NASIHA ZUWA GA YAN MEDIA: Kan maganar Mallam Rabi'u Funtua



Ayyukan dan Media a harkar muaulunci aiki ne na sadaukarwa,sannan ayyuka ne na da'awa domin shi ma yana yin aikin isar da sakon harka ne ga duniya,ta hanyoyin sadarwa daban daban.

Wasu daga cikin manya manyan ayyukan dan Media a harkar musulunci sune kamar haka:

1

Isar da sakon Harkar musulunci bisa tsarin da harka ta doru a kai (Tabligh)

2

Sai kuma bai wa ita harkar kariya ta dukkanin wani janibin da makiya zasu iya kawo farmaki da dukkanin karfin alkalaminsa,cikin hikima,basira,ilimi da kuma tsari ta hanyar da ya dace (Difa'i)

3

Sai kuma yin ayyukan da zasu hada kan yan'uwa waje daya kuma karkashin jagorancin jagoran harkar musulunci Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) (Tauheed)

4

Sannan kuma dan Media ya dauka a ransa kuma har ga Allah cewar, yana yin wani aiki ne na sadaukarwa a tafarkin gwagaarmayar musulunci,kuma domin neman yardar Allah ba yardar wani ko waau ba. Kuma ya ji a ransa cewar zai fa iya samun yardar Allah wato shahada a ta wannan fanni din (aikin Media) da sauran wasu ayyukan alheri na da'awa din.

Duk wadannan abubuwan da muka lissafo su a sama,idan har dan Media yaji a ransa cewar shi yana yin aikin nan ne domin neman yardar wani ko wasu,ko kuma domin ya samu kusanci ga wasu manya a harkar nan. Ko kuma yana yi ne domin kawai yayi suna,ko kuma ya samu shiga wajen Amir din su da sauransu,to gabaki daya ayyukan nasa sun baci. Kuma ya kwan da sanin cewar ayyukan nasa zasu koma suna amfanar azzalumai ne maimakon su amfani harka din.

Haka zalika idan dan Media ya saka nasa son zuciyar da son ransa,ko kuma sakamakon kiyayyarsa ga wani ko wasu suka hana shi yin abinda ya dace,to alkalamin nasa zasu koma ne suna amfanar makiya,maimakon ya amfani harkar da yan harka din. Misali a nan:

Wani dan Media din na iya tsintar kansa a wajen wani taro (programs) sai kuma ya zamanto ahine zai rubuta rahoton taron,to idan har akwai wani wanda baya kauna,ko akwai abinda baya so a wurin,ko kuma auna da sabanin fahimta da wani,sai ya yi wa rahoton kwange. Ko kuma ya rubuta abin da yafi yi wa zuciyarsa dai dai,ko kuma ya guje wa abinda zai bakanta ran iyayen gidansa wadanda don su don su yaba masa yake yin aikin,amma ba abinda ya fi yi wa ita harkar dai dai ko abinda zai hada kan yan'uwa zai rubuta ba.

A irin wadannan yan Media din sun fi kallon maslahar Kansu sama da maslahar ita harkar baki daya.

Haka zalika,irin wadannan yan Media din sukan fifita bukatun wasu a kan bukatar ita harka din. Sukan yi abinda zai faranta wa wasu rai ne maimakon abin da zai ciyar da ita harka din gaba. Ko kuma abin da zai faranta wa jagoranmu rai.

Misali a nan: ranar da aka yi maulidin Imam Musa bn Ali Arridha a Abuja,an yi wasu tambayoyi guda uku ga maluman dake jagorantar Abuja Struggle din? Inda aka bai wa mallam Rabiu Funtua damar ya bada amsa,kuma ya bada amsar dai dai da abin da ya sani bisa adalci. Kuma ya ambaci sunayen wasu malaman Harka a yayin da yake bada amsa din,kuma alhamdu lillahi duk wadanda ya ambata din wasu na wurin taron zazzaune,wasu kuma dai duk suna raye kuma zasu ji.

Amma abin mamaki a nan shine,shi malamin yayi wa amsar adalci sosai,amm kuma shi dan rahoton ko yan rahoton da suka rubuta rahoton (yqn Media) sai suka kawo jawabin nasa,amma sai suka cire inda shi mallam Rabiu din yake fadar cewar Jagoran Harka ya bada sako zuwa ga yan Struggle cewar 'Forums' uku kacal aka yarda su tsara Abuja Struggle din, wato da Sisters Forum da Academic Forum da kuma Mu'assasatul Abul Fadl Abbas.

Sannan duk abinda suka tsara to su mika wa Shaikh Dr.Sunusi Abdulkadir Koki ya duba musu. Sannam idan shi Shaikh Dr.Sunusi din baya nan to sai a mika wa mallam Sidi Manniru Sokoto..

Amma kuma su yan Media din da suka kawo rahoton sai suka ciccire idan basa so,da kuma inda bai yi musu dadi ba,domin kawai suna kiyayya da wani mutun daya,don haka sai suka lalata rahoton suka rubuta abinda ransu yake so.

To,yanzu ina hikimar yin rahoton nan amma kuma sai ka zare ainihin zuciyar rahoton sukutum guda domin me? Domin biyan bukatar wane? An ce maka ga sakon jagora,kai kuma ka zare sakon Jagoran daga ciki,to sakon wa ka saka a ciki? Ko kuma sakon wa kake son ka Isar ga yan'uwa? Kuma me kake son ka cimma?

Ga wadanda suka karanta wancan rahoton na wancan ko wadancan yan Media din,suna iya sauraron wannan Audion na kasan wannan rubutun domin su ji ainihin abin da mallam Rabiu Funtua ya fada da bakinsa.

MEDIA FORUM KANO.

22/6/2021

CODE 002

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post