Jami'an Gwamanti 6 Da Suka Raka Ni Indiya Ne Ke Rike Da Takardu da Fasfo Dina; – Shaikh Zakzaky

An gano hakan ne tun daga sakon da Sheikh Zakzaky ya aiko a ranar Laraba, 14 ga watan Agustan 2019, inda har zuwa yanzu basu bashi takardu da Fasfo din nasa ba.

Ga abinda shehin malamin yake fada cikin sakon nasa; “Sannan har lokacin nake ce musu na ga kune kuke riƙe da FASFO na mu komai na hannun ku, amma idan mu kaje filin jirgi DELHI muka sauka, lalle ni Bazan yarda na bar filin jirgin sama ba, sai na ga likitocin da muka amince da su” —Shaikh Ibraheem Zakzaky

Wannan wani ɓangaren Jawabin Shaikh Zakzaky ne da ya aiko daga Asibitin Medanta da ke ƙasar Indiya ranar Laraba, 14 ga watan Agustan 2019, bayan hukumomin Najeriya sun wargaza shiri bayan isar shi Indiya jinya. A cikin jawabin da yayi bayan yayi na farko a bayyana cewa lalle duka takardun su da Fasfo an damƙa hannun jami'an gwamnati 6 da suka rako su daga Najeriya, ga wani ɓangare na jawabin na rubuto.

“Lalle siƙa ɗin mu da wannan asibitin ya kawo ƙarshe, saboda dama wasu likitoci ne a Najeriya suka bada shawarin wannan asibiti akayi tsari da komai yanzu kuma bayan zuwan mu sai mu kaga wani abu daban! An canza komai, sannan su likitocin da muka sani muka aminta da su, wai bama da su za'ayi aikin ba, amma de suna iya bada shawara. Na sai na maimaita komai ba, amma de almuhim gaskiya siƙa ɗin mu da wannan asibitin ya ƙare.

“Kuma lalle ba zamu zauna a nan asibitin kamar muna gidan yari ba, sai a kaimu wani Hotel, DOMIN DUKA FASFUNAN MU YANA HANNUN SU, idan mun tashi tafiya sai mu tafi tare da waɗanda suka rakomu, ko kuma ma'aikatan su da suke nan. Ina yaso sai su zauna suna gadin mu a ƙofar Otel ɗin. Su ma ƴan sanda bamu ƙiba idan ma za suyi gadin mu suyi a wajen Otel ɗin, ba'a cikin Otel ko a ƙofar ɗaki ba.

“Sannan da su kace wai an fara wasu abubuwa tin a Dubai, wai mene-mene, to, kun san de irin maganan su. A Dubai de mun tattauna da jami'an har ma mu kayi 'introduction' cewa; wannan shi ne wane, wannan shi ne wane! Saboda ba mu samu yi a Abuja ba, haka muka taho babu sanayya. Sannan har lokacin nake ce musu na ga kune kuke riƙe da FASFO na mu komai na hannun ku, amma idan mu kaje filin jirgi DELHI muka sauka, lalle ni bazan yarda na bar filin jirgin sama ba, sai na ga likitocin da muka amince da su.

“Bayan mun iso har nake faɗawa likitocin da suka zo tarban mu cewa mu 'Family' ne mu 11 da mu mu 5 da kuma jami'an gwamnati su 6 da suka rako mu. Aka karbi FASFO na mu aka lissafa aka ga lalle sun cika 11 sannan aka wuce da mu 'Immigration' aka deɓi kayan mu aka loda a waje guda, a kace mu zamu shiga 'Ambulance' sauran kuma suzo a wasu motoci daban, hakan kuma akayi. Wannan shi ne abinda ya faru kuma FASFO na mu guda 11 haka aka damka musu a hannun su (su jami'an gwamnati 6 da suka yi rakiya), to, ban san meye abinda Al-Zakzaky yayi ba, da suke cewa wai munƙi bin ƙai'da.

“Kuma abinda su suke fadawa gwamnatin Indiya shi ne, cewa su ne suka kawo mu, munyi jinya sannan a kula da mu a matsayin wasu mutane da ake tuhuma da miyagun lefuka. Alhali mu muka kawo kan mu, muka ɗauki ɗawainiyan kan mu, muka nemi asibitin, su kawai na su sa'ido ne amma sun sa baki da hannu kai har ƙafa ma sun sa sun hamɓare”.

Daga Shafin Bilya Hamza Dass

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. FREE ALLAMA SAYYID ZAKZAKY(H) AND MALAMA ZINAT PASSPORT

    ReplyDelete
Previous Post Next Post