Hukuncin wanda aka same shi da wasu laifuka Uku



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WANNENE ZA A FARA DAGA KANSA ?

Bisa dabi'a irin ta 'yan Adam an sansu da aikata laifuffuka kala-kala a lokaci guda tare da sanin anyi hani a kansu. Saboda haka sai ka samu hukunci masu yawa sun hau kan mutum sakamakon aikata laifuffuka mabambanta.

To, idan haka ta kasance da wanne hukunci za a fara hukunta shi bayan zartar masa da hukuncin laifuffukan ? Ga yadda za a fara hukunta wanda ya aikata wadannan laifuffuka uku.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

قرب الإسناد عَنْ عَلِيٍّ عَنْ أَخِيهِ ع قَالَ: سَأَلْتُهُ عَنْ رَجُلٍ أُخِذَ وَ عَلَيْهِ ثَلَاثَةُ حُدُودٍ الْخَمْرُ وَ الزِّنَا وَ السَّرِقَةُ بِأَيِّهَا يُبْدَأُ مِنَ الْحُدُودِ قَالَ بِحَدِّ الْخَمْرِ ثُمَّ السَّرِقَةِ ثُمَّ الزِّنَا[1].

Ya zo cikin Qarrabul-Isnaad, daga Aliyu daga dan'uwansa yace:

An tambaye shi game da mutumin da aka same shi tare dashi akwai haddodi 3, Giya da Zina da kuma sata. Wanne za a fara daga cikin haddodin ? Yace:

" DA HADDIN GIYA, SA'AN NAN SATA, SA'AN NAN ZINA ."

(2) قرب الإسناد ص 112 ط حجر.

Dalilin farawa da hukuncin Giya kuwa shine, hukuncin Giya shi yafi qanqanta domin bulala ce. Sata kuwa yanke hannu ne idan an saci abinda qimarsa takai na hanke hannu.

Zina kuwa shi yafi komai girma, domin bulala 100 ce ga wanda bai taba yin aure ba, idan kuwa ya tafa yin aure sai a jefe shi bisa haddi.

In da za ace ka fara daga hukuncin zina na kisa, to, zai koma ga Allah kenan da sauran hukuncin laifuka biyu a kansa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

30th August, 2021/ 22nd Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post