Duk Wanda Yake Son Mu Juyawa Sheikh Dr. Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara Baya To Ga Dama Ta Samu ..!!

 Kashi Na Farko (1)Daya Daga Cikin Ruwayoyin Da Suka Taba Janibin Manzon Allah  😭😭


Duk Wanda Yake Son Mu Juyawa Sheikh Dr. Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara Baya To Ga Dama Ta Samu, Ga Daya Daga Cikin Masalolin Da Tambayar Da Muke Bukatar Warwareta Da Karbata Daga Masu Ganin Cewa Muna Kan Kuskure, Kuma Suna Son Fitar Damu Daga Wannan Kogon Domin Suna Ganin Cewa Kogon Halaka Ne. 🤔🤔


Da Farko Ina Son Mai Karatu Kayi Hakurin Biyar Wannan Rubutu Bayan Ka Kammala  To Sai Kayi Hukunci A Kaina, Amma Ka Fara Amsa Wannan Tambayoyin Guda Ukku (3).


1. Dan Allah A Yarin Hausa Idan Akace Ga Wani Magidanci Duk Rana Yana Kewaya Matansa -Jima'i- Su Goma Sha Daya (11) Da Safe Ya Koma Mai-Mai Tawa A Dare, Idan Zan Fadi Sunansa Da Aikin Da Yake A Yaren Hausa Miye Zan Kirasa....??? 


2. Dan Allah A Yarin Hausa Idan Akace Ga Wani Magidanci Duk Rana Yana Kewaya Matansa -Jima'i- Su Goma Sha Daya (11) Da Safe Ya Koma Mai-Mai Tawa A Dare, Idan Zan Kwatanta Wannan Aikin Da Yakeyi Da Wata Dabba Daga Cikin Dabbobi.. Da Wace Dabba Zan Kwatantashi...??? 


3. Dan Allah Magidanci Ne Akace Duk Rana Yana Kewaya Matansa -Jima'i- Su Goma Sha Daya (11) Da Safe Ya Koma Mai-Mai Tawa A Dare, Kuma Sai Ga Wani Labari Cewa Idan Ya Fita Waje Yaga Macce Akan Hanya Sha'awarsa Zata Mutsa Har Ya Kasa Mallakar Kansa Sai Yaje Yayi Jima'i Da Iyalinsa, Idan Nace Dashi Mai. Tsananin Sha'awa Nayi Dai-Dai Ko Nayi Kuskure...???


To Mu Waiwaya Muga Wata Ruwaya Da Malaman Hadisi Suka Rawaito Mu Fara Da Limaminsu Imamul-Bukhari Acikin "Littafen Wanka" -Babe Mai Bayanin Idan Mutum Yayi Jima'i Sannan Ya Sake Koma Jima'i Da Wanda Yayi Jima'i Da Matansa Duka Da Wanka Daya- Lambar Hadisi 265 Ya Maimaitashi Acikin "Littafen Aure" -Babe Mai Bayanin Wanda Ya Kyewaya Matansa -Jima'i- Acikin Wanka Daya- Lambar Hadisi 278,4917,5068,5215,284.


Abdurrazzak San'ani Acikin "Musannaf" Lambar Hadisi 1061, Ibn Khuzaima 230, Ahamad Bin Hambal Acikin "Musnadu" 11946, 1264, 12701, 12925, 12926, 12967, 13505, 13555, Nasa'i Acikin "Kubura" Lamba 933, Ibn Sa'ad Acikin "Addabakah" J/1 S/374 Abu Ya'ala Lambar Hadisi 2941, 3176, 3202, 3717, Dahaweey Acikin "Sharhu Ma'aneey Al'asar" J/1 S/129, Addabaraneey Acikin "Sager" 682, Jbn Maja 589, Ibn Hibban 1207, Da Wasansu Da Yawa. 


Mu Dauke Lafazin Imamu Bukhari Lamba 268 Daga Qatada Yace: Anas Dan Maliku Yace Yace: Annabi Ya Kasance Yana Kyewaya Matansa -Yana Jima'i Dasu- Acikin Sa'a Daya -Wani Yanki Na Lokaci- Na Dare Da Rana Suna Su Goma Sha Daya (11), Qatada Yace: Nace Da Anas Shin Yanzu Annabi Yana Iya Haka..??  Sai Anas Dan Malik Yace: Ai Mun Kasance Muna Labarin Cewa An Bawa Annabi Karfin Namiji Talatin (30).


Mu Koma Lafazin Sa Lamba 283 Zamu Wani Abin Mamaki Yana Cewa Daga Qatada Cewa Anas Dan Malik Ya Basu Labari Cewa Hakika Annabin Allah Ya Kasance Yana Kyewaya Matansa -Jima'i- Acikin Dare Daya A Lokacin Yana Da Mata Tara (9) !!!.


بَاب إِذَا جَامَعَ ثُمَّ عَادَ وَمَنْ دَارَ عَلَى نِسَائِهِ فِي غُسْلٍ وَاحِدٍ

حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ بَشَّارٍ قَالَ حَدَّثَنَا مُعَاذُ بْنُ هِشَامٍ قَالَ حَدَّثَنِي أَبِي عَنْ قَتَادَةَ قَالَ حَدَّثَنَا أَنَسُ بْنُ مَالِكٍ قَالَ  كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدُورُ عَلَى نِسَائِهِ فِي السَّاعَةِ الْوَاحِدَةِ مِنْ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَهُنَّ إِحْدَى عَشْرَةَ قَالَ قُلْتُ لِأَنَسٍ أَوَكَانَ يُطِيقُهُ قَالَ كُنَّا نَتَحَدَّثُ أَنَّهُ أُعْطِيَ قُوَّةَ ثَلَاثِينَ


Mai Karatu Ka Duba Wannan Cin Karu Mai Ban Mamaki A Lamba 268 A Lokacin Da Annabi Yake Jima'in Yana Da Mata (11). A Mai Lamba 284. Yace A Lokacin Yana Da Mata Tara (9).!!!


بَاب مَنْ طَافَ عَلَى نِسَائِهِ فِي غُسْلٍ وَاحِدٍ

4917 حَدَّثَنَا عَبْدُ الْأَعْلَى بْنُ حَمَّادٍ حَدَّثَنَا يَزِيدُ بْنُ زُرَيْعٍ حَدَّثَنَا سَعِيدٌ عَنْ قَتَادَةَ أَنَّ أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ حَدَّثَهُمْ  أَنَّ نَبِيَّ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَطُوفُ عَلَى نِسَائِهِ فِي اللَّيْلَةِ الْوَاحِدَةِ وَلَهُ يَوْمَئِذٍ تِسْعُ نِسْوَةٍ


Ibn Hajar Yana Cewa Acikin "Fatahul-Bare" J/2 S/449 : Ruwayar Isma'il Ta Hanyar Abi Musa Daga Mu'azu Dan Hisham (An Bawa Annabin Karfin Namiji Arba'in (40) Ba Talatin (30) Ba). 


وَوَقَعَ فِي رِوَايَةِ الْإِسْمَاعِيلِيِّ مِنْ طَرِيقِ أَبِي مُوسَى مِنْ مُعَاذِ بْنِ هِشَامٍ " أَرْبَعِينَ " بَدَلَ ثَلَاثِينَ وَهِيَ شَاذَّةٌ مِنْ هَذَا الْوَجْهِ لَكِنْ فِي مَرَاسِيلِ طَاوُسٍ مِثْلُ ذَلِكَ وَزَادَ " فِي الْجِمَاعِ " 


Acikin "Sifatul-Jannah" Na Abi Nu'aim Daga Hanyar Mujahidu Ya Ruwaice Irin Wannan Hadisin Amma Da Karin Cewa (Anba Annabi Karfin Namiji Arba'in Na Daga Mazan Aljannah!!!). 


وَفِي صِفَةِ الْجَنَّةِ لِأَبِي نُعَيْمٍ مِنْ طَرِيقِ مُجَاهِدٍ مِثْلُهُ وَزَادَ " مِنْ رِجَالِ أَهْلِ الْجَنَّةِ " 


Kuma Ruwaya Ruwaya Daga Abdullahi Dan Umar Yayi Raf'insa Zuwa Annabi Cewa: An Bawa Annabi Karfin Mutum Arba'in A Wurin Damka Da Jima'i


وَمِنْ حَدِيثِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ وَرَفَعَهُ "  أُعْطِيتُ قُوَّةَ أَرْبَعِينَ فِي الْبَطْشِ وَالْجِمَاعِ  "


Kuma Ruwaya Ta Yan Ganta Daga Ahamad Da Nasa'i Hakimu Ya Ingantata Ta Hanyar Zaidu Dan Arkam Kuma Yayi Raf'in Hadisin Zuwa Annabi Cewa : Namiji Daga Cikin Mazan Aljannah An Bashi Karfen Namiji Dari A Wurin Cin Abinci Da Shan Abin Sha Da Jima'i Da Karfin Sha'awa.!!! 


 وَعِنْدَ أَحْمَدَ وَالنَّسَائِيِّ وَصَحَّحَهُ الْحَاكِمُ مِنْ حَدِيثِ زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ رَفَعَهُ "  إِنَّ الرَّجُلَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ لَيُعْطَى قُوَّةَ مِائَةٍ فِي الْأَكْلِ وَالشُّرْبِ وَالْجِمَاعِ وَالشَّهْوَةِ  "


Sai Ya Zama A Lisafi Kenan An Bawa Annabi Karfin Jima'i Na Namiji Dubu Hudu (4,000) Ina Lillahi Wa'inna Ilaihin Rajiun... 😭😭


A Gaskiya Wannan Hadisin Ya Firgitani Kamar Yanda Wanda Asan Ya Fadawa Ruwayar Yaji Firgita A Lokacin Har Yake Tambayar Cewa : Shin Yanzu Annabi Zai Iya Yin Haka...???  Kuma Bai Same Amsa Gamsashiya Daga Ansa Ba..... 🤔🤔


Amma Tambayoyin Da Nake Dasu Akan Wannan Hadisin Sune Kamar Haka :


1. Miye Dalilin Da Yasa Babu Wanda Ya Ruwayto Irin Wannan Aikin Na Sirrin Sirri -Abinda Miji Ya Kiyi Da Iyalinsa- Sai Anas Dan Malik Karamin Yaro.... ?? Ina Matan Annabi...??  Ina Mayyan Sahabbansa...???


2. Tayaya Anas Yasan Wannan Irin Aikin Kuryar Daka -Na Sirri- Da Annabi Yake Yi Da Iyalinsa.....??? 


A Iya Ilimin Babu Ta Hanyar Da Anas Zai San Irin Wannan Aikin Sai Ta Hanya Guda Uku (3) :


1. Ya Zama Cewa Annabi Muhammad (S. a. w) Ya Fada Masa Da Kansa.... 😭😭 Kuma Wannan Ba Zayyo Ba Ga Annabi Ya Zama Shine Ya Fadawa Anas Cewa Yana Jima'i Da Matansa Su (11) Ko (9) Safi Da Yamma.... 


Dalilin Da Yasa Nace Ba Zayyo Ace Annabi Shin Ya Zaunar Da Ansa Yana Fada Masa Aikin Da Yakeyi Da Iyalin Sa Ba, Shine Fadar Abinda Kayyi Da Iyalinka Na Jima'i Ko Fadar Kayi Jima'i Da Iyalinka Haramun Ne A Shari'ar Manzon Allah..... 


Abdurrazzak San'aneey Ya Ruwayta Acikin "Musannaf" J/3 S/391, Ahamad Bin Hambal 11655, Musulim Acikin Sahihinsa Lamba 1437, Daga Abi Sa'idil Khuduri Yace: Manzon Allah Yace :(Yana Daga Mafi Girman Amana Ranar Alkiyama Namijin Da Zai Biya Bukatarsa Zuwa Ga Matarsa Ta Biya Bukatarta Zuwa Gareshi Sannan Ya Watsa Sirrinta...... 

 

إنَّ مِن أَعْظَمِ الأمَانَةِ عِنْدَ اللهِ يَومَ القِيَامَةِ، الرَّجُلَ يُفْضِي إلى امْرَأَتِهِ ثم يُنشر سرّها


Idan Kace A'a Ay Ni'imace Da Ubangiji Yayi Masa.... Sai Nace To Naji Ni'imace To Amma An Ruwaito Daga Gurinsa Kamar Yanda Ahamad Ya Ruwaita 10977, 11655, Abu Ya'ala 1366 Baihakeey 5232 Abu Dauda 2174, Tirmizeey 2782, Daga Abu Sa'id Alkuduri Yace Annabi Yace :(Alfahari Da Yawan Jima'i Haramun Ne)..


"الشّياء حرام" أي المفاخرة بكثرة الجماع


2. Hanya Ta Biyu Ya Zama Anas Yasan Haka Ta Hanyar Iyayen Muminai... 😭😭 Shima Wannan Ba Zayyuba Ace Matan Annabi Suka Zaunar Da Anas Suka Fada Masa Cewa Annabi Yana Jima'i Dasu Su Duka Da Safe Da Yamma. To Wannan Ba Zayyu Ba Saboda Dalilan Da Suka Gaba Ta...... 


3. Ko Ya Zama Anas Shine Da Kansa Yasan Cewa Annabi Yana Wannan Aikin Ko Leke Yake Masa Yana Ganin Sadda Yake Fitowa Daga Wannan Daki Ya Shiga Wannan Daki Ko Dashi Ake Shiga Acikin Dakunan Na Matan Annabi Ko Ya Zama Anas Ya Kirkira Domin Ya Bata Mutuncin Annabi Saboda ...  😭😭😭 


Dalili Ya Nuna Indai Anas Hadimi Ne Hakika -Na Gaskiya- Tu Ba Zayyo Ya Aykata Irin Wannan Aikin Domin Like Da Zato Haramun Ne A Hakin Ko Wane Mutum Bale Annabin Allah A Shari'ar Islam Zamu Ga Bukhari Ya Ruwaita "Kitabul Adabi" Lambar Hadisi 4849, 5717, 5719, 6345 Daga Abu Huraira Hakika Annabi Yace: Ka Shidinku Da Zato Domin Zato Shine Mafi Karyar Labari...... 


بَاب يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنْ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ وَلَا تَجَسَّسُوا 


 حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ يُوسُفَ أَخْبَرَنَا مَالِكٌ عَنْ أَبِي الزِّنَادِ عَنْ الْأَعْرَجِ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ وَلَا تَحَسَّسُوا وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا تَنَاجَشُوا وَلَا تَحَاسَدُوا وَلَا تَبَاغَضُوا وَلَا تَدَابَرُوا وَكُونُوا عِبَادَ اللَّهِ إِخْوَانًا 


To Tambayata Anan Tace Idan Nazo Karanta Dalibai Wannan Hadisi Da Nuna Cewa Wannan Hadisin Karara Babu Wani Abu Tabbatace Da Ya Nuna Cewa Annabi Yana Irin Wannan Aikin..??  Kuma Abin Ban Takaici Ya Taba Mutuncin Annabi, Sai Nace Wannan Hadisi Ya Mayar Da Annabi Tambakar -Bunsuru- Ko Ya Mayar Dashi Mai Tsananin Sha'awa...🙄🙄


Shin Dan Allah Na Fadi Dai Dai Ko Nayi Kuskure...??? 

Shin Idan Wannan Hadisi Ya Tabbata Duk Duniya Akwai Wanda Yake Da Tsananin Sha'awa Irin Sa.....??? 

Shin Idan Annabi Yana Da Karfin Jima'i Dubu Hudu (4,000) Tayaya Zai Same Matar Da Zata Iya Zaman Aure Dashi...???

Idan Ya Zama Wannan Shine Aikinsa A Gida To Yaushe Ya Same Lokacin Iyarda Sakon Allah....???


Idan Kace Wannan Ba Taba Mutuncin Annabi Ba Ne.... 


Sai Ince Idan Akace Da Mahaifinka Yana Jima'i Da Matansa Hudu Duk Rana Zayyi Jima'i Dasu Sau Biyu (2) Da Safi Sau Biyu (2) Da Yamma Kaga Ga Yini Yana Jima'i Sau 24 A Rana..... Sai Nace Wallahi An Mayar Da Babanka Tamkar Bunsuru Ko An Mayar Dashi Khariji.... Shin Zakaji Dadi Ne....???  Zaka Sake Kallon Wanda Ya Fadawa Mahaifinka Haka Da Mutunci....??? 


To Wannan Hadisin Duk Mai Hankali Zai Tabbatar Da An Samar Dashi Domin Ya Ci Mutuncin Annabi Muhammad (S. a. w).. 😭😭


~Shareef Abdul Basid Sidi Ibrahim~

                  11 Jul 2021

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post