NA AMBACI HUSSAINI SAI IDANUWA SU CIKA DA HAWAYE 😭 ?......."


Sai Allah (T.W.A) ya bashi labari game da qissarsa, yace;


" كٓهيعٓصٓ "


" AI WANNAN KAFUN 'DIN SHINE SUNAN KARBALA, HA'UN KUMA SUNE TSARKAKAKKUN TSATSO, YA'UN KUMA SHINE YAZIDU (L.A), SHINE WANDA YA ZALUNCI HUSSAINI, AINUN KUMA SHINE QISHIRWA (wacce Imam Hussaini da Sahabbansa suka sha), SADUN KUMA SHINE HAQURINSA (Hussaini)."


Yayin da Zakariyyah yaji haka bai bar Masallaci ba na tsahon kwana uku, kuma ya hana mutane shiga zuwa gare shi. Na cigaba da kuka 😭 da shassheqa.


Ya kasance yana ambatonsa;


" YAA ABIN BAUTANA !  YANZU ZA KA JARRABCI MAFI ALKHAIRIN HALITTUNKA TA HANYAR 'DANSA ?


YAA ABIN BAUTANA ! YANZU ZA KA SAUKAR DA DAMUWA GA WANNAN ZURIYYA TA HANYAR QARAR DA SHI ?


YAA ABIN BAUTANA ! YANZU ZA KA LULLUBE ALIYU DA FADIMATU DA TUFAFIN MUSIBA ?


YAA ABIN BAUTANA ! YANZU ZA KA HALATTA BAQIN CIKIN WANNAN MUSIBA A TARE DASU ? "


Sa'an nan ya kasance yana cewa ;


" YAA ABIN BAUTANA ! KA AZURTANI DA WANI YARO WANDA ZAN RIQA JIN SANYIN IDO DA SHI AKAN TSUFATA. IDAN KA AZURTANI SHI KA JARRABCE NI DA SONSA,  SA'AN NAN KA JARRABCE NI DASHI KAMAR YADDA KA JARRABCI MUHAMMADU  MASOYINKA DA 'DANSA."


Sai Allah ya azurta shi da Yahya kuma ya jarrabce shi dashi (aka yanka shi kamar yadda aka yanka Hussaini). Tsahon cikin Yahya (a cikin mahaifiyarsa) wata shida (6), kuma cikin Hussaini (A.S) ma kamar haka yake.


(1) الاحتجاج ص 239.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏44، ص: 224



Sannan kuma Annabi (S.A.W.W) shima ya bada labari game da kisan 'Dan nasa Hussaini (A.S) kamar yadda za mu gani cikin wannan riwayar dake tafe insha Allahu.


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


 الأمالي للصدوق أَبِي عَنْ حَبِيبِ بْنِ الْحُسَيْنِ التَّغْلِبِيِّ عَنْ عَبَّادِ بْنِ يَعْقُوبَ عَنْ عَمْرِو بْنِ ثَابِتٍ عَنْ 

أَبِي الْجَارُودِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع‏ قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ ص فِي بَيْتِ أُمِّ سَلَمَةَ فَقَالَ لَهَا- لَا يَدْخُلْ عَلَيَّ أَحَدٌ فَجَاءَ الْحُسَيْنُ ع وَ هُوَ طِفْلٌ فَمَا مَلَكَتْ مَعَهُ شَيْئاً حَتَّى دَخَلَ عَلَى النَّبِيِّ فَدَخَلَتْ أُمُّ سَلَمَةَ عَلَى أَثَرِهِ فَإِذَا الْحُسَيْنُ عَلَى صَدْرِهِ وَ إِذَا النَّبِيُّ يَبْكِي وَ إِذَا فِي يَدِهِ شَيْ‏ءٌ يُقَلِّبُهُ فَقَالَ النَّبِيُّ يَا أُمَّ سَلَمَةَ إِنَّ هَذَا جَبْرَئِيلُ يُخْبِرُنِي أَنَّ هَذَا مَقْتُولٌ وَ هَذِهِ التُّرْبَةُ الَّتِي يُقْتَلُ عَلَيْهَا فَضَعِيهِ عِنْدَكِ فَإِذَا صَارَتْ دَماً فَقَدْ قُتِلَ حَبِيبِي فَقَالَتْ أُمُّ سَلَمَةَ يَا رَسُولَ اللَّهِ سَلِ اللَّهَ أَنْ يَدْفَعَ ذَلِكَ عَنْهُ قَالَ قَدْ فَعَلْتُ فَأَوْحَى اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ إِلَيَّ أَنَّ لَهُ دَرَجَةً لَا يَنَالُهَا أَحَدٌ مِنَ الْمَخْلُوقِينَ وَ أَنَّ لَهُ شِيعَةً يَشْفَعُونَ فَيُشَفَّعُونَ وَ أَنَّ الْمَهْدِيَّ مِنْ وُلْدِهِ فَطُوبَى لِمَنْ كَانَ مِنْ أَوْلِيَاءِ الْحُسَيْنِ وَ شِيعَتُهُ هُمْ وَ اللَّهِ الْفَائِزُونَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ .


Ya zo cikin Amali na Sudduq Abiy, daga masoyina Bn Hussaini At-Taghlibiy, daga Abbad Bn Ya'aquba, daga Amruu Bn Thaabit, daga baban Jaruud, daga Abu Abdullah (A.S) yace:


" Annabi (S.A.W.W) ya kasance a gidan Ummus-Salamata, sai yace mata: " KADA WANI YA SHIGO GARE NI ."


" Sai Hussaini (A.S) ya shigo yana dan jariri, bai mallaki wani abu tare dashi ba har ya shigo ga Annabi (S.A.W.W), sai Ummus-Salamata ta shigo a bayansa. Sai ga Hussaini akan qirjinsa (S.A.W.W) kuma yayin da Annabi (S.A.W.W) ke yin kuka. Kuma cikin hannunsa akwai wani abu yana jujjuya shi.


Sai Annabi (S.A.W.W) yace: " Yaa Ummus-Salamata ! Lalle wannan Jibrilu ne yana bani labari cewa wannan (Hussaini) kashe shi za ayi. Kuma wannan ce qasar da za a kashe shi a kanta, ki ajiyeta a wajenki, a duk lokacin da ta zama jini, to, an kashe abin sona 😭😭 !"


Sai Ummus-Salamata tace: " Yaa Ma'aikin Allah ! A tunkudar da wannan (kisa) mana gare shi ." Yace:


" HAQIQA NA AIKATA. SAI ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YAYI MIN WAHAYI CEWA; " LALLE HAKAN DARAJA CE GARE SHI, KUMA BABU MAI SAMUNTA DAGA HALITTU. KUMA TARE DASHI AKWAI MABIYA MASU NEMAN CETO, KUMA ZA A CECE SU. SANNAN KUMA MAHDI DAGA 'YA'YANSA YAKE.


DADI (joy) YA TABBATA GA WANDA YA KASANCE CIKIN MASOYAN HUSSAINI KUMA MABIYINSA, WALLAHI SUNE MASU RABAUTA RANAR ALQIYAMA ."


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏44، ص: 226


Yaa Allah ka tabbatar damu cikin masoyansa kuma mabiyansa har bayan tashin alqiyama.


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda.


       (08137925034)


10th August, 2021/ 2nd Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post